← Book details Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 51 OF 59

Sashe 51

Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Bayan kwana 3 da bikin Yusuf Anty Khadija tazo gidansu Rafi'ah, dai dai gate din tayi parking sannan ta fito ta shiga ciki, Mustapha ne kadai a compound din yana wanki caan gindin pampo, ganin bakuwace yasa ya wanke hannunsa ya karaso inda take tsaye, cike da ladabi ya ce "Ina yini Hajiya" a hankali take chewing gum din bakinta, kamar ba zata amsa ba ta ce "Lafiya, ina ne apartment din Amaryar gidan nan?" Mustapha ya nuna mata part din Anty Amina ya ce "Wancen ne Hajiya" ba tare data yi magana ba ta fara takawa zuwa apartment din, bayan ta hau balcony ta danna bell taja gefe ta tsaya. Few seconds aka bude kofar parlor, Anty Khadija ta dinga kallan Ikleemah data dawo kamar skeleton, dan ba karamin rama tayi ba, dan yatsine fuska tayi ta ce "Matar gidan na nan?" Ikleemah ta daga mata kai sannan ta bata hanya ta huce, bayan sun shiga ta turo kofar ta ce "Tana ciki bari na mata magana" daga haka ta haura upstairs Anty Khadija kuma ta nemi waje ta zauna. Da sallama ta bude dakin ta shiga, Anty Rahama dake kwance tayi saurin tashi zaune ta ce "Ikleemah bance karki hawo bane, kina ganin yadda ake fama amma ke bakyajin magana" karasawa tayi gefen mahaifiyarta ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, dafe kirjinta tayi a hankali ta ce "Ammi kirjina, wayyo Allah na" cike da damuwa Anty Rahama ta rungumeta ta ce "Allah zai baki lafiya Ikleemah, amma menene na haurowa bayan kinsan nima yanzu zan sauka" silently ta ce "Anty Amina ne tayi bakuwa" Anty Rahama ta ta6e baki ta ce "Koma wacece karki kara yin gangancin haurowa ba tare dani ba, bazaki kwala min kira ba" tana rife bakinta Anty Amina ta shigo dakin da phone dinta a hannu, karasawa wajensu tayi ta ce "Subhanallah, lafiya dai ko?" Anty Rahama ta ce "Ina lafiya Amina, daga kinyi bakuwa wai ta hauro sama kiranki, tana gani jiya sai da muka koma asibiti aka bamu wasu magungunan" Hannun Ikleemah Anty Amina ta kama ta ce "Haba Leemah, so kike ki kara jawo mana wani abun ne, ai yau kam jiki yayi kyau, maza muje kasa a dafa miki abinda kikeso" dagata tayi suka nufi kofar fita Anty Rahama tabi bayansu, a hankali suka dinga saukowa a stairs din saboda Ikleema, bayan sun shigo parlor Anty Amina ta dinga kallan Anty Khadija dake zaune tana danna wayarta. Kwantar da Ikleema tayi akan kujera ta zauna ta ce "Sannu da zuwa" Anty Khadija kallesu ta ce "Yauwa sannu" zama Anty Rahama tayi ta ce "Wa kike nema?" Anty Khadija ta danyi murmushi ta ce "Fatan an gama biki lafiya" harara Anty Rahama ta balla mata ta ce "Malama kinyi kuskure, ai ba anan akayi auran ba da zaki zo mana ban gajiya" murmushi Anty Khadija tayi ta ce "Nasani, nazo ne muyi magana da matar gidan nan" Anty Amina dake kallanta ta ce "Wace irin magana?" Anty Khadija ta gyara zama ta ce "To da farko sunana Khadija Bello, nice yayar Yusuf wanda ya auri 'yar gidan nan" dan murmushi Anty Amina tayi, bata san Anty Khadija ba amma tanajin labarinta dan ita tayi sanadiyyar raba Yusuf da Nusaiba, a hankali ta ce "Sannu da zuwa Hajiya Khadija, bari a kawo maki abin sha" daga haka ta mike, cikin saurin Anty Khadija ta ce "No, No, karki damu, ba zama nazo yi ba, nazo ne daman muyi magana, nasan kina daya daga cikin makiya auran nan" Anty Amina ta koma ta zauna tana kallan yayarta ta ce "Aiba ni kadai ba, kinga dani da yayata da 'yarta da Ummanmu da wasu daga cikin danginmu duk ba so muke ba, dalili kuwa shine basu dace ba, ga kuma cuta dake cin yarinyar" Anty Khadija tayi crossing legs dinta tana jijjiga key din mota ta ce "To kun samarwa kanku mafita?" Anty Rahama dake kallanta ta ce "Tukunna dai" juyowa Anty Khadija tayi ta kalleta sannan ta ce "Tukunna fa kika ce?" Anty Rahama ta ce "Ehh, bakiga muna da marar lafiya ba, wannan yarinyar da kike gani sanadin auran nan ta shiga wannan hali" Anty Khadija ta kalli Ikleema sannan ta ce "Allah ya kyauta, to muma dai ta bangarenmu basan auren muke ba, taya za'ai shekara daya da auran 'yar uwata ya mata kishiya, kishiyarma yarinya karama da bata san ciwan kanta ba, to ni ba dogon magana nazo yi ba, harka ce ta samu yadda zakuji dadi muma muji dadi, idan kun yanke shawarar ga card dina da komai ajiki" tana rife bakinta ta dauko card din ta ajiye akan kujera sannan ta mike ta ce "Sai anjimanku" Anty Amina ta ce "Allah ya kiyaye". Tana fita Anty Rahama ta kalleta ta ce "Anya kuwa yayarsa ce? Naga basa kama" Anty Amina ta ce "Ba iyaye daya suke ba, inaga a gidansu ya girma, amma kinsan mubi matarnan komai zai tafi dai dai" Anty Rahama ta ce "Nima naga alamun nasara, amma kinsan baza su so Ikleema ta shiga gidan ba" Anty Amina ta ta6e baki ta ce "To shine autan maza? Mu dai idan Rafi'ah zata fito na har abada ai ko ba komai mu mukai nasara, wallahi Ikleema ki kwantar da hankalinki namiji sai kin zama amma ki manta da Yusuf" shiru Ikleema tayi tana kallan Anty Amina, caan ta danyi murmushi ta ce "Na hakura Anty indai itama xata fito, wallahi a yanzu bani da burin daya wuce naga ta gama wulkanta" Anty Rahama ta ce "Gaskiya mu yarda kawai, kuma idan auran ya 6alle sai dai kinga tai ta zama a gida, daga nan suyi rayuwarsu muyi tamu" Anty Amina ta dauka card din tana kallan address din gidan ta ce "Zanje gobe na sameta nima" Anty Rahama ta ce "Bari naje na kira Umma na fada mata komai, daga haka ta mike ta wuce sama tana murmushi. Gently ya dinga daga kafarsa yadda baxata ji footsteps dinsa ba, juyowa yayi yana kallan Rafi'ah dake kwance akan kujera, mistakenly kafarshi ta bugi center table tayi saurin mikewa tana kallan parlor, komawa yayi bayan kujera da sauri ya buya, ta dinga bin parlorn da kallo jin motsi, mikewa tayi ta leka bayan kujerar suka hada ido, ta turo baki ta koma kan kujera ta kifa kanta ta fara kuka, with lots of disturb ya tashi yana murmushi ya zauna gefenta ya ce "Yanzu fa zan dawo, i just want to buy something akan junction" kwace hannunta daya rike tayi ta ce "Nasan ai wajen matarka zakaje" jawota yayi jikinshi ya rungumeta ya ce "Noo, zan samo mana lunch ne" ta kara turo baki ta ce "Ni bazanci irin na jiya" ya shafa bayanta ya ce "What do u want then?" A hankali ta ce "Egg and bread with tea" ya ce "Meyasa kike shan tea da rana" ta ce "Ni ko yaushe ma idan inasan sha" ya ce "To bari na hada miki" daga haka ya kwantar da ita akan kujera ya fita a parlor, kamshi yaji a kitchen hakan yasa ya nufi nan, Jiddah ce tsaye a gaban gas tana soya kwai, ya rungumeta unexpected tayi saurin juyowa, suna hada ido ya manna mata kiss a kumatau ya ce "How are u, dazu da safe naje na samu kina bacci" ta ce "Fine" daga haka taci gaba da abinda take, yana rike da ita harta gama ta kashe gas din, a hankali ta ce "Zan wuce parlor na ka sakeni" ya danyi murmushi yana kallan egg din hannunta ya ce "Nima zanci" ta hade fuska ta ce "To muje parlor" ya ce "Noo, sai dai ki zuba min nawa" kallansa ta dingayi kafin ta sauke kanta, ya ce "Bazaki bani bane?" Ta ce "Nifa banci komai ba tin safe gashi yanzu karfe 2 ne, kuma idan na zuba maka baxai isheni ba, dama kai zaka ci saina baka, amma wallahi bazan hada abinci wata banza taci ba" Yusuf ya matseta a jikinshi ya ce "Yanzu dai bazaki bani ba kenan" ta ce "Na fada maka ai" ya ce "Zanje eatery na siyo mana abinci yanzu sai mu kara" make kafada tayi ta ce "Nifa bazata ci abincina ba" kin saketa yayi saima kansa daya kwantar a wuyanta, Tana kokawar kwacewa Rafi'ah ta shigo kitchen din, hakan yasa tayi collapsing a jikinshi tana dallawa Rafi'ah harara, ko kallansu batai ba ta wuce ta dauko flask da mug ta fito a kitchen din, kasa hada tea din tayi ta tsaya rike da mug din a hannunta, jin motsi yasa tayi saurin bude flask din zata debi ruwa Yusuf ya ce "What are u doing?" Kin kulashi tayi ta zuba ruwanta sannan ta rufe ta dauka liptopn akan dinning ta saka a ciki, daukan mug din tayi zata wuce part dinta ya riko hannunta ya ce "Sugar fa" juyawan da zatai ta zubo ruwan zafi a kafarta, ta saki kara ta jefar da cup din ya tarwatse a wajen, da sauri Yusuf ya dagata ya ajiyeta kan kujera yana kallan kafar, Jiddah ta dinga hararansu tana murguda baki, cikin rarrashi Yusuf ya ce "Sorry dear, bari na gyara wajen muje mu siyo abinci" hawayen idanta ta share ta ce "Bayan kasa na xubar da tea dina" dariya ya danyi jin ta kirashi da tea, ya san ko me za'ai ba iya sha zata tai ba, ya dagata suka nufi part dinta ya ce "Keda baki da lafiya menene naki na hada tea kuma" a hankali ta ce "Ba kabarni da yunwa ba kaje wajen matarka, meyasa bazan hada ba" ta turo baki ta kwanta akan kujera, murmushi yayi ya fita a parlor ya share inda mug din ya fashe sannan yayi mopping wajen, karasawa yayi gefen Jiddah ya ce "Zamuje eatery me zan kawo maki" girgiza masa kai tayi ta ce "Ni banasan komai" ya bata light kiss ya ce "I know u like shawarma, ita zan siyo maki" bata ce masa komai ya koma part din Rafi'ah, a tsaye ya sameta harta sa hijabi, ya ce "Bafa dake zanje ba" cushion din gefenta ta wurga masa ta ce "Kuma saina bika, ai jiya ma daka fita baka dawo da wuri ba" ya danyi murnushi ya ce "Zance naje
Chapter 51 · 0% Book details