Sashe 48
Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 5 min read
make sure kinsha panadol sai ki kwanta kinga yanzu is 12 idan an daura auran i will call u" boye fuskarta tayi a jikin kujera tana murmushi ya ce "Yess i will be the first to tell u insha Allah" bude kofar tayi ta fito, ta dan saci kallansa ta ce "Thank u" ya fito shima yana kallanta ya ce "Allah ya sauwake" daga haka ta daga masa hannu ta koma cikin gida. Mami ce ta shigo gidan da Ikraam a bayanta, suka dinga wuce mutane a tsakar gida suka shigo ciki, Gwaggo ta kalli daya daga cikin 'ya'yanta ta ce "Waccen ba kishiyar Halima bace?" Anty Salma dake kallan Mami ta ce "Itane mana Gwaggo" Gwaggo ta ce "Shine ta wuce ba gaisuwa, aiko bata sanni ba tana ganina taga jinin su Halima" ita dai Anty Salma shiru tayi taci gaba da danna wayarta, Ummi na shirin fitowa a parlor suka ci karo da Mami, ta danyi murmushi ta ce "Sannu da zuwa Hajiya" ba yabo ba fallasa Mami ta ce "Sannu" Ummi ta juya ta ce "Ku shigo ciki" daga haka ta wuce dasu dakinta dake sama inda Anty Halima da kayenta suke, sosai Mummy tayi mamakin ganinta, dan tanaji da safe Abi na mata fada jiya bata zo gidan biki ba, Mummy ta ce "Sannunku da zuwa" Mami ta gaisa da kawayenta, ta ce "Ina Amaryar?" Ummi dake jera musu abinci agabansu ta ce "Tana nan neighbors dinmu" Mami ta ce "To ya hidima?" Ta ce "Mun gode Allah" kallan Ukraam Mummy tayi ta ce "Ke bakya gaisuwa ne?" Mami ta dan hade rai sai kuma ta ce "Haka take ai" Ikraam ta gaishe da mutanen dakin sannan ta koma bayan uwarta ta lafe, bayan minti 10 Mami ta mike tana kallan Ummi da shigowanta dakin kenan ta ce "To ni zan wuce ga wannan ba yawa" ta nunawa Ummi food flask da bedsheet din da suka kawo, Ummi ta ce "Allah ya saka da alkhairi, mun gode, Jawad ma bana kusa ban mishi gidiya ba ya wuce, Allah yasa ya tafi a sa'a kuma" ciki ciki Mami ta ce "Ameen" daga haka ta dan kalli Mummy ta ce "Sai kin dawo" bata jira cewarta ba ta kama hannun Ikraam suka fita a dakin, gaba daya mood dinta ya canza, leda Ummi ta samu ta juye musu snacks din da basu ciba, Abdul da shigowansa kenan ta ce "Kaima Mamansu Jawad kafin su tafi, kace mun gode" cikinsa ya fara shafawa yana kallanta ya ce "Yunwa nakeji Ummi" ta dalla masa harara ta ce "Ba aiken ka nayi ba, nima babu abinda naci tin ruwan lipton dana sha da safe" juyawa yayi ya fita a dakin, da sauri ya fita gate ya samu tana shirin ta tada mota, mika mata ledar yayi ya ce "Ina yini" taja motarta ta bar kofar gidan, kallan hannunsa ya dingayi yaga ba abinda ya sameshi dan dama da sauri ya janye, ya koma cikin gida ya zauna kusa da Gwaggo dake balcony akan tabarma ya fara cin snacks din. Karfe 1 aka dinga tafiya babban masallacin juma'a dake unguwar dan anan za'a daura auran. Rafi'ah na daki taci kwalliya sosai suna ta hotuna kiran Ummi ya shigo mata, tayi picking call din ta fito a dakin saboda hayaniyar friends dinsu, a hankali ta ce "Ina yini Ummi" ta ce "Lafiya, kinci abinci ne?" Ta ce "Ehh, naci" Ummi ta ce "Kina addu'a dai ko Rafi'ah?" A hankali ta ce "Inayi" Ummi ta ce "Never get tired of praying daughter, ko me kike ki dinga addu'a, make sure kina kiran Allah a duk kan lamarinki" silently ta ce "Insha Allah Ummi" Ummi ta ce "Good, Ga Mummynki" kar6ar wayar Anty Halima tayi ta ce "Kina jina Rafi'ah?" Ta ce "Eh" Mummy ta ce "Ku shirya ayi kamun nan da wuri a kaiki kafin dare yayi sosai, kowa saiya dawo gida cikin nutsuwa, karfe 4 kuna wajen nan dan Allah" ta ce "To zamu shirya" Mummy ta ce "Allah ya tsare yasa a gama komai lafiya" a hankali ta ce "Ameen" sannan tayi hanging call din ta koma daki, gefe ta zauna tayi shiru tana kallan time, karfe 2 harda minti 15, ta kifa kanta akan gwaiwoyinta tana karanto ayatul qursiyyu, Maryam ta juyo tana kallanta ta ce "What's wrong Fatima?" Sai a lokacin duk hankalinsu ya kai wajen, suka koma gefenta suna tambayarta menene, Ameera ta ce "Ko ciwan kanne?" girgiza musu kai tayi ta ce "Ba komai" daga haka ta fashe da kuka, Ameera da gaba daya ta rikice ta ce "Wai menene Fatima?" Cikin kuka Rafi'ah ta ce "Abbana, i will miss him" Ameera taja dan karamin tsaki tana murmushi, ita a tinaninta ma wani abin ne ya faru, daga haka ta rungumeta tana kallan agogon dakin ta ce "Kinga time kenan? Ai hamdala ya kamata ki farayi not crying Teemah" Rafi'ah ta share idanta ta ce "Na fada ai" su Maryam dake kallansu suka kwashe da dariya, harara ta musu ta turo baki tana juya kai gefe, wayarta ne ya fara vibrating tayi saurin kallan screen din, daga call din tayi kirjinta na bugawa da sauri~da sauri, Yusuf ya danyi murmushi ya ce "You are now my wife" limshe idanuwanta tayi tana murmushi. Karfe 2 da rabi 'yan daurin aure suka fara dawowa, Anty Amina ta fito tsakar gida ko zata ji wani labari amma taga kowa hidimar gabansa yake, Ikleemah na biye da ita har suka karaso wajen apartment din Ummi, juyawa tayi sai ga Abba ya shigo gidan, tayi karfin hali ta kakalo murmushi ta ce "Abban Rafi'ah har kun dawo?" Ya ce "Ehh an daura aure, ki samo min abincin mutum 10 akai guest house dina" da ido kawai ta bishi yana magana, juyawan da zatai taji faduwar Ikleemah a kasa, Abba da har ya fara tafiya ya juyo da sauri yayi kansu, Anty Amina ta saki kara tana jijjigata ta ce "Na shiga uku Ikleemah dan Allah ki tashi" dai dai nan Anty Rahama ta shigo, tayi kansu da gudu tana ta shiga uku, daga Ikleemah Abba yayi ya nufi bakin gate da ita Anty Amina tabi bayansu tana kuka.