Sashe 40
Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Gently Yusuf ya karasa inda suke ya kalli Rafi'ah sannan ya ce "Go inside" ta juya duk jikinta a sanyaye ta shige gate, dan murmushi Jawad yayi bai ko kalli inda yake ba yabi bayan Rafi'ah, tana nan tsaye bakin gate tana lekawa to see if they will quarrel, saurin ja da baya tayi ganin Jawad ya turo gate din, ta sunkuyar da kanta ta fara kame~kame ta ce "I'm...looking for my....for my earring...it just fall down here" durkusawa tayi ta dinga bin interlock din da ido, Jawad ya dinga kallanta kafin a hankali ya ce "Fatima" dagowa tayi ta kalleshi ya ce "U are just 17 and i'm 35 so don't think zaki iya min karya ban gane ba, and don't forget my profession, daga yadda mutum yayi magana i know if he's lying, kawai kice kina kallan wancen mutumin ne" dan zaro ido tayi ta ce "Laa nifa ba shi nake kalla ba, na leka ne naga ko zaka shigo" murmushi Jawad yayi yana kallanta ya ce "This is strictly no, bani card din hannunki nagani" mika masa tayi sannan ta sauke kanta kasa tana ta wasa da zoben hannunta, sai daya karatanta tass sannan ya mika mata ya ce "And u are happy ko?" Ta girgiza kai sai kuma ta ce "That's God plan" Jawad ya dinga kallan pink lips dinta dake motsi a hankali lokacin da take magana, shafa kansa yayi ya dauke idansa a kanta ya ce "Haka dai kika za6awa kanki, but ai there's a way out, u can leave him and find another love" noke kafada tayi ta dan turo baki kafin ta ce "No, ni dai a'a" Jawad ya dinga kallanta with passion, juyawa yayi ya nufi cikin gida tabishi da ido kafin ta kara turo baki tabi bayansa. Ummi na zaune a parlor Abdul yayi pillow da cinyarta Jawad ya shigo da sallama, Ummi ta daga Abdul a jikinta tana murmushi ta ce "Barrister" murmushi shima yayi ya zauna akan carpet, dai dai lokacin Rafi'ah ta shigo da card a hannunta ta wuce upstairs, ya sauke idanuwansa daga kallan Rafi'ah ya ce "Ina Yini Ummi" ta ce "Lafiya kalau Ahmad, how is work? kwana biyu baka leko mu ba" shafa kansa yayi yana murmushi ya ce "Aikine yanzu yakemin yawa" ta ce "To Allah ya taimaka ya bada sa'a" ya ce "Ameen", kwalawa Rafi'ah kira Ummi ta shiga yi, bayan ta sauko ta tsaya bayan kujera ta ce "I'm here" Ummi ta ce "Ki kawowa Ahmad abinci" juyawa tayi zata nufi kitchen Jawad ya mike ya ce "Zan wuce ne dama" Ummi ta ce "Abincin fa?" Ya ce "Fitowana naci abinci, and na samu call daga court" Ummi ta ce "To nagode Jawad, Allah ya saka maka da alkhairi, kana da kokarin zumunci keep it up" murmushi yayi ya fita a parlorn byan ya sake mata sallama. Shirye~shirye Umma keta yi baji ba gani, kai kace Anty Khadija ce me yin auren, komai ta gani tace za'a raba a biki, musamman da yanzu biki ya rage saura kwana biyu, sai dai duk abinda take siya aljihun Yusuf ne yake yin kuka, kuma ko kadan baya nuna gajiyawarsa dan dai su rabu lafiya. Sai ranar Friday su Abba suka dawo Kano saboda aiki daya masa yawa, Mustapha ne ya daukosu a airport, bayan sun dawo yayi parking ya ciro karamar jakar Abba a boot ya nufi cikin gida, Anty Amina ta wuce apartment dinta, da sauri Ikleemah ta fito ta rungumeta ta ce "Anty gidanma ba wani datti fa, harna sallami me aikin ta tafi" Anty Amina ta ce "Uwarki bata zo ba ko?" Ikleemah ta ce "Sai anjima tace zata zo" daga haka Anty Amina ta kama hannunta suka wuce ciki. Rike da hannun Abdul Abba ya shigo parlor, Ummi dake kitchen ta fito tana murmushi ta ce "Ur welcome" ya ce "Thank u Madam, how is everyone?" Ta ce "All fine, sannu da hanya" daga haka ta daga masa cushion din kan kujera ya zauna, kan Abdul ya shafa ya ce "Babana ka fara tara gashi ko?" Abdul ya danyi murmushi ya ce "No, zanyi aski anjima" fitowa Rafi'ah tayi a kitchen ta dan zauna akan carpet ta ce "Sannu da dawowa Abba" hannunsa ya mika mata ta saka nata a ciki sannan ya ce "Come close Mamana i missed u, how are u?" Kanta na kasa sosai ta ce "Fine Abba, ya hanya?" Ya ce "Alhamdulilah" daga haka ya bata side hug, duk sai taji kunya sosai, bayan ya saketa ta koma gefe ta ce "Abba baka siyo mana Apple din nan ba" ya ce "Na siyo mamana, ki duba boot inaga basu fito dashi ba" har zata fita Abba ya ce "Come back, let ur brother go" daga haka ta dawo Abdul ya mike ya fita, kiran da Ummi ke mata yasa ta fasa zama ta wuce kitchen. Ummi ta mika mata carrot ta ce "Ki gyara sai ki hada komai ki kai dinning, after then sai ki daura wancen naman" turo baki tayi dan tin safe take aiki a gidan nan, duk ta gyara ko ina tayi mopping sama da kasa, kafin ta gyara kitchen suka dora abinci, Ummi dake hararanta ta ce "Idan ba zakiyi ba u let me know, ai ba yau na saba yin komai da kaina ba" daga haka ta fice a kitchen din, turo baki ta karayi ta dauko chopping board ta fara yayyanka carrot din, ta kusan gamawa kenan mistakenly ta yanka yatsanta na hagu, ta saki kara sosai ta jefar da knife din a kasa, da sauri Ummi ta shigo tana kallanta ta ce "What's that shouting for Rafi'ah?" Rafi'ah ta fashe da kuka tana nuna mata yatsanta, Ummi ta dinga kallan yatsan da yankan ma is not that deep, jinin ma dan kadan ne ta fito, wukar ta dauka ta ci gaba da gyara carrot din bata kulata ba, Abba ne ya shigo rike da newspaper ya ce "Ya akai ne?" Ummi ta ce "Ba komai, ta tsorita ne" Abba ya juya ya ce "Alright, be careful Mamana" harara Ummi ta maka mata ta ce "Fita min a kitchen" ta goge hawayen idanta ta ce "Ummi zafi yakemin fa" cikin tsawa Ummi ta ce "I said get out here, dama aiba niyyar yi kikayi ba" tana fita a kitchen din Abba kuma ya shigo ya ce "Wai lafiya dai?" Ummi ta ce "Wai yankewa tayi shine takemin kuka, dama dai ba niyyar yin aiki tayi ba, banga abin kuka ba a wannan wajen" Abba ya kalli Rafi'ah data kifa kanta akan kujerar dinning, karasowa cikin kitchen din yayi ya ce "Pls u stop shouting at her, kiji tausayinta mana, after ciwan dake daminta kiyi ta mata tsawa, haba Ummu Rafi'ah, let her rest pls, ke kinki kuma a nemo mai aiki" Ummi dake sauraronsa ta ce "Allah ya baka hakuri, mai aiki ne banaso, sai dai idan aure tayi" Abba ya danyi murmushi ya ce "Nifa ba fada nazo muyi ba Madam, kinbi kin hade rai" a hankali ta ce "To ai kaine sai kaita nunamin kamar bani na haifi Rafi'ah ba" Abba ya ce "Pardon, amma u have to see her condition" ta ce "To" fitowa yayi a kitchen din jin phone dinsa na ringing. Jiddah ce zaune a high table wajen Kamu, tayi masifar yin kyau, make~up very light aka mata amma kamar ka saceta a wajen, hall din babbane sosai kida nata tashi, a gaba gaba tawagar Umma take, manyan mata sun sha tsadadden lace dinsu yawancinsu da gold a neck dinsu, Anty Khadija ma ta cakare sai hotuna suke da friends dinta maza da mata, ganin Jiddah ta hade rai yasa Anty Khadija ta fara takawa steps din har inda take zaune ta ce "Ke dalla ki kwantar da hankalinki sai kace bakisan halinsa bane, Umma ta kirashi yanzun nan zakiga ya karaso" Jiddah ta marairaice ta ce "Anty dan Allah kiyi iya bakin kokarinki, Allah yaya zai iya kin zuwa ko waye ya kirashi" tashi Anty Khadija tayi ta kira number Aliyu, yana dauka ta fice a hall din saboda karan kida ta ce "Ali kuna ina ne? anata jiransa gashi har time ya tafi" Aliyu ya ce "Hajiya Anty yanzun nan zaki ganmu, muna jiran wani abokinmu ne" Anty Khadija ta ce "To kuyi sauri dan Allah, gashi karfe 7 time dinmu zaiyi expire su gyara wajen wasu zasu shiga by 8, Aliyu ya ce "Don't mind Antyn mu gamu nan" daga haka yayi hanging call din yana kallan Yusuf dake zaune ya limshe idanuwansa, tin jiya yake kiran Rafi'ah a waya amma wayanta a kashe, Aliyu ya dafa shi ya ce "Kaifa ake jira Yusuf, sai kirana ake wallahi" Ajiyar zuciya Yusuf ya sauke ya ce "I'm not going Aliyu, sai da nace ni banason wannan kidan amma sai da akai" Aliyu ya matso kusa dashi ya ce "Yau ne fa kawai Doctor, pls entertain her baza taji dadi ba idan baka je ba" yana rife bakinsa wasu friends dinsu su shida suka shigo dakin, daga haka dai har sukai convincing dinsa yace zaije amma ba dadewa zaiyi ba, canza kaya yayi cikin milk gezna, tayi bala'in mishi kyau sosai, ga beard dinsa sun kwanta saman farar fuskarsa sai kamshi yake, daga haka suka shiga mota suke wuce shida Aliyu, sauran motoci hudun kuma suka bisu a baya. Ba karamin farinciki Jiddah tayi ganin Yusuf ba, gaba daya ta kasa dauke idanta a kansa, ta dinga murmushi tana kallansa harsu Aliyu suka rakoshi gefenta sannan suka koma table dinsu, sosai aka ci aka sha a wajen, aka cashe sosai musamman Umma da kawayenta, da kyar Yusuf ya tashi ya manna mata 'yan 500, sannan ya juya ya mannawa Jiddah ma, Anty Khadija na rawa har zuwa wajensu ta dinga watsa musu kudi tana video, ba jimawa Ammin su Sameer ta fito itama ta dinga watsa masa kudi tana tsokalarsa, duk 'yan uwa da abokan arziki saida suka manna masa kudi, musamman Sameer yafi kowa watsawa dan uwansa kudi, jin an kama hannunsa yasa ya juya, ya sakar mata murmushi ya ce "Khairiyyan Yaya" ta washe masa baki ta ce "Yaya banga Anty ba?" Ya ce "Wa?" Ta ce "Wannan faran, Anty wama