Sashe 19
Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 7 min read
enter" dagowa tayi tana kallansa, ya ce "Do i look like a kidnapper?" Ta ce "No, but i prepare to stay here" Yusuf dake kallanta ya ce "Pls ki shiga" ta ce "Here is also ok Doctor" ya sauke ajiyar zuciya yana cusa hannunsa a pocket dinsa ya ce "To akwai balcony a nan kwanar sai mu zauna" a hankali ta juya ta kalli direction din inda yake nuna mata, ganin wajen ba mutane yasa ta karasa wajen ta zauna, bayan ya rife motar shima ya karaso ya zauna gefenta yana murmushi, kauda kanta tayi gefe ganin kallanta yake, Yusuf yayi dariya kafin ya ce "How is Ummi?" Ta ce "Tana gida" ya ce "Daddy fa?" Ta ce "Dazu ya koma Abuja" Yusuf ya ce "Allah ya kai shi lafiya" ta ce "Ameen", shiru duk sukai na tsawon lokaci, Yusuf yayi breaking silent din ta hanyar kiran sunanta, ta juyo ta kalleshi sannan ta amsa, ya ce "U told me that u aren't in any relationship right?" Ta daga masa kai ba tare data kalleshi ba, Yusuf ya ce "Good" shiru yayi na dan lokaci kafin ya dan kalleta ya ce "I think it's a care and pity before, but now i discover that it was love at first sight" dago kanta tayi da sauri ta kalleshi, suna hada ido ta sauke kanta kasa zuciyarta na bugawa, she never expect such speech from him, bayan haka this is the first time wani ya ta6a cewa yana santa, Yusuf ya gyara farin glasses din idansa ya ce "I know u are shock with my words, but pls do accept me, i Yusuf i promise not to disappoint, zan zauna dake har karshen rayuwata Rafi'ah, i will never ever cheat on you, wallahi wallahi words only can't express how much u are to me, na fara sanki since from the first day i saw u". Shiru Rafi'ah tayi ta dinga jujjuya ring din hannunta, she can't just imagine herself wai ita ne aka furtawa kalmar so, cikin sweet and cool voice dinsa ya ce "But it isn't by force, if u are not interested in me i can give up" shiru bata ce komai, ya dan shafa gashin kansa yana kallanta ya ce "Ohk, idan baki ce komai ba that means u accepted" da sauri ta juyo tana kallansa ta ce "No! pls" ya ce "Then say something" turo baki tayi ta ce "To ai ni ban san ya ake cewa ba, and this is the first time wani yace min yana so..." Shiru tayi ta rife fuskarta da himar din jikinta, Yusuf couldn't hold his laugh, looking smiley ya ce "I know Fatima, but say something even if it is OK" har lokacin bata bude face dinta ba, ta ce "Sai dai ka zama Yayana tinda ni banda shi" ya ce "To kinsan me za'ai" ta girgiza kai still fuskarta a rife, ya ce "Ai Yaya baya auren kanwarsa, but let's make ourselves to be cousins, kinga at the end zamu iya yin aure" ita dai bata ce komai ba banda murmushi da take, Yusuf ya janye hijabin a fuskarta ya ce "Ki daina rufemin cute face din nan" juya kanta tayi gefe ta ce "Pls stop Doctor" ya ce "To kice wani abu" ta make kafada, Yusuf ya ce "Pls beautiful" Mikewa tayi da sauri sakamakon bell da taji an kada, ta dan kalleshi ta ce "Zan tafi kar Abdul ya nemeni" ya ce "Muje to saina sauke ku a gida" ta ce "Driver dinmu zaizo" daga haka tabi ta gefenshi ta wuce ya bita da kallo yana murmushi. Tana zuwa bakin gate din islamiyyan ta samu Mustpha yayi parking, ta bude back seat ta shiga sannan suka jira Abdul, bayan ya shigo Mustapha yayi reverse suka juya, Rafi'ah ta kalli direction din da motar Yusuf yake, a tsaye ta ganshi yana kallansu, yayi saurin daga mata hannu ta kauda kanta gefe. Within 10 minutes suka isa gida, Mustpha na parking suka fito suka nufi entrance din gida, Ummi ce zaune a parlor tana yanka pumpkin leaf, Rafi'ah ta zauna gefenta ta ce "Mun dawo" Ummi ta ce "U are welcome" ta cire hijabin jikinta ta ce "Pls Ummi ki samin credit na kira Mummy" Ummi ta ce "Never, Abba baya tura maki kudi ba?" Rafi'ah ta ce "A'a fa, bai bani ba" Ummi ta ce "Check now, dazu da mukai waya yace ya tura maki" wayarta ta dauko a jaka ta shiga messages, aikam tana budewa taga credit alert na 10k, ta danyi murmushi ta ce "Na gani, thanks" Ummi ta ce "Sai ki kirashi". Recharging ta fara yi sannan tayi dialing phone din Abba, yana picking ya ce "How are u Mum? Kunje islamiyya?" Ta ce "Fine Abba, how was ur journey?" Ya ce "Alhamdulilah" ta ce "Yanzu naga alert thank u so much, Allah ya kara arziki" ya ce "Mention not, i will call u ltr" a hankali ta ce "Ohk bye" tana hanging wayar Ummi ta ce "Da yamma zakuje gidan Umma" Rafi'ah ta dan hade rai ta ce "Nikam gaskiya bazanje ba, dama dai da Abba ne" Ummi ta dalla mata harara ta ce "Sai ki kira wanda ya fada kice mishi baza kije ba" turo baki ta kara yi ta ce "Ni kam gaskiya ni banaso, Ummi fa basa dariya sai suyi ta hade rai, kuma wallahi wannan karan bazan musu shara ba" ko kallanta Ummi batai ba bare ta bata amsa, Rafi'ah ta ajiye wayarta gefen Ummi ta ce "Kuma ma Anty Amina tana caan, su taru suyi ta zagin mutum, ni wallahi gara nayi bacci akan..." cushion Ummi ta gefa mata ta ce "Idan sun zageki ajikinki zai fito ko naman jikinki suke gutsura? Wallahi idan baki shiga hankalin ki ba i'm going to deal with u honestly, ke ba kya shiru ne a rayuwarki? Must u talk? and let me hear u talk again kiga ikon Allah" shiru tayi ta kifa kanta akan kujera, deep down her kuma tayi alkawarin indai taje baza ta musu aiki ba, ba kuma za'a zageta ta kyale ba. Suddenly phone dinta dake ajiye kan sofa ya hau ringing, Ummi ta dinga kallan screen din ganin an rubuta Dr. Yusuf, tashi Rafi'ah tayi daga inda take ta dauka wayar sannan ta nufi upstairs Ummi ta bita da kallo. Direct dakinta ta shiga bayan tayi picking call din ta zauna bakin gado, Yusuf ya ce "How are u dear?" Silently ta ce "Fine" ya ce "Why the mood?" share dan guntun hawayenta tayi ta ce "Wai saina je gidan Umma ne" Yusuf ya shafa gashin kansa yana murmushi ya ce "Who said so? And who is Umma" a hankali ta ce "Kanwar Kakanmu ce" Yusuf ya dan zaro ido ya ce "To meyasa bakinsan zuwa? Is she not ur grandmother?" Sake share idanta tayi ta ce "She is, but basa sona ai" Cikin rarrashi Yusuf ya ce "Kiyi hakuri to kije kinji Baby" ta dan turo baki ta ce "Ni banaso" ya ce "I know but for the sake of ur parents, ai lada ma zaki samu idan kikaje, kinga kinyi ziyara" ta ce "Uhm, uhm" ya ce "Bakisan ladan Baby?" Ta ce "Inaso" ya ce "Then smile" ita kanta batasan lokacin data saki murmushi ba, ya ce "Alright, i will call u ltr ina driving ne" ta ce "Allah ya kiyaye" ya ce "Won't u say bye~bye my love" ta danyi dariya kawai, ya ce "Oh na baki dariya kenan?" ta ce "Something like that" ya ce "ko?" Ta ce "Ehh" ya ce "To zan kiraki anjima, bye bye love" saurin rife ido tayi ta janye wayar a kunnenta tayi hanging call din, tana juyawa sukai ido hudu da Ummi, sai da zuciyarta ya buga at first, Ummi ta ce "Who's that?" Shiru tayi ta sunkuyar da kanta kasa, Ummi ta ce "I'm i not talking to Rafi'ah?" A hankali ta dago kanta tana kallanta ta ce...