← Book details Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 15 OF 59

Sashe 15

Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 6 min read

*SHARIK HAYATI*

Dedicated to Maryam Shehu 🧡

_08103810398_
[6/9, 11:00 AM] Teemarh: *_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

*BY FATIMA* _{Real~Teemarh}_

_15~16_

Kiran da CMD yayi wa Anty Khadija yasa ta juya tana hararan Yusuf ta bar wajen, sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke hade da limshe ido sannan ya juya ya fita shima, direct parking space ya nufa ya shiga motarsa ya bar clinic din. Misalin karfe 5 na yamma akai discharging din su Rafi'ah, bayan an gama kai komai mota Abba ya shafa kanta looking into her eyes ya ce "Sannu Mamana, i hope u are not feeling any pain?" Ta daga masa kai tana gyara wuyan hijabinta ta ce "Ehh Abba" ya kalli Ummi dake nade bedsheet din kan gadon ya ce "Let's go Madam" ta ce "Ina fitowa yanzu, akwai sponge dinta a toilet da sauran abubuwa zan dauko" Abba ya kama hannun Rafi'ah suka fita a dakin, sai sannu yake mata har suka isa mota, ya zaunarta a back seat ya durkusa daidai fuskarta yana murmushi ya ce "What do u want to eat?" Ta mayar masa da murmushi ta ce "Nothing Abba" ya shafa fuskarta ya ce "In siya maki Shawarma, i know u like it" ta zaro ido tana dariya ta ce "Abba bayan a asibiti shawarma nayi ta ci, nidai a'a banaso" ya ce "To me kikeso?" Ta ce "Dan~wake, nasan Ummi zata dafamin idan muka koma" Abba ya zaro phone dinsa a aljihu ya ce "Let your stepmother cook, kinga muna zuwa idan kikai wanka sai kici" ita dai murmushi kawai tayi tana kallan Abbannata, yana fada mata bai jira cewarta ba ya kashe wayarsa, Ummi na karasowa ta shiga front seat Abba ya zagaya mazauninsa yaja motar suka tafi. Cikin 15 minutes suka isa gida, Mustapha ya bude gate suka shigo, bayan Abba yayi parking ya fito yana kallan Rafi'ah dake kokarin bude kofa ya ce "Let me get the food for u" ta daga masa kai tana satan kallan Ummi, suna hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, Ummi dake kallanta ta ce "Which food?" Rafi'ah ta rife kofar motar ta ce "Dama Abba ne yace wai tamin dan wake" Ummi ta ta6e baki ta nufi entrance din gidan, tana danna bell Abdul ya bude yana mata sannu da dawowa, daga haka ya wuce ta ya rungume Rafi'ah yana patting bayanta ya ce "Welcome home dear" ta shafa bayansa itama ta ce "Thank u bro" daga haka ya kama hannunta suka shiga ciki, suna shiga ta kwanta kan sofa tana limshe ido, Ummi ta ce "Get up Rafi'ah" ta dan turo baki ta ce "I just want to rest Ummi i'm not sleeping" Ummi ta ce "Won't u bath?" ta ce "Ba yanzu ba" Ummi ta dagata ta ce "Tashi kije kiyi wanka" tashi tayi dan ba yadda zatai ta wuce upstairs. Cikin fishi Abba ya shigo farlon ya zauna, kana kallansa kasan ransa a 6ace yake, kallan direction din inda yaji footsteps yayi, Ummi ta ajiye flask din hannunta akan dinning ta ce "What are u taking for dinner?" Abba ya girgiza kai ya ce "Ki hadawa Mamana abinda tace tana so, i think tea is ok for me" ba tare da Ummi ta kalleshi ba ta ce "Dama ban jira tamin ba ai, na riga na gama komai ruwa kawai nake jira ya tafasa" Abba ya juyo yana kallanta, ganin ta koma kitchen yasa ya mike ya nufi mosque danyin sallan magrib, ba jimawa Rafi'ah ta sauko cikin sleeping dress dinta iya knees, Ummi ta juyo tana kallanta ta ce "Have u pray?" Ta ce "Yes" Ummi ta ce "Abincin yana kan dinning, and after all ki tabbar kinyi combing gashinki" Rafi'ah ta shafa gashinta dake daure da ribbon tana kallan Ummi ta ce "Dan Allah kimin" Ummi ta dalla mata harara ba tare da tace komai ba. Anty Khadija ce zaune gaban Umma tana mata bayanin inda taga Yusuf, Umma ta numfasa ta ce "To ke a ganinki wajenwa yaje?" Anty Khadijah ta ta6e baki ta ce "Ina xan sani Umma, ai badan CMD ya kirani ba wallahi saina shiga dakin, kuma abin haushi dana gama aiki naje room din na samu ba kowa ciki" Umma na jijjiga kafarta dake kan kujera ta ce "Bari dai yazo, nasan maganinsa kuma" tana rife baki sai gashi ya shigo da sallama, duk cikinsu babu wanda ya amsa, Anty Khadija ta wani hade rai ta juya kai gefe, a hankali ya karaso cikin parlorn ya zauna kan sofa ya ce "Sannu da gida Umma" sai a sannan ta kalleshi ta ce "Ai da wucewarka kayi Yusuf, how many times kake diban kafafuwanka kabar gidan nan ba tare da kaje ka gaisheni ba, sai yanzu zaka wani zubamin jaar fuskarka kacemin sannu da gida, gadin gidan nakeyi?" Tinda ta fara magana kansa na kasa, sai da yaji ta dasa aya ya dan dago kansa ya ce "I'm sorry, almost sometimes banasan naje kina bacci ne na tasheki shiyasa, amma insha Allah bazan kara ba i apologize" Umma taci gaba da taunar chewing gum dinta ta ce "Inaso kuma ka fara hada lefe, saika turomin kudi ta account dina" Cikin sauri ya dago kansa yana kallanta ya ce "Lefe kuma Umma, ni ban tsayar da matar aure ba har yanzu" Umma ta dalla masa harara ta ce "Jiddan uban waye yace yana santa?" Yusuf ya gyara hulan kansa ya ce "It's before Umma, but ni yanzu bani da ra'ayin aurenta, sabida she isn't my type" Anty Khadija ta juyo tana kallansa ta ce "Kama samu zata aureka kenan? Kai har kanada hurumin za6ar matar aure, kaida kake fama da ciwon zuciya mutuwa ko yau ko gobe" nunata Yusuf yayi da yatsa ya ce "Enough Khadijah, don't let me show u d bad side of me, i Yusuf don't fight, but idan kika kara shiga rayuwata i swear to almighty Allah u will regret" daga haka ya kalli Umma ya ce "Saida safe Umma" Umma data hangame baki tana kallansa ta ce "Lalalala karka sake ka kirani da Umma dama, ai zaifi maka ka kirani da Fatima sunan da ubana ya rada min, Khadijan daka fada Aisha ka kira baka saya ba, shekara biyu ta baka a duniya idan baka sani ba yau ka rubuta ka ajiye, wawa kawai" ba tare daya juyo ba ya shige dakinsa ya rufo kofar, Anty Khadija da ranta ya gama 6aci ta mike zata nufi kofarsa Umma ta rikota ta ce "Sa ido kiga ikon Allah Dije, maza kwantar da hankalinki" cije baki Anty Khadija tayi ta koma ta zauna tana huci tana huhhuro hanci.
Chapter 15 · 0% Book details