← Book details Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 59 OF 59

Sashe 59

Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 11 min read

_08103810398_
[8/12, 10:27 AM] My Imaan: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_43_

Ummi ce zaune a room din da akai admitting dinta, drip ne a hannunta na dama dayan hannun kuma tissue ne a ciki, lokaci~lokaci tana goge hawayen dake sakkowa kumatunta. Kusan awanta 5 da tashi kenan amma har yanzu Rafi'ah bata farfado ba, jin an bude kofar yasa ta daga kanta tana kallan direction din kofar, Abba ya shigo dakin ya zauna gefenta, kana kallan idanuwansa kasan shima yayi kuka, ga rashin jin dadi a fuskarsa karara, karfin hali kawai yake a matsayinsa na babba wanda ya yarda da kaddara either good or bad. Kamo hannun Ummi yayi ya ce "Ya jikin?" Ta share hawayen idanta ta ce "Da sauki" Abba yayi shiru yana kallanta kafin ya ce "It is a test from God Zainab, babu kuma wanda ya isa ya wuce kaddararsa a rayuwa, idan Allah ya rubuta zai faru definitely it might happen, amma dan Allah ki daina kuka haka nan, nasan abin da ciwo, it really hurt us, musamman keda kika haifeta" Ummi tayi shiru kawai tana ci gaba da goge idanta, Abba ya juyo yana kallanta sosai ya ce "Itama ta tashi yanzu, amma dan Allah idan kikaje kar kiyi kuka, pray for her, u are a mother, don't make her to give up in life, encourage her, support her, karki bari ta tsaneni aure at this her age, it's a destiny" a hankali ta ce "Insha Allah, kun kira shi dinne?" Abba ya ce "I called him, ya kuma ce ya saketa so muyi hakuri kawai, nata kaddarar kenan" Ummi ta kara share hawayen idanta ta ce "She's pregnant fa Abbu Rafi'ah, wallahi bazan yafewa Yusuf ba, dama tun farko abinda nayi gudu kenan" Abba ya girgiza kai ya ce "That should not be a problem, fatana Allah ya raba lafiya, ko guda 100 zata haifa i can take care of them, kawai kici gaba da addu'ah, soon komai zai zama tarihi, shi kuma watarana zaiyi nadama" Ummi ta ce "Hakane, Allah ya bamu ikon cinye wannan jarabawar" ya ce "Ameen" daga haka ya zare mata drip din hannunta ya ce "Ki daure ki mata sannu don't forget all i said" Ummi ta gyara hijabinta kawai ta nufi kofar fita walking slowly, dan ji take kamar zata kara faduwa, kamata Abba yayi har suka je dakin da Rafi'ah ke kwance, Abba ya bude kofar suka shiga, Mummy ce tsaye a kanta tana rarrashinta, sai maganganu take anyhow komai yazo bakinta fada take, dayan side din kuma Ammi ne tsaye da Khairiyya sai share idanta take da hijabi, Anty Amina dasu Anty Rahama ma suna tsaye, sai goge hawayen munafirci suke, Mummy ta dago jajayen idanuwanta da suka kumbura tana kallan Ummi ta ce "Sannu" Ummi ta daga mata kai tana kallan Rafi'ah dake kwance, a hankali ta karasa kusanta ta ruko hannunta, jikinta zafi gaau, tana kallan Ummi ta zabura ta mike ta rungumeta, fashewa tayi da kuka tana fadin "Ki yafemin Umminah, ya sakeni for no reason, ban masa komai ba sai ma shine yake cutana for almost 2 months, ban ta6a fadawa kowa ba, pls Ummi kuce karyamin haka, never thought i will be divorced at this my age" saketa Ummi tayi ta fita a dakin saboda kuka da take itama, Mummy ta kama hannun Rafi'ah ta zaunarta akan gado ta ce "So u haven't heard all i said Fatima" cikin kuka ta ce "Naji Mummy, but u people should let me cry, idan banyi ba bazanji dadi ba, Allah ya Allah idan mafarki nake kasa na tashi yanzu" rungumeta Mummy tayi ta dinga jijjigata tana fada mata kalaman da zasu mata dadi, bayan kusan minti 30 tayi shiru tana bin kowa na dakin da kallo, Mummy ta kwantar da ita ta ce "Kiyita addu'ar dana fada maki dazu, dan Allah u stop crying, kinsa Umminki na caan tana kuka, so kike BP dinta yayi raising ne?" Ta girgiza kai a hankali hawaye na sakko mata ta ce "Indai a kaina take kuka nima na daina, kice mata bazan kara ba Mummy" Mummy ta ce "To karki kara, ki kwanta kiyita addu'a" mikewa tayi ta kwanta tana kallan Abdul dake share hawaye yana zaune akan kujerar dake opposite din gadon da take. Mummy na fita taji hawaye masu zafi na sakko mata, ta share idanta sannan ta karasa dakin da Ummi take, tana zaune Abba na gefenta ya hada mata tea, Mummy ta shigo dakin tana kallansu ta ce "Zakici abincin ne?" Ummi ta girgiza kai ta ce "Na koshi" Mummy ta ce "Allah ya sauwake". Bata wani jima a nan b ta koma dakin da Rafi'ah take, tana nan kwance bakinta na motsi tana ta addu'a, kujera taja ta zauna itama, duk dakin yayi shiru sai numfashinsu kakeji a hankali, jin an turo kofar yasa Mummy ta daga kanta tana kallan Mami data shigo, Mummy ta ce "Ya mai jikin?" Mami na kallan Rafi'ah ta ce "Ai taji sauki, cikinma ya daina ciwan, sun sallamemu yanzu, ya jikin Rafi'ah?" Mummy ta ce "Da sauki itama" Mami ta kara kallanta ta ce "Bari mu wuce gida ga dare yayi, gobe na dawo" Mummy ta ce "To Allah ya kara sauki, a mata sannu" Mami ta fice a dakin bayan tayiwa su Ammi sallama. Karfe 11 na dare Abba ya shigo dakin da Daddynsu Khairiyya sai Abi dan tin dazu da sukazo aka hana kowa shiga wajenta sai data tashi, sun tausaya mata matuka ba kadan ba, Daddyn Khairiyya ya dinga mata addu'a da nasiha iri iri, haka Abi ma yayi ta mata kafin sukai musu sallama, Ammi ta kalli Mummy dake zaune ta ce "Hajiya zamu tafi, Allah ya kara mata lafiya" Mummy ta ce "Mungode Allah ya tsare" Khairiyya dai sai kallan Rafi'ah dake kwance take har suka fita a dakin, ba jimawa Abba ya dawo dakin, ya kalli su Anty Amina dake zaune ya ce "Bari na maidaku gida" kamar jira take ta mike tana kallan Mummy ta ce "Allah ya sauwake" Mummy ta ce "Yauwa Amina mun gode" Abba ya kalli Abdul dake zaune ya ce "Kaifa?" Ya girgiza kai ya ce "Zan zauna anan Abba" Abba ya ce "To shikkenan, bari in kaisu, Umminsu ma gida zata kwana sun sallameta" Mummy ta ce "Ehh yafi kam taje ta huta, Allah ya tsare hanya" Abba ya ansa da Amin kafin ya fita a dakin. Ta6e baki Anty Rahama tayi ta ce "Kawai kinsamu zaman asibiti kamar dole, wallahi da niyyata sanda Umma da Ikleemah zasu tafi muma mu wuce" Anty Amina ta ce "Haba Anty, idan ban zauna ba ai zasuce murna nake, bakiga yadda na dinga kakalo kukan karya ba?" Har Anty Rahama zatai magana sai tayi shiru saboda Abba data hango yana tahowa da Ummi, Anty Amina na kallansu ta dauke kai, bayan sun karaso ya bude lock din motar Ummi ta shiga gaba su kuma suka shiga baya yaja motar suka bar clinic din.
Daren ranar kwana Ummi tayi tana salla tana kai kukanta ga Allah, tayi kuka ba kadan ba a daren nan, kafin safiya ita kanta tasan ta rame tsabar damuwa, tana idar da sallan asuba ta shiga kitchen tayi dan~wake da kunu sannan tasa a basket, sama ta koma dakinta tayi wanka ta shirya, tana gamawa Abba ya dawo daga masallaci, bayan sun gaisa ya kalli agogon dakin ya ce "Karfe 7 saura yanzu, kinyi breakfast ne?" Ta girgiza masa kai ta ce "Idan naje caan zanci" Abba ya ce "No, kafin na shirya kiyi breakfast"daga haka ya juya ya koma dakinsa, half cup na kunu kawai ta iya sha, shima turawa tayi ta shanye bawai son ranta ba, bayan ta gama ta ajiye cup din ta shiga dakin Saudatu mai aikinta, tana zaune akan sallaya tayi shiru itama, duk da ba wani zama tayi da Rafi'ah ba, jiya data ganta sai da tayi kuka, haka kawai takeji tana san yarinyar, jin an rufe kofar tayi saurin jaa baya tana kallan Ummi ta ce "Ina kwana Ummi" Ummi ta ce "Lafiya kalau, jiya mun dawo kinyi bacci" ta ce "Ehh nayi bacci, ya Anty Rafi'ah da jiki?" Ummi ta ce "Da sauki, yanzu zamu koma, da rana ki dafa komai ma kici, ba sai an kai asibiti ba" Saudatu ta ce "Toh, Allah ya kara mata lafiya" daga haka Ummi ta mike ta ce "Ameen" tana fita a dakin Abba na sakkowa, ta dauka basket din suka fita zuwa parking lot, Mustapha ya musu ya mai jiki sannan ya bude gate suka fita, sosai Abba ya dinga kwantarwa Ummi hankali a mota, ba irin misalan da bai mata ba dan hankalinta ya kara kwanciya, kuma Alhamdulilah ta rage fargaban da takeji sosai. Bayan sunyi parking ta dauko basket din suka shiga ciki, Abba ne ya bude kofar dakin ya shiga Ummi ta bishi a baya, kan gadon duk suka nufa, tana nan zaune da hijab a jikinta, da alamu salla ta gama idarwa, Ummi dake kallanta ta ce "How are u daughter" ta dan goge hawayen idanta ta ce "Alhamdulilah Ummi" daga haka ta kalli Abba da shima kallanta yake ta ce "Ina kwana Abba" ya ce "Lafiya kalau Mamana, ya jikin ki?" Ta ce "Da sauki Abba" nan suka gaisa da Mummy ma, Abdul ya gaishe dasu shima, Rafi'ah dai na zaune akan sallaya ta lula duniyar tinani, idan ta tuna abinda Mummy ta fada mata sai ziciyarta ta buga, wai itane dauke da cikin Yusuf, jin Ummi na ta6a ta yasa tayi saurin zabura, lokaci daya hawaye ya shiga zirya a idanta, Ummi ta sauke ajiyar ziciya ta ce "Ko so kike na koma gida?" Ta girgiza kai a hankali tana share hawayen idanta, she can't believe that she's pregnant, ta kara rufe idanta da hijab dinta ta fara kuka tina ko shekara 18 bata cika ba, saura two months ta cika shekara 18, bayan Abba ya fita tare da Abdul Mummy ta ce "Aiba a kanki aka fara saki da ciki ba, kinganta harta yi shiru tindana gaya mata tana da ciki ta daga hankalinta" Ummi ta shafa kanta cikin rarrashi ta ce "Stop crying daughter, duk abinda kika gani jarabawace daga Allah, watarana sai labari, ki daina damun kanki ko dan cikin dake jikinki ma" rungume Ummi tayi ta ce "Ina kokarin yin hakan Amma Ummi bana iyawa" Ummi ta ce "Zaki iya Rafi'ah, just forget about Yusuf, ki manta da kin ta6a rayuwa dashi" kwanciya tayi liif a jikin Ummi tana sauke ajiyar zuciya. Karfe 8 Ammi ta karaso asibitin da warmers din abinci, sosai taji dadi ganin Rafi'ah nacin dan wakenta sosai, kunu ne dai bata wani sha ba, da azahar Mami ma sukazo ita da Sadeeq, minti 10 sukai suka koma gida, wajajejn karfe 2 su Umma dasu Anty Rahama suka iso, carton din maltina Umma tasa aka siyo aka ajiye musu. Kwanan Rafi'ah 3 a asibitin aka sallameta bayan an bata magunguna sabi, by now ta dan sake saboda kullum Ameera na zuwa asibiti ita da mamanta, anan take kara kwantar mata da hankali, Mami ma kullum sai tazo ta kawo abinci, haka Ammima itakam safe rana dare sai ta kawo abinci duk da hanata da Ummi take amma bata fasawa, kafin a sallameta 'yan uwa da abokan arziki su kaita zuwa dubata, Yusuf ya sha tsinuwa a gun Gwaggo ba kadan ba, motsi kadan saita tsine masa. Washegarin randa aka sallameta tana zaune a daki ita da Ameera, gaba daya ta damu dan Ameera sallama ke mata zata tafi zaria makaranta ta samu admission, Rafi'ah ta fashe da kuka ta ce "Zanyi missing dinki Ameera, Allah bazanji dadi ba" Ameera ta share mata idanta ta ce "Duk bayan sati biyu zan ringa zuwa, nidai kawai ki daina damuwa ki kula da kanki sosai" Rafi'ah ta kamo hannayenta ta ce "Insha Allah friend, Allah ya bada sa'a yasa ki fara a sa'a" Ameera ta ce "Ameen Fatima" duk jikinta sanyi yayi ganin yadda Rafi'ah ke share hawaye, jin hawaye na zuwa mata tayi saurin daga mata hannu ta fita a dakin, a corridor ta goge idanta sannan ta sakko downstairs, tayi wa Mummy da Ummi sallama, Ummi ta mata fatan alkhairi sannan ta bata leda me dauke da tirare da sleeping dress, da kyar ta kar6a sannan ta kara musu sallama ta tafi, Ummi ta kalli Mummy dake zaune ta ce "Anty bazaki koma gida ba, ai jikinta yayi sauki?" Mummy ta ce "Anjima zan tafi Zainab, Jawad ma yau zai dawo" Ummi ta ce "Allah ya dawo dashi lafiya", tashi Ummi tayi ta ce "Bana leka Rafi'ah ko zata ci abinci" Mummy ta ce "Ohk to" daga haka Ummi ta dauki warmer da plate ta haura sama.

_ALHAMDULILAH, anan na kawo karshen littafin *SHARIK HAYATI* part one, ina rokon Allah ya yafemin kuskuren danayi ya kuma bani ikon rubuta abinda shine dai dai_ 🙏🏻

_Special thanks to the members of my Groups, wallah u people are the best, ina sanku sosai da sosai 💞💞_ _And again my Kk 🥰 i luv u so much sweetheart, u are always supporting me right from the beginning, billahil azeem ina sanki Dije ta, my Jiddah soyayyarki is endless_ 😍, _AISHA SHEHU can't forget with u sister, Fatima is thanking u again and again Allah ya raya Na'eem ya bashi ilimi me inganci_ 😇, _Then my FANS 😇 Billah ina sanku a duk inda kuke sisters, only God knows how much i luv u people, ina muku fatan alkhairi duniya fil akhirah 😘_ .

_08103810398_
Chapter 59 · 0% Book details