← Book details Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 41 OF 59

Sashe 41

Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 4 min read

sunanta? but you used to called her Fatima" a hankali yayi murmushi ya ce "Her name is Rafi'ah, she's not here" Khairiyya dake kallansa ta ce "Why Yaya? Ba kace she's ur best friend ba, why is she not presence at ur marriage?" A hankali ya ce "Soon zakiga tazo" a hankali ta sakeshi ta koma dai dai saitin kofa tana kallan masu shiga da fita ko zataga Rafi'ah amma babu, ganin Yusuf da abokansa sun fita a hall din ta 6ata fuska kamar zatai kuka, dan tasan an gama event din kenan. Da dare Rafi'ah nasan kunna wayarta amma taki sabida batasan kiran Yusuf ya shigo mata, haka nan ta hakura har bacci ya dauketa. Washegari ya kama Sarurday, sassafe ta kunna wayarta ta masa text sannan ta kashe wayar ta sauko dan taya Ummi aiki. Yusuf na zaune a dakin Aliyu text din ya shigo, ya gama karantawa sannan yayi murmushi, ji yake duk duniya babu wacce yakeso irin Rafi'ah" Aliyu dake kallansa ya ce "What's that" Yusuf ya ce "She send me message now, that i shouldn't worry, ta bani time ne nayi hidimar aure naji da baki" Aliyu ya ce "Yanzu hankalinka ya kwanta kenan? Sai kayi baccin da bakayi da daddare ba kafin lokacin daurin aure yayi" Yusuf ya ce "But ba haka naso ba, i need to hear her voice, i missed her much" Ali ya ta6e baki ya ce "Kasan dai bazaka je wajenta a yau ba kam, ba kuma gobe ba, ba jibi ba, sai dai ko gata" Yusuf ya kai masa duka ya ce "Karka kaini har gata Malam, jibi zanga abata" daga haka ya kwanta yana murmushi jin answer da Aliyu ya bashi. Karfe 10 Abba ya fito cikin shirinsa na alfarma yayi breakfast sannan yayi wa Ummi sallama zai tafi daurin auren Yusuf, ta masa Allah ya kiyaye sannan ta ci gaba da gyaran dakinta. Jawad ne tsaye a kofar gidansu Aliyu ya jinginu da motarsa, Aliyu ya fito ya mika masa hannu ya ce "Barisster always behaving somehow, tinba yau ba muke tare amma sai kazo kayi parking a waje, kuma wallahi Mama jiya sai data tambayeka" Jawad ya danyi murmushi ya ce "Zanzo na gaisheta but gobe insha Allah" Aliyu ya ce "Allah ya kaimu, zakaje daurin auren Yusuf ne?" Harara Jawad ya dalla masa ya ce "Kai din dai daya zame maka dole, over my dead body" Aliyu ya dinga dariya ya ce "Pls, yana ma ciki yana shiryawa, kaga kaima kaci manyan kaya kuma kayi kyau sai dai ba babban riga" Jawad ya bude motarsa ya ce "Pls let me go Ali, nima daurin auren wani zanje, tare mukai masters" Aliyu ya ce "Friend dinka?" Jawad ya kalleshi sannan ya kunna motarsa ya ce "Kasan banda friends, i only have good mates" Aliyu na daga masa hannu yana dariya ya ce "Allah ya shiryeka kai dai, still dai friends din ne" Jawad baice komai ba ya juya kan motarsa ya nufi gidan Kawu daga nan ya wuce. Karfe 11:30 aka daura auren Yusuf Muhammad da Hauwa Sa'eed (Jiddah), uncountable people sun shaida dauruwar wannan aure, bayan nan akaci akasha sannan kowa ya watse. Yinin Ranar Rafi'ah a daki tayi shi tana kallo, duk da abin na damunta but she's just trying to calm herself musamman da taji muryar Abba ya dawo, lokaci lokaci Ummi kan lekata taga kallo take hankali kwance, nan kuwa ita kadai tasan abinda ke daminta deep down. Bayan isha aka shirya amarya tsaf dan kaita dakinta, Umma tayi mata fada sosai da sosai a gaban jama'a, Jiddan na kuka haka aka tafi da ita gidan Yusuf, gidan yayi kyau sosai komai sabo ga kamshin turaren wuta dake tashi. Yusuf na zaune dakin Aliyu Sameer da wani abokinsu Mukhtar suka shigo, Sameer ya mika masa ledan kaza da fresh milk ya ce "Karfe 10 saura fa Yusuf, muje mu raka ka mu wuce gida" Yusuf ya mike suka fita, shima kansa jikinsa duk yayi weak, gani yake kamar Rafi'ah fishi take dashi. Har karfe 12 Rafi'ah batai bacci ba, da taji motsin Ummi zatai pretending kamar bacci take, har Ummi ta rufeta da blanket ta fita ko motsi batai ba, Ummi na fita ta mike ta zauna, sai a sannan hawaye ya gangaro idanta, tayi saurin sharewa sannan ta mike ta shiga toilet tayi alwala ta dawo tasa himar ta tada sallah. Washegari wajajen karfe 10 Jawad ya fito daga dakinshi ya nufi dakin Abi, yana nan zaune da newspaper a hannunsa yana karantawa, Jawad ya durkusa ya ce "Ina kwana Abi" Abi ya ajiye newspaper hannunsa ya ce "Lafiya kalau Ahmad, yau bazaka fita bane?" A hankali ya ce "Zan fita amma sai da yamma" Abi ya ce "Masha Allah, yau na kira Kawunka nace Maminku ta dawo" murmushi ya danyi ya ce "Allah ya saka da alkhairi Abi, Allah kuma ya kara kiyaye gaba" Abi ya ce "Ameen" shafa kansa Jawad yayi ya rasa ta ina zai fara wannan maganar, caan dai yayi karfin hali ya ce "Abi dama inaso muyi magana ne" Abi dake kallansa ya ce "Go on Son i'm all ears"...
Chapter 41 · 0% Book details