← Book details Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 49 OF 59

Sashe 49

Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 10 min read

*I dedicated this page to the members of my groups, i love u all and thanks for d comments i appreciate sisters 🥰*
_08103810398_
[8/7, 2:53 PM] Zarah: *_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_39_

Anty Rahama na tsaye rike da hannun Ikleemah a ward din da akai admitting dinsu, lokaci~lokaci ta kan jijjiga hannunta tana kiran sunanta ko zata tashi, Anty Amina dake tsaye bakin kofa tana kallansu ta ce "Anty Rahama ki bar jijjigata tunda sunce very soon zata tashi" dago kanta tayi tana kallan Anty Amina kafin ta fara magana kamar haka "Na rantse da Allah, na rantse da wanda ya halicci uwata da ubana Rafi'ah bazata zauna a gidan Yusuf ba, sai tayi nadamar auransa a rayuwarta, sai ta dandana bakin ciki kamar yadda tasa Ikleemah" a hankali Anty Amina ta karaso inda suke ta dafata ta ce "Kamar anyi an gama, amma yanzu hankalinmu ya dawo wajen Ikleemah kafin komai" tana rife bakinta wani Doctor ya bude kofar dakin Abba na biye dashi a baya, Abba ya karasa kan gadon yana kallan Ikleemah dake kwance kamar gawa ya ce "Allah ya baki lafiya" Anty Rahama ta ce "Ameen" Doctor na gyara mata drip din hannunta ya ce "Soon zata tashi, so karku daga hankalinku ba wani damuwa" Abba ya ce "Fatanmu kenan, amma menene yake damunta Dr" kallan Abba yayi kafin ya ce "We can talk in my office yallaboi" Abba yabi bayansa suka fita zuwa office dinsa, bayan sun zauna Doctor ya kalleshi ya ce "How are u related with her? Naga kamar kaine mahaifinta" Abba ya ce "Yess i'm a dad to her but not biological father" Doctor ya ce "Do u have any heridity of Heart Attack either family dinku kona mahaifiyarta" Abba ya ce "Yess we have" Doctor ya ce "Allah ya karawa masu shi lafiya, i'm sorry to say itama ta kamu dashi" Abba ya danyi jiim kafin ya ce "What the next thing now" Doctor ya ce "Eh insha Allah zata tashi anjima, zamu daurata akan magani, amma ina ga ba lallaima ta kwana ba" Abba ya mika masa hannu ya ce "Mungode sosai" Doctor ya ce "Allah ya bata lafiya yallaboi" daga haka Abba ya fita a dakin ya wuce masallacin dake asibitin, bayan an idar da sallan la'asar ya dawo ward din da suke, a zaune duk ya samesu sunyi jugum Abba ya kalli Anty Rahama ya ce "Ko zaki kira mahifinta ki sanar masa" ta hade fuska ta ce "Sai dai idan an sallamemu kuma, mutumun da ko nemanmu baya yi" Abba ya ce "Koma menene u let him know, uba ai uba ne, kuma rabuwa ba hauka bane, dole ne yasan abinda yake damin 'yarsa" Anty Rahama da idanta ya kawo ruwa ta ce "Menene yake damunta Ya Muhammad? Dan Allah ka fadamin ina ba mutuwa zatai ba" Abba dake kallanta ya ce "Ba kuka zakiyi ba, kiyita mata addu'a kawai" Anty Rahama ta goge idanta ta ce "Menene yake damun Ikleemah Yaya" Abba ya ce "Itama ta kamu da ciwan zuciya, yace zai sata akan magani idan ta tashi, so dont worry about Allah ya basu lafiya baki daya, zanje na sallami bakina da suka zo daurin aure" daga haka ya fita a dakin Anty Rahama ta bishi da kallo, yana fita ta rushe da kuka tana jijjiga Ikleemah ta ce "Na shiga uku na, Ikleemah ciwan zuciya? Nida nakewa wasu dariya yau gashi a jikin 'yata na shiga uku Umma ya zanyi inasan 'yata wallahi" Anty Amina dake kuka itama ta ce "Mun shiga uku, dan Allah suce ba gaskiya bane". Haka suka dinga rusa kuka har saida Doctor ya shigo ya musu magana sannan suka sassauta kukansu. Parking Abba yayi a kofar gida ya fito sannan ya shiga ciki, wayar Ummi ya kira yace ta sameshi a parlorn shi, ba jimawa ta shigo cikin shigarta ta alfarma, kana kallanta kaga uwar amarya sai kamshi take da gold dinta a wuya da kunne, zama tayi a gefen Abba ta ce "Ya jikin Ikleeman?" Ya ce "Da sauki, wai ciwan zuciya ne itama" Ummi ta dan zaro ido ta ce "Subhanallah, Allah ya bata lafiya, anyi discharging dinta ne?" Abba ya ce "Noo, sunce dai may b anjima, an kai abincin da nace akai guest house?" Ta ce "Ehh, an kai dazu" Abba ya mike ya ce "Bari naje na sallami baki, sannan ku hakura da wannan event din da zakuyi" Ummi ta ce "Nifa bani zanyi ba, Anty Halima ce ta hada musu" Abba ya ce "To kice mata a barshi kawai, akwai marar lafiya a gida" ta ce "To Allah ya sauwake" daga haka ya fita a parlorn.
Da kyar Ummi ta shawo kan Anty Halima aka fasa kamun nan, dan cewa tayi ita ba ruwanta da ciwansu sai anyi kamu, wai idan sune da yanzu suna abinda yafi haka. Duk da haka sai da Mummy ta kira mai hoto sukai ta hotuna a compound din gidan bayan anyi decorating dinsa, sosai Rafi'ah tayi kyau kamar ka saceta ka gudu, ganin Yusuf da friends dinsa sunzo yasa Ummi ta koma cikin gida, Mummy kuwa hotunansu suka sha da Yusuf har kusan Magrib sannan suka tafi, daga haka kowa ya watse, Aliyu ne ya dauki su Rafi'ah ya maidasu gidansu Ameera.
Umma ce zaune a gefen Ikleemah tana bata tea a baki, Anty Rahama da idanuwanta suka kumbura tsabar kuka tana gefe a zaune kamar marainiya, bayan Ikleemah ta koshi Umma ta kalli Anty Amina ta ce "Yanzu dai rashin lafiyar Ikleemah shine gaba da komai, idan ta samu sauki na tabbata komai zai tafi dai dai rannan zasu gane banbancin aya da tsakuwa" su dai suna zaune ba wanda yace kala a acikinsu, kowa da abinda yake sakawa cikin ransa musamman Anty Rahama gani take kamar su Ummi dariya zasu mata.
Da damuwa Anty Khadija ta shigo dakin da Ummanta take, bayan ta zauna ta ce "Umma mahaifiyarta tana da kishiya, sai dai kuma tafi zama a Abuja akan a nan, inaga kafin su koma zuwa gobe ni zanje" Umma ta ce "Hakan za'ai, shima Malam da mukai waya cewa yayi baisan me faru ba aikin yaki yi, yana da tabbacin aurin ba zai dade ba" Anty Khadija tayi wani murmushi ta ce "Ai dama bai cancanta ya dade ba, ai Yusuf Umma bazai ta6a samun kwanciyar hankali ba" Umma ta mike ta fita a dakin sakamakon kiran Malam daya shigo wayarta.
Karfe 9 bayan sallan isha su Mummy suka shirya Rafi'ah tsaf, tinda aka fara shiryata take hawaye, bayan an gama Mummy ta kama hannunta zuwa dakin da Ummi take, Mummy ta damka hannunta cikin na Ummi ta ce "And pls don't cry daughter" daga haka ta fita a dakin, silently Ummi ta kira sunanta, ta dago idanta da suka cika da hawaye ta ce "Ki yafemin Ummi na" rungumeta Ummi tayi trying hard not to cry ta ce "Allah ya miki albarka daughter, Allah yasa auranki ya zama abin kwatance, i will miss u daughter" Rafi'ah ta fashe da kuka ta kankame Umminta, bude kofar dakin akayi Abba ya shigo, ya zauna gefensu ya fara magana cikin rarrashi, sosai ya lalla6a Rafi'ah hade da mata addu'an samun sa'ar aure, bayan nan shida Ummi suka mata nasiha sosai da sosai, a karshe suka mata addu'ah, duk sai jikinta yayi mungun sanyi, ta rungume Abba tana kuka, da kyar ya raba ta da jikinsa ya fita a dakin, Ummi ta kama hannunta suka fito, Mummy ce ta lullu6a mata alkyabbar jikinta suka sauko downstairs har lokacin kuka take da haka suka wuce da ita.
Minti 14 ya kaisu gidan Yusuf, aka shiga da Rafi'ah har dakinta, zuwa karfe 10 kowa ya watse sai Mummy, Gwaggo da Anty Salma, sosai da sosai suka kara mata nasiha, da zasu tafi gwaggo harda kukanta, Rafi'ah na kuka haka suka tafi suka barta, koda suka fito Jiddah na zaune aparlor taci uban kwalliya tana kallo, ko kallansu batai ba bare susa a rai zata gaishe su, Gwaggo sai mita take har suka fita, Mummy ce ta jasu zuwa gidanta dan a caan zasu kwana. Karfe 11 Yusuf ya shigo gidan, ajiye dayan take away yayi ya shiga da daya, a kwance ya samu Jiddah tayi rub da ciki, ya hau kan gadon ya dagota ya ce "How are u?" Ta fashe da kuka ta kankameshi, a hankali ya ce "Ga abinci na kawo maki, amma ai kinmin alkawari u won't cry ko?" hawayenta ta share ta koma gefe ta zauna, Yusuf ya kara matsawa inda take ya ce "Take ur food, and stop crying" kai kawai ta gyada masa, ya ajiye mata take away din akan bed side drawer ya ce "Good night" da ido ta bishi harya fita ya rufo mata kofar, ta fashe da kuka tayi wurgi da take away din. A kan dinning ya dauki ledan daya ajiye ya shiga part din Rafi'ah, tana zaune a parlor tana kallon wani series, tayi saurin dago kanta tana kallanshi, bude hannayensa yayi ta taso da sauri tayi hugging dinsa, ya rungumeta shima yana shafa bayanta ya ce "This was my dream always" Rafi'ah ta sake shi tana kallansa tayi murmushi, ya bata side hug yana kissing forehead dinta ya ce "I luv u" ta ce "I luv u more" hannunta ya kama suka shiga cikin daki, ta zauna akan stool ta dan turo baki ta ce "I'm missing my parent Doctor" durkuswa yayi ya kamo hannayenta biyu ya ce "Not when u have me dear, tashi muyi sallah" make kafada tayi ta ce "Ai nayi sallah a gida" ya ce "I know, wancen da wannan ba daya bane" ta ce "To amma ai nace maka nayi" ya ce "Kinyi kuka ba, ur eyes are red" sauke kanta tayi ta daina kallansa ta ce "I'm hungry kuma" babban rigarsa ya ajiye a gefenta ya ce "Idan kikai sallah sai kici abincinki" ta dan kalleshi sai kuma ya ce "Sai bacci" ta dan turo baki ta ce "Kafana ciwo yake i can't walk" tashi yayi ya dagata kamar Baby suka shiga toilet, da alwala suka fito yaja su sukai sallah sannan ta jawo take away din ta fara cin kazar dan yunwa takeji bama wasa ba, shi dai kallanta kawai yake yana murmushi harta gama, ta mike ta dauko cup ta sha fresh milk sannan ta shiga toilet tayi brush ta fito tana kallansa ta ce "Doctor" ya ce "Matar Doctor" tayi saurin rife fuskarta ta ce "Banaso" ya ce "Nine bakyaso" ta dan kalleshi sai ta ce "Tsokalan ne i don't want" ya kamo hannunta ta zauna gefenshi ya ce "Gist me, meyasa aka fasa event din?" Rafi'ah ta kwanta a jikinshi ta ce "Ikleemah ne ba lafiya" ya ce "Waye ita?" Ta ce "Wacce ta kai maka abinci first time kazo gidanmu" yaja hancinta ya ce "Kice wacce kike kishi da ita" ta dan yatsine fuska ta ce "Ni ina ruwana da ita" bakinshi ya daura akan nata tayi saurin komawa baya ta ce "Are u not sleepy?" Ya ce "Of course, kwana zamuyi muna hira yau" ta dan zaro ido ta ce "Oh oh, ni bacci nakeji" ya ce "Ni banajin bacci to, ya zamuyi" ta dan bude hannayenta alamun bata sani ba ta ce "Nasan kuma kanaji" ya ce "Banaji, i can spend the whole night without sleeping" dariya ta danyi ta koma baya ganin yana kokarin kamota, ya jawota jikinshi ya ce "Sai munyi hira fa" tana dariya ta ce "Then let me sleep sai na baka labarin" ya kara rungumeta ya ce "Bacci zakiyi" ta ce "I won't" kwantar da ita yayi yana jaan hancinta ya ce "Good" tayi shiru tana saan kwace jikinta ya ce "Wait,,, let me show u something" tsayawa tayi tana kallan phone dinsa da yake dannawa, kashe hasken wayar yayi sannan ya kashe wutan dakin, ta dan zare ido ta ce "Doctor" sai kuma ta yatsine fuska kamar xatai kuka ta ce "Pls stop".
Chapter 49 · 0% Book details