Sashe 3
Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
A hankali ta juyo ta kar6a ledan drugs din ta ce "Thank you" daga haka ta juya ta nufi inda motarsu yake. Mustapha na ganinta ya tashi da sauri ya bude mata back seat yana ta murmushi ya ce "Kinsan turawa nawa na gani sun wuce daga fitar ki?" Rafi'ah ta danyi murmushi ta ce "To idan munje gida zan gayawa Ummi sai kuyi magana" ya sakar mata murmushi yana shafa keyarsa ya ce "Haba haba ai maganar bai kai aje gun Hajiya ba, ni ina ni ina wadannan turawan" Dariya ta danyi taci gaba da danna wayarta shi kuma yaja motar suka fita a clinic din. Suna isa gida Mustapha yayi parking ya fito ya bude mata door ya ce "A huta gajiya" ta ce "Nagode" daga haka ta nufi entrance din gidan, a hankali ta murda handle din kofar ta shiga, sai da zuciyarta ya buga ganin kallan da Ummi ta mata, ta saurin sunkuyar da kanta ta ce "Kiyi hkr, i just saw ur missed call now" Ummi ta dauke idanta a kanta ta maida kan TV ta ce "Take ur breakfast now, after all kizo" akan sofa ta ajiye ledan drugs dinta sannan ta nufi kan dinning ta dauka plate da serving spoon sannan ta bude warmer. Few minutes ta gama cakalar abincin data diba sannan ta dauka glass cup ta bude dispenser ta diba ruwa kafin ta koma parlor ta zauna, ledan drugs dinta ta jawo ta balla wanda take sha as usual sannan ta mike zata bar parlor. "Rafi'ah" sunanta da Ummi ta kira ne yasa ta tsaya, ta juyo da sauri ta ce "Ohh Ummi na manta kince idan na gama" daga haka ta koma gefen mahaifiyartata ta zauna, Ummi ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Yanzun nan na gaya maki abu har kin manta Rafi'ah? Me yake daminki ne two days? Or are u sick this days?" Girgiza mata kai kawai tayi, Ummi ta ce "To Allah ya shiryeki, can u remind how many days baki kira Anty Halima kin gaisheta ba?" Turo baki ta danyi kafin ta ce "Ummi ce maki tayi bana kiranta?" Ummi ta mata dakuwa ta ce "Ko karya ta miki? I don't know what's wrong with u this days, gaba daya kinyi turning upside down" Rafi'ah ta sunkuyar da kanta ta ce "Wallahi is her fault Ummi, haka kawai sai tai ta min wata magana da bana so" Ummi ta dalla mata harara ta ce "Do as u wish, ko yayyankaki take banga dalilin rashin kiranta ba, duk duniya ina da wacce ta fita ne, 'yar uwata daya tak a duniya kiyi kusan sati baki kira kinji lafiyarta ba, idan baki kirata ba who will u call?" Shiru tayi ta dinga jujjuya ring din hannunta bata ce komai ba, Ummi ta mike ta ce "Abbanku ma yace baki kira kin gaishe shi ba" Murmushi tayi jin an anbaci Abbanta ta ce "Ai Ummi na fita very early today, da bazan manta ba" Ummi ta ta6e baki ta tattara plate din kan dinning ta wuce kitchen. Phone dinta dake kan TV stand ta dauka tayi dialing number Abbanta, bugu biyu ya dauka hade da sallama bayan ta amsa ya ce "Good morning Mummy nah" ta dan langwa6ar da kanta ta ce "Morning Abba, how is work?" Ya ce "All fine Mamana, u missed school today why?" cike da shagwaba ta ce "Abba naje clinic yau fa kuma ni kadai na" Abba ya sauke ajiyar zuciya ya ce "This is not safe at all, ya za'ai ta barki ki fita ke kadai?" Shiru kawai Rafi'ah tayi tana jujjuya ring din hannunta, Abba ya ce "How many days baki kira Hajiya kun gaisa ba? She called me day before yesterday and yesterday too still complaining, meya hanaki kiranta ki gaisheta? cewa tayi ma ni nake hanaki zumunci da ita" ta turo baki ta ce "Abba dazu fa Ummi ma saida tamin fada, kuma kona kira Mummy sai tai tamin maganar aure as small as i am" Murmushi Abba yayi kafin ya ce "And that not the reason da zaisa kiyi sati daya baki kirata ba Mamana, remember she the only one of your mother's sister" a hankali ta ce "To" Abba ya ce "Not just To alone, idan baki kirata ba wallahi Abba zai manta da Mamansa yayi mata fada" ta danyi murmushi ta ce "Insha Allah Abba, when are u coming back Abba, muna ta missing dinka nida Abdul" cike da rarrashi Abba ya ce "Worry not Mamana, zan dawo ending week din nan insha Allah" ta ce "Allah ya kawo ka lafiya Abba" ya ce " Ameen, try and be taking ur drugs kinji ko" ta ce "Yanzu ma nasha Abba" ya ce "Good, we will talk ltr in the evening i have a lot to cover" ta ce "Allah ya tsare" ya ce"Ameen Mamana" daga haka yayi hanging call din. Kwanciya tayi akan sofa kafin ta bude lock din wayarta ta kira number Mummy, yana fara ringing ta dauka, Rafi'ah tayi kasa da murya ta ce "Assalamu alaikum" ba tare da Mummy ta amsa sallamarta ba ta ce "Ai dama ubanki kadai zaice ki kirani kiyi" Rafi'ah da mood dinta ya canza ta ta6e baki ta ce "Bafa ki amsa sallamar ba Mummy kuma ba Abba yace na kira..." kafin ta rufe bakinta Mummy ta ce "Keep that ur small mouth shut, inba iskanci irin naki ba kwana nawa baki kirani ba? Ko danni ba Zainab bace?" Rafi'ah ta bubbuga kafarta a kasa ta ce "To kiyi hakuri, ni wallahi zancen auren da kikeminne banaso shiyasa bana san kiranki" Mummy taja dogon tsaki ta ce "Aida dangin ubanki ne da yanzu kin ishesu da kira, kowa da dangin uwarsa yake fara alfahari amma banda ke saboda wauta ta miki yawa, inba hauka ba me suke muku wanda kuke jin dadin sa?" A hankali Rafi'ah ta ce "To kiyi hakuri, i know i hurt but that's not my intention, how will i not call u Mummy, bayan kinyi 1 month bakya kasar, wallahi ina missing dinki sosai" Ajiyar zuciya Mummy ta sauke kafin ta ce "Fine, ita kuma mahaifiyarki zan kirata tana tina muku cewa ni yayarta ce, ni kadai take dashi a duniyarnan tinda ba uwa ba uba" Dariya tayi a hankali ta ce "Ai munsani Mum, tana kuma gaya mana, ni maganar aure ne banaso kina min wallahi" Mummy ta ce "Bari dai na dawo kasar kafin komai, aure ko bakyaso sai kinyi shi tinda ba zama zamuyi tayi dake ba" Rafi'ah ta yatsine fuska ta ce "Ai Abba is not in support, SS2 fa kawai nake Mummy, why not idan na gama degree" Mummy ta ce "Allah ya kiyaye, kina gama secondary school zakiyi aure, shiyasa nake tina miki ki tsaida miji, shi kuma Abban naki idan bazai aurar dake ba sai ya bani ke tinda shi gani yake kamar labari kawai nake, indai ina raye sai dai ki karasa karatunki a gidan miji" Rafi'ah ta dan ta6e baki a hankali ta ce "Ai iyayena ma ba yarda zasuyi ba" Cike da masifa Mummy ta ce "Yimin bori dan ban haifa ba, da ace ina da 'ya'ya mai zaisa na saka miki ido Rafi'ah, ai a rashin babu ne" jin mood dinta ya canza yasa Rafi'ah yin dariya sannan ta ce "Just joking fa Mummy, kiyi hakuri" Mummy ta ce "Sai anjima zan kira idan na koma gida" bata jira cewar Rafi'ah ba tayi hanging call din. Wajajen karfe 3 na rana Rafi'ah ta tashi daga nauyayyen baccin da yayi gaba da ita, ta mike a hankali ta shiga toilet tayi brush sannan ta doro alwala ta fito, hijabi har kasa ta saka sannan ta hau kan sallaya. Bayan ta idar tayi addu'a sannan ta cire hijab din ta dauka phone dinta dake kan gado ta fice a dakin. Tafiya take cikin quick light step har ta karasa saukowa daga stairs din, ta karasa cikin falon tana kallan Ummi dake marking papers din gabanta, saam bata kula da luvly brother dinta dake zaune akan dinning ba, bayan ta zauna gefen Ummi ya taso a hankali ya cire scarf din kanta, tayi tsaki ta juya tana kallansa ta ce"Ka dawo kenan ko?" daga haka ta kwace hulanta ta saka, tana juyawa ya kara cire mata yana dariya, kamar zatai kuka ta ce "Ummi wallahi zan zane Abdul, kiga abinda yakemin" Ko kallansu Ummi batai ba bare tayi magana, Abduljalal ya zauna gefenta ya dora hannunsa a shoulder dinta ya ce "How are u Anty nah, yau a school anata tambayan ki nace kinje follow-up Clinic" a hankali ta ce "Ohk". Bayan Ummi ta gama marking dinta ta dago tana kallan Rafi'ah da gaba daya tayi collapsing jikin Abdul tana kallo, Ummi ta dalla mata harara ta ce "Tashi ki zauna" mikewa tayi da sauri tana turo baki ta ce "To Ummi kice ya tashi na kwanta, mu 3 akan sofa daya" Ummi ta ce "Ke ki koma caan mana" ta make kafada ta ce "Ni kusanki zan kwanta" tana rife bakinta Abdul ya tashi ya nufi dakinsa yana murmushi ya ce "Na kar6i girman". Daga haka ta koma ta kwanta tayi pillow da cinyar Umminta, bayan few minutes Ummi ta ce "What did u told Abba in the morning?" Tashi Rafi'ah tayi tana kallanta ta ce "I haven't told him anythi..." Kallan da Ummi ke mata yasa tayi shiru ta sunkuyar da kanta, Ummi ta ce "This should be the last zamuyi abu baya nan ki kirashi ki gaya masa, sau nawa ina kaiki Clinic muna kar6an magani?" Tayi shiru still kanta na kallan kasa, Ummi ta ce"Talk now, how many times? Ya kirani dazu yana ta fada na barki kin fita ke kadai, ba Mustapha nace ya kaiki ba? shekara 17 ace bazaki iya zuwa ki kar6a common drugs ba, i still don't like yadda Abba yake treating dinki wallahi, nayi magana harna gaji, wallahi Abdul ya fiki iya abubuwa, ya dawo kamar shine gaba dake, when will u change Rafi'ah fisabililliah?" Sai lokacin hawayen idanta ya sakko, wallahi har zuciyarta ba wai ta fadawa Abba dan yayi fada bane. Bayan hannunta tasa ta share hawayen idanta sannan ta dago ta kalleta ta ce "I'm