Sashe 25
Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 4 min read
wani waje, end of d month zanci gaba da kar6an salary" beedsheet ta rufawa Ikram ta ce "Allah ya taimaka, Allah kuma yasa da gaske kake, danni yanzu lamuranka tsoro suke bani" murmushi ya danyi ya fita a parlorn ta bishi da harara. Fitowa yayi a dakinsa cikin manyan kaya, sai kamshi yake ya dauka lab coat dinsa dake kan kujera ya daura akan kayansa, kaan dinning ya zauna yaga babu komai cikin warmers din, hakan yasa ya mike ya shiga daki ya dauko wasu files sannan ya nufi kofar fita hannunsa rike da key din mota, da sauri Jiddah tabi bayansa tana murmushi ta ce "Good morning Ya Yusuf" juyowa yayi yana kallanta ya ce "Morning Jiddah" idanta ne ya ciko tapp da hawaye, tayi kasa da murya ta ce "Dan Allah Yaya mena maka kace ka fasa aurena, ka fadamin koma menene Allah zan daina, i promise u Yaya" ta karashe magana tana goge hawayen idanta, duk jikinsa sai yayi sanyi, shima Allah na gani yana saan Jiddah but tinda Umma taki yarda tun farko ya janye jikinsa, hannunta ya kamo ya bata side hug ya ce "Keep quite" tayi shiru tana kwantar da kanta akan fadarshi taji ya ce "I luv u Jiddah, but i don't like some of ur attitude sometimes" dago kanta tayi tana kallansa ta ce "Na daina Yaya trust me" ya danyi murmushi ya ce "Then zaki aureni?" Ta daga masa kai ya ce "Kinyi alkawari bazaki kara yin abinda na hanaki ba?" Ta kara daga masa kai, ya sake murmushi yana kallanta ya ce "Kenan kinyi alkwari zaki zauna da wacce zan hadaku, but u are my first wife, she will come after u" turo baki ta danyi sannan ta daga masa kai, yayi patting bayanta ya ce "Then stop crying" zame jikinta tayi ta koma cikin gida ya bita da kallo, daga haka ya juya ya wuce parking lot. Da yamma liss Mummy ta sauke Rafi'ah a gida, bayan sun shiga duk da sauri take sai data labartawa Ummi Rafi'ah nada saurayi, Ummi batai wani mamaki ba sabida taga yadda take making calls, sai dai bata ce komai ba, Mummy ta mike tana kallanta ta ce "Na tilasta mata dai ta bani numbersa, tinda gobe ubanta zaizo sai a kirashi yazo suyi magana" kai kawai Ummi ta daga mata, daga haka ta rakata har paking lot kafin ta dawo ciki. Har dare Ummi bata cewa Rafi'ah komai ba, ita kuwa tinaninta kawai aiki ne ya mata yawa saboda taga tana ta marking, bayan sallan isha ta sakko downstairs daga ita sai 'yar rigar baccinta iya gwiwa, kanta ba dankwali hannunta rike da phone dinta, tana zama ta kalli Ummi ta ce "Gobe Abba da wuri zai iso ko sai caan yamma?" ba tare da Ummi ta kalleta ba ta ce "Sai ki kirashi ki tambayeshi" ta dan turo baki ta ce "Amma Ummi ai zai gaya miki" tana rife bakinta phone dinta ya hau ringing ta kalli screen din tayi murmushi ganin Yusuf ne, daga haka ta mike ta wuce upstairs Ummi ta bita da harara. Cikin cool voice dinsa yayi mata sallma ta amsa, ya danyi murmushi ya ce "I am happy Babyluv, and it's all because of u" zama tayi gefen gado ta ce "What hapoend Dr" ya limshe idanuwansa kamar tana kllansa ya ce "Mummy just called me, tace Abba zai dawo gobe around 12 na rana" Rafi'ah ta dan zaro ido ta ce "Then what?" Yusuf ya ce "I will come and see him insha Allah, tace min ta mishi magana" kamar zatai kuka ta ce "Pls ka bari ba yanzu ba Dr" Yusuf yayi murmushi yayi hanging call din, dama kawai he just call to let her know, tashi tsaye tayi ta fara zagaye dakin, duk tabi ta rikice, wayarta ta dauka tayi dailing number Mummy taji not reachable, ta kara kiran na Yusuf still d same thing, kwanciya tayi akan carpet ta rasa ta ina zata fara tsayar da Yusuf, Allah na gani batasan hukuncin da Abba da zai dauka ba, jin an bude kofa tayi surin rife idanuwanta kamar me bacci, Ummi ta shigo ta dauko wasu takardu kan stool sannan ta fice a dakin, Rafi'ah ta sauke jiyar zuciya ta mike zaune ta buga uban tagumi.