Sashe 57
Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
A hankali Jiddah ta tura kofar dakin ta rufe, ta kama kugu tana murmushi ta ce "Dama duk macen da tasan inda yake mata ciwo bai dace ta shigo gidan wata ba, gashi kin shigo banda azaba babu abinda kike sha" kwashewa da dariya tayi tana tafa hannu, Rafi'ah ta kauda kanta tana share hawayen idanta, Jiddah sake cewa "Gara ki tattara naki ya naki kibar mana gidanmu kafin abu yayi tsanani, dan yanzun nan ya gama gayamin ya tsaneki fiye da kowa a duniya" tana fadin haka ta juya ta fice a dakin. Tsabar bakin ciki kasa kuka tayi ta kifa kanta akan gado numfashinta yana neman sarkewa, a hankali ta jawo wardrobe din dake gefenta ta dauko drugs dinta, bayan ta balla ta mike ta dauki guntun pure water ta hadiye maganin, komawa kan gadon tayi ta kwanta tana addu'a ko zata samu saukin abinda take ji. Washegari da tinda ta tashi ta gama abinda za tai ta shirya tana jiran Yusuf saboda clinic da zata je, shiru yana dakin Jiddah ko lekowa baiyi ba, Rafi'ah na zaune a parlor Jiddah ta fito da plate din abincin a hannunta, sai rakwarkwasa take tana murmushi, bayan ta ajiye plate din ta koma part dinta tana dariya, shiru har bayan azahar Yusuf bai fito ba, Rafi'ah dake kwance ta jawo phone dinta tayi dialing number Ameera, yana shiga ta dauka ta ce "Amarya, how are u?" Cikin sanyin murya Rafi'ah ta ce "Fine, where are u now?" Ameera ta ce "I'm at home, do u need something?" Limshe ido Rafi'ah tayi ta ce "I want to see u Khadijah" Ameera ta ce "To bari nazo yanzu" hanging wayar Rafi'ah tayi ta share hawayen idanta ta koma ta kwanta. Bayan minti 15 taji ana knocking, ta mike ta fita a dakin, tana bude kofar Ameera ta rungumeta ta ce "I missed u friend, how are u?" Murmushi kawai Rafi'ah tayi ta kama hannunta ta ce "You're welcome" daga haka suka shiga part dinta, har dakin Rafi'ah ta shiga da ita suka zauna, Ameera dake kallanta ta ce "Kinyi rama and kin kara fari, is anything wrong?" Tare hawayen idanta takesan yin amma hakan bai yuwu ba, ta rungume Ameera ta fashe da kuka ta ce "I'm tired Ameera, na gaji da zaman auren nan kuma" zaro ido Ameera tayi tana kallanta ta ce "What are u saying Rafi'ah? Indai matsalar Jiddah ce ba sai kin shiga harkarta ba" Rafi'ah ta hau girgiza kai cikin kuka ta ce "No it's Doctor, Ameera bansan da wani ido zan kalli Ummina na fada mata na gaji da auren Yusuf ba" kara fashewa tayi da kuka ta sulale kasa ta zauna akan carpet, Ameera ta sauko itama tana kallanta ta ce "Pls explain further, ban gane abinda kike fada ba". Share hawayen idanta tayi ta ce "Ameera Doctor ya tsaneni, tin satina biyu a gidan nan nake ganin ba dai dai ba, baya min magana, baya cin abincina, baya min komai da kika sani, ko dakina baya shigowa yanzu" daga haka ta fashe da kuka ta turo baki ta ce "Wannan ma shiya dama ai, ni babban damuwana daina min magana da yayi, i'm in pain Ameera, my heart is always beaten, it hurts me morethan u know Ameera" ganin yadda take kuka yasa idan Ameera ma ya ciko da hawaye, gaba daya ta shiga damuwa itama, ko a mafarki bata tinanin Yusuf zaiyi abinda Rafi'ah ta fada ba, amma gashi a zahiri tin aure na wata daya matsaloli iri iri, lallai yau ta yarda maza abin tsoro ne. Share hawayen daya gangaro mata tayi ta dago Rafi'ah dake kuka kamar ranta zai fita ta ce "Have u tell anyone?" Rafi'ah ta girgiza kai ta ce "Noo, dan Allah karki fadawa kowa banasan hankalinsu ya tashi, and beside that inasan mijina, no matter how zan zauna dashi har karshen rayuwata" Ameera ta shiga share mata hawayenta ta ce "No Fatima, u have to tell someone ko zaki samu mafita, u can't be hurting yourself this much, bayan haka ma bakya tinanin ciwanki ya tashi" Rafi'ah ta rungumeta ta ce "Dan Allah promise me u won't tell anyone, Khadija kar ki bari wani yaji zancen nan, pls keep my secret only u Ameera" fashewa ta karayi da kuka jikinta na rawa, Ameera dake kuka itama ta ce "Ohk i promise u that i will keep this secret alone, amma meya kamata muyi yanzu?" Rafi'ah ta saketa ta fara goge hawayen idanta ta ce "U help me praying Ameera, nasan dai tinda nake ban ta6a cutar wani ba, so Allah ba zai bari a cuceni ba nima" Ameera ta ce "Insha Allah zan taya ki da addu'a, kuma zaki cinye wannan jarabawar da yardar Allah" Rafi'ah ta share mata idanta ta ce "Nagode Ameera, dama inasan in baki hand card dina na asibiti, sai ki kar6omin drugs dina, zan kira Doctor Hisham na gaya masa" Ameera ta ce "Ohk ba komai zan kar6o maki yanzu" tashi Rafi'ah tayi ta dauko hand card dinta cikin jaka ta mikawa Ameera ta ce "Zakiga office dinsa da sunansa a jiki, zan kirashi sai na masa bayani" ta ce "To shikkenan, kinci abinci ne?" Girgiza kai Rafi'ah tayi ta ce "Zan dafa anjima naci" Ameera ta yafa veil dinta ta ce "Ohk saina dawo" daga haka ta fita a dakin, kwanciya Rafi'ah tayi ta kira Dr. Hisham, bayan sun gama wayar taja blanket ta rufu har kanta, dan wani sanyi take ji yana ratsata har cikin jikinta. Tana nan kwance har Ameera ta dawo, Rafi'ah na jin an bude kofar ta mike zaune, Ameera ta karasa kusanta ta ce "Are u ok?" Ta daga mata kai kawai, Ameera ta ajiye mata ledan drugs din ta ce "Yace kinsan yadda kike sha ko?" Ta daga mata kai ta ce "Yes i know" daga haka Ameera ta mika mata wani leda mai takeaway a ciki ta ce "Ga abinci na siyo miki, u don't have to cook" murmushi Rafi'ah tayi ta ce "Thank u so much" Ameera ta mike ta ce "I'm going Fatima, Abbana ya kirani da ina hanya, idan kina bukatar wani abu u call me, ko Sajeed zan bawa ya kawo maki" Rafi'ah ta kamo hannunta ta ce "Thank u so much Khadijah, i don't know how much to thank u friend, nagode sosai" Ameera ta ce "Mention not, sai anjima" daga haka ta fita a dakin, tana fita Rafi'ah ta share hawayen idanta sannan ta koma ta kwanta. Ba ita ta shi ba sai kusan la'asar, ta shiga toilet tayi wanka tayi alwala sannan ta fito, gaban mirror ta zauna ta shafe jikinta ta tashi tasa kaya, tayi kyau sosai sai dai kana kallanta kaga rama sosai da damuwa a tattare da ita, takeaway din da Ameera ta siyo mata ta bude, tana kallan abincin ta fara yatsina fuska, spoon ta dauka ta debi fried rice din ta kai bakinta, da sauri ta zubar jin yadda zuciyarta ke tashi, ta rufe takeaway din ta ajiye a gefe sannan ta mike ta shiga toilet ta wanke bakinta ta dawo ta kwanta. Da dare kasa kwanciya tayi saboda yunwa dake daminta, ta fito a blanket ta dauka himar dinta ta saka ta fita a dakin, ba kowa a main parlor sai dai tana juyo muryarsu a parlorn Jiddah, ta dan turo baki ta shiga kitchen, tsayawa tayi tana bin kitchen din da kallo ko zata ga abinda ranta yake so, flour ta duba taga babu, ta tsuguna tayi tagumi, babu abinda take kwadayi taci sai dan wake, mikewa tayi ta bude fridge ta dauki fanta da glass cup ta koma part dinta, ta kai minti 6 tana kallan Fantan kafin ta zuba a cup ta dauka ta kai bakinta, tin kafin ta hadiye ta fara kakarin amai, tayi saurin zubar dana bakinta sai sauke numfashi take tana kallan sauran fantan dake cikin cup din, mikewa tayi ta shiga toilet ta wanke bakinta sannan ta fito ta dauki bottle din fantan ta jefar ta window, sauran na cup dinma ta zubar dashi sannan ta ajiye cup din akan drawer ta neki waje ta zauna. Haka Rafi'ah take ta faman shan wahala ita kadai har tsawon sati uku, wani lokaci ta samu abinda takeso wani lokaci idan babu ta hakura tayi kuka ta share ko kuma ta kira Ameera, kullum sukai waya da Ummi ko Mummy bata ta6a fada musu abinda ke faruwa, laulayi take sosai amma ko kadan bata kawowa kanta ciki ne da ita ba, ga mungun zazza6i da take kwana dashi duk dare, duk ta kara ramewa tayi mungun haske, ita kanta batajin nauyin jikinta saboda ramar da tayi. Ranar Monday da Yamma tana zaune a bakin gado ta buga uban tagumi, damuwarta bai wuce kiran da Mummy ta mata ba na cewa zata zo, duk sanda ta tuna sai kirjinta ya buga, tana nan zaune wayarta ya fara ringing, ganin Mummy ce yasa ta danyi jiim kafin ta dauka, Mummy ta ce "Kina jina Fatima?" Ta ce "Ehh Mummy" ta ce "Kiyi hakuri na fasa zuwan, kinga Ikram ne ba lafiya yanzu haka muna hanyar asibiti" wani 6oyayyen ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce "Ohk ba komai Allah ya bata lafiya" Mummy ta ce "Ba damuwa ki gaishe da Yusuf din" daga haka tayi hanging call din, tana nan zaune aka danna bell, ta mike a hankali ta zura hijabi har kasa sannan ta fita ta bude kofar, Khairiyya ta rungumeta ta ce "Anty" Rafi'ah na murmushi ta ce "You and who?" Ta ce "Driver ya kawoni" Rafi'ah ta tura kofar ta kama hannunta suka shiga ciki, a parlor suka zauna Khairiyya ta ce "Ina yini Anty" Rafi'ah ta ce "Fine, how is Ammi?" Ta ce "She's fine, tace na gaisheki wai yaushe zaki sake zuwa" Murmushi kawai tayi bata ce komai ba, ita gidansu ma sau biyu kawai taje, Khairiyya ta ce "Anty jiya na gama exams dina, jss3 zan shiga next term" Rafi'ah ta gyara mata himar dinta ta ce "Good, Allah ya sanya alkhairi, kiyi karatu sosai" Khairiyya ta ce "Sure, i want to be a medical doctor just like Yah Yusuf" Rafi'ah ta ce "Allah yasa to" mikewa tayi ta ce "Let me get