Sashe 24
Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
______________Jawad ne zaune a parlorn Abi Mami na zaune a kan kujerar dake opposite dinsa, tinda ya shigo parlorn kansa na kasa bai yarda sun hada ido da Mami ba ya zauna akan carpet, bayan Abi ya gama answering call din da yake ya dago kansa yana kallan Jawad ya ce "Why will u not follow them Ahmad? Or do u have something to do?" Ba tare daya dago kansa ba ya ce "Sure, i have alot to do Abi" Mami dake dalla masa harara ta ce "Munafikin Allah, babu wani abinda zakai a garin nan, saboda haka keep this at back your mind, wallahi saika tafi Abuja, i swear to God and i won't regret telling you such" ta karashe maganar tana jijjiga kafarta fuskarta babu walwala, ta dinga hararan Jawad da baisan tanayi bama, Abi yayi gyaran murya yana kallanta ya ce "Iook Hadiza, i see nothing to bother in this case, is Jawad still a kid? ko Ikram bazata zauna nan ba in taga batasan tafiya ballantana Jawad? Pls u keep this issue aside, tinda yace bazai je ba let him stay" Abi na rife bakinsa ya jawo newspaper dake gefensa yaci gaba da karatunsa, kasa daina kallan Jawad Mami tayi, shima kuma yaki yarda su hada ido, caan taja tsaki ta mike ta wuce part dinta tayi banging kofar da karfi, kallan direction din Abi yayi sannan ya girgiza kai yaci gaba da abinda yake, gently Jawad ya mike yana kallan Abi d hankalinsa ke kan newspaper, kallan part din Mummy yayi, caan ya wuce dakinsa ya rufo kofa. Zaro ido Rafi'ah tayi tana kallan Mummy ta ce "Dan Allah Mummy karki gayama Ummina, nifa ba saurayina bane" Mummy dake murmushi ta ce "I can't promise u bazan gaya mata ba, haka zamu zuba maki ido kiyi ta tsayuwa a titi da saurayi sai kace daga wancen garin muke, ai yafi kuyi hirar a gidan auranku, kince sunansa Yusuf ko?" Turo baki Rafi'ah tayi bata ce komai ba, ga kirjinta dake bugawa sosai, babban tsoronta idan Ummi taji wannan zance, ajiyar zuciya ta sauke tana kallan Mummy dake shirya kayanta cikin wardrobe ta ce "Dan girman Allah Mummy don't let her know, Allah it won't be good for me, zata iya dukana" Mummy ta ta6e baki tana kallanta ta ce "Sai kuma kiyi, baki isa kula samarin bane ko me da zakice zata dakeki, ni shekarata goma sha uku sanda nayi aure, duk karatun danayi a gidan mijina nayi" hawayen daya gangaro a idanta ta goge ta kara turo baki ta ce "To ai ku lokacinku haka ake, ni kuma Abba yace saina gama degree zanyi aure" ba tare da Mummy ta kalleta ba ta ce "U better wipe those tears, dan babu abinda zai hanani bashi dama ya turo magabatansa, dama faduwa ne yazo daidai da zama, kina karasa karatunki kiyi aure, idan yaso daga nan kiga karshen boko, shi kuma ubanki idan bazai aurar dake ba, inada kudin da zan iya miki komai ni kadai na, atooh in baka dashi ne saika jira an maka" Tashi Rafi'ah tayi ta fito parlor ta kwanta kan kujera tana goge hawayen idanta, imagining kawai take idan iyayenta suka saan wannan labarin, what will she even tell Abba bayan kullum burinsa tayi karatu me zurfi, taja dan karamin tsaki tana regretting zuwan Yusuf gidan Mummy. Umma ce zaune a parlor jidda tayi pillow da cinyarta, kana kallanta kasan taci uban kuka ba kadan ba, idanta duk sun canza kala sunyi jazir, Umma ta dan shafa kanta ta ce "Nace kiyi shiru ko Jiddah?" Cike da karfin hali ta ce "Nayi Umma" daga haka tasa hannayenta ta sharce hawayen daya sakko a idanta, Umma tayi patting bayanta cikin rarrashi ta ce "Ai Jiddah idan baki auri Yusuf ba sai dai idan ba raina, ki kwantar da hankalinki duk kukan nan da kike ki daina, kuma karki nuna masa komai, aure kuma kamar anyi an gama" tashi Jiddah tayi tana kallan Umma cikin muryar kuka ta ce "Allah Umma inasan Ya Yusuf, mutuwa zanyi idan ban aure shi ba" daga haka ta rungume Umma ta fashe da kuka, Ta6e baki Anty Khadija tayi ta tashi ta haura sama, ita haushin Jiddah ma takeji har ranta musamman idan ta tuna akan Yusuf take wannan kukan. Har dare yayi Rafi'ah bata samu tayi convincing Mummy ba, hakan yasa bugun zuciyarta ya karu, ta jawo ledan drugs dinta tasha sannan ta dake kirjinta ta limshe ido, har kusan karfe 10 tana a haka, jin an bude kofar dakin yasa ta bude idanta, Mummy ta zauna gefenta ta ce "Are u sick?" Ta girgiza mata kai kawai, Mummy ta ce "Tona menene dafe kirji? ko ciwo yake?" A hankali ta kara girgiza mata kai, Mummy ta ce "Then u stand up and take ur dinner" tashi tayi ta zauna tana yamutse ta ce "Tea kawai zan sha" Mummy ta ce "To kije ki hada a kitchen" daga haka ta fita a dakin ta koma dakinta. Sai bayan few minutes Rafi'ah ta janye duvet din dake jikinta ta sakko akan gadon, dogon hijabi ta saka saboda kayan baccin jikinta, daga haka ta fito a dakin, ba kowa a parlorn Mummy hakan yasa ta kashe faan da sockets sannan ta fita main parlor, Sadeeq ne kawai zaune a parlor yana kallo, ta danyi kasa da murya ta ce "Ina yini" a takaice ya ce "Lafiya" daga haka ta wuce kitchen, tana shiga taji kamar ta juya ta fito ganin Ikram da Jawad a kitchen din, kowa kuma harkar gabansa yake, shiga tayi ciki a hankali ta durkusa dai dai inda taga cups ta dauka guda daya da tea spoon sannan ta karasa inda taga flask ta bude zata bebi ruwan zafi, Ikram na gama juye indomie a cikin plate ta dauka tana ta6e baki ta fita a kitchen din. Sugar da milo tasa a cikin tea din, ta dinga bin kitchen din da kallo ko zata ga milk, dai dai inda Jawad ke tsaye ta hango tin din, ta karasa a hankali tasa hannunta zata dauko tin din suka hada ido, sauke kanta tayi kasa ta ce "Zan dauka madara ne" bai sake kallanta ba yaci gaba da abinda yake, ta dauki tin din ta bar wajen, bayan ta zuba ta dauka cup dinta zata fita taji ya ce "Who was that guy?" Juyowa tayi tana kallansa, yana tsaye inda yake kuma bai juyo ya kalleta ba, ta juya a hankali zata fita ya ce "Baki ji bane?" Silently ta ce "A friend" daga haka ta fice a kitchen din, har lokacin Sadeeq na zaune a parlor, Rafi'ah ta ce "Sai da safe" ya ce "Allah ya kaimu" daga haka ta shige part din Mummy. Washegari da safe Mummy ta shiga kitchen saboda girkinta ne ranar, Rafi'ah najin ta fita ta saka hijabi ta bita suka fara aikin tare da mai aiki, Mummy batai wani aiki ba tana dai zaune tana ce musu suyi wancen suyi wancen, bayan sun kusan gamawa Rafi'ah ta kalli Mummy ta ce "Nifa anjima zn wuce gida Mummy, i have school tomorrow" Mummy ta ce "Ki bari da yamma saina saukeki idan zan fita" girgiza kai tayi ta ce "No, inasan inje islamiyya ne da yamma, kinga jiya banje ba" Mummy dake kallanta ta ce "Ko kuma saurayinkin ne zaizo?" Turo baki Rafi'ah tayi ta ce "Nifa bance ba islamiyya nace miki zanje" Mummy ta ce "Sau nawa kina fashin islamiyyar for no reason, zaki wani fake zakije islamiyya" Ita dai bata ce komai ba banda hade rai da tayi, Hindatu me aiki nata dariya kasa kasa. Bude kofar kitchen din akayi Mami ta shigo, fuskarnan a daure ko walwala babu, sai data dauki abinda zata dauka tazo fita ta ce "Mun kwana lafiya?" Mummy ta ce "Alhamdulilah", abinda yake hadasu kenan a gidan, shima gaisuwan Abi ne yasa Mami tana gaishe da Mummy each and every day, wani lokaci ko Mummy tai mata magana sai taga dama take amsawa, hakan yasa itama tayi watsi da ita dan ita bata iya daukar rainin hankali. Bayan sun kammala komai aka jera akan dinning din Abi, Mummy tasa Rafi'ah ta dibar musu nasu a warmer, plate da cups Mummy ta dauko zata wuce part dinta, Jawad da fitowansa kenan yayi kasa da kansa ya ce "Ina Kwana" ta ce "lafiya Jawad, ya gajiya" ya ce "Alhamdulilah" daga haka ta wuce ciki, Mami sai hararansa take, bayan ta gama dibarwa Ikram abinci ta wuce part dinta ta rufo kofa, Jawad ya dawo kan dinning din ya zauna yayi sarving kansa ya hada tea, sai daya gama sannan ya mike ya nufi part din Maminsa, da sallama ya shiga parlor, Mami ta hade rai ganinsa taci gaba da bawa Ikram tea a baki, zama Jawad yayi yana kallansu ya ce "Take it yourself" ya karashe magana yana kallan Ikram, hannu tasa zata kar6i cup din a hannun Mami, Mami ta ce "Ina ruwanka to? Kai ka sani na bata?" Girgiza kai yayi yana kallanta ta ce "Then u mind ur words, babu ruwanka da abinda nayi niyya a cikin gidan nan" kansa ya kara saukewa kasa ya ce "Amma Mami yanzu Ilkram bazata sha tea da hannunta ba saikin bata, just because ta tashi da zazza6i, ita raguwar inane? shekara 17 fa" Hararansa kawai Mami take harya gama magana, ta ce "To saika hanani abinda nayi niyya tinda kaika haifeni, ko kishin uwarka bakayi ka bude baki ka gaishe da waccen matar, kana gani 'yar kanwata na ganina ina zirya ko sannu bata ce min ba, amma saboda kai kafi kowa ladabi ka gaishe da uwarta" shiru yayi baice komai ba, bayan few seconds ya ce "Kiyi hkr, amma dai kun fasa tafiya yau din?" Ta ce "Inafa tafiya Ikram ta tashi ba lafiya" a hankali ya ce "Allah ya sauwake" Mami ta ce "Yanzu ina zakaje?" silently ya ce "Court" ta ce "Saboda neman suna ko me?" Ya mike yana kallanta ya ce "May b i will just continue my work there, tinda sun bukaci hakan" ta6e baki tayi ta ce "A banza zaka musu aikin kenan?" Ya shafa kansa ya ce "No, ai dama sunce inna dawo zan iya ci gaba kona nema