Sashe 28
Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 6 min read
danne dannen waya, Mustapha ya ce "Dan Allah 'yammata kicewa Alhaji ana sallama dashi a waje, idan ya tambaya kice saurayi ne, me farar mota" Ikleemah ta mike ta bude kofar falon, bayan ta shiga ta tsaya bayan kujera ta ce "Abba wai ana sallama da kai" ya juyo yana kallanta ya ce "Waye?" Ikleemah ta ce "Mustapha dai yace saurayine me farar mota" Abba ya mike yana duba phone dinsa ya ce "And he didn't call me, je kice ya shigo a kaishi parlon BQ" Ikleemah ta juya ta fita bayan ta amsa da "To". Kallansa Anty Amina tayi ta ce "Ko wanda kuka dauka aiki ne? Wanda ka bani labari" Abba ya ce "No, wannan wanda yake neman Rafi'ah ne" Wani katon abu ta hadiye hade da zaro ido bata dai ce komai ba, Abba ya fita a parlorn bayan yasa takalmansa. Har bakin gate Ikleemah taje tace wa mustapha Abba yace a kaishi BQ, Mustapha ya bude kofar yana kallan Yusuf dake jingine jikin mota ya ce "Oga yace ka shigo" Yusuf ya shigo yana kallan Mustapha ya ce "Nagode fa" Mustapha nata washe baki ya ce "Bismillah" daga haka Yusuf ya fara binsa a baya, juyowa Ikleemah tayi suka hada ido da Yusuf, sai da kirjinta ya buga ganin yadda yayi kyau, ta dan saki murmushi ta juya, sai kuma ta fara tafiya slowly har suka iso dai dai da ita, ta sake kallansa cikin iyayi ta ce "Ina yini" ya ce "Lafiya kalau" daga haka ta shige apartment din Anty Amina, har bakin kofar parlorn Mustapha ya rakashi ya ce "Nan ne, zaka iya shiga" Yusuf ya gyada masa kai sannan ya murda handle din a hankali hade da sallama, Abba ya amsa shi cike da fara'ah ya ce "Bismillah", kan carpet ya zauna kansa a kasa ya ce "Ina yini Abba" Abba ya ce "Lafiya kalau, ya aiki" Yusuf ya ce "Alhamdulilah ka iso lafiya?" Abba ya ce "Lafiya kalau", shiru ne ya biyo baya, Abba ya kira layin Ummi bayan ta dauka ya ce "A kawo abinsha BQ" daga haka yayi hanging wayar, Abba na murmushi ya sake kallan Yusuf ya ce "Your name" Yusuf ya kara kasa da kansa ya ce "Sunana Yusuf", Ikleemah na shiga parlornsu dama ta samu Anty Amina jikin window tana leken wanda zai wuce, Ikleemah ta zauna gefenta ta ce "Naga halittar ubangiji Anty, kinga kyansa kuwa?" Anty Amina ta ce "Ni dama nasan wannan santa yake" Ikleemah ta ce "Kinsan shi Anty? Wallahi na kamu da san shi" Anty Amina ta ce "Saurayin Rafi'ah ne, taab ai wallahi ba zatai auren jin dadi ba, sai tayi auran wahala tazo tana rokona na sammata abincin da zasu ci" Ikleemah dake kallanta ta ce "Anty wallahi kyakkyawa ne" Anty Amina ta ce "Yanzu tashi na hada miki fruits ki kai masa" cike da murna Ikleemah ta ce "Yauwa Anty, zan kare masa kallo" daga haka tabi ta zuwa kitchen. Gajiya Ummi tayi da jiran Rafi'ah ta tashi ta haura sama, tana nan ta dukunkune a karshen gado tana rera kuka, Ummi ta dalla mata harara ta ce "Idan bazaki kai ba sai ki tashi kije ki fadawa Abban cewar baza ki iya ba" cikin kuka ta ce "Allah Ummi ni bazan iya ba, ni dai ki bawa wani ya kai" Ummi ta ce "Ni kikeso naje na kai kenan? Ai iyayin dayasa kika bari Anty Halima tasan shi, shi zaisa ki dauki hijab dinki ki kai masa ruwan sha" daga haka Ummi ta fice a dakin, Tashi Rafi'ah tayi ta leka ta window dinta ta hango motar Yusuf, hakan yasa ta kara fashewa da kuka ta zube a wajen, Ummi ne ta bude dakin ta dawo rike da wayarta yana ringing ta mikawa Rafi'ah ta ce "Sai ki fada masa bazaki kai ba" daga haka ta ajiye mata a kan gado ta fita. Tashi tayi a hankali ta shiga toilet ta wanke fuskarta sannan t fito ta bude press dinta ta dauko gogggen himar dinta har kasa tasa akan gown din jikinta, Sai sauke ajiyar zuciya take ta sauko downstairs, Ummi ta nuna mata babban tray akan dinning ta ce "Gashi caan ki dauka" Rafi'ah ta dinga kallan kan tray din ganin drinks har kala 4 sai kankana a yayyanke cikin dan bowl da pineapple sai Apple a gefe, turo baki tayi ta dauka ta fita a parlorn Ummi ta bita da kallo harta fita. Murmushi Abba yayi bayan ya gama sauraron meaningful words din Yusuf ya ce "Amma iyayanka 'yan nan garin ne?" Yusuf ya ce "Ehh, sunan mahaifina Muhammad saraki, amma Allah ya musu rasuwa shida mahaifiyata shekara 7 kenan, akwai dai kanwar Mamana a unguwar Rimi, yanzu dai ina zaune ne wajen kanwar mahaifina da suke uba daya" Abba ya girgiza kai looking so sad ya ce "Allah ya musu rahama" Yusuf ya ce "Ameen". Rafi'ah na zuwa dai dai apartment din Anty Amina Ikleemah ta fito rike da tray itama, fruits salad ne a gefe sai fanta da glass cup, Rafi'ah ta dalla mata harara ta wuce, itama harara ta dalla mata tabi bayanta, ajiye tray din Rafi'ah tayi ta bude kofar parlorn, Ikleemah ta shige da sauri, harara Rafi'ah ta bita da shi, daga haka ta dauka tray dinta ta shiga da sallama, a gefen Yusuf ta samu Ikleemah ta zauna wai tana gaishe shi, ta dire tray din hannunta ta juya ta fice a parlorn Yusuf ya dan saci kallanta, bayan sun gama gaisawa da Ikleemah ta mike tana ta rangwada ta fita a parlorn itama. Abba ya ce "Bismillah son, ga abinsha da abinci" Yusuf yayi kasa da kansa yana murmushi, bayan few seconds Abba ya ce "Kace kana aiki a Aminu kano TH ko?" Yusuf ya ce "Ehh" Abba ya danyi shiru kafin ya ce "But kasan class din da take a school?" Ya dirgiza kai, nan kwa yasan a SS2 take , Abba ya ce "To tana SS2 yanzu, sannan koda zatai aure sai ta gama secondary school, na kuma maka alkhawarin in har na gama bincikena zan baka auran Rafi'ah but on one condition" sai lokacin Yusuf ya kalli Abba sannan ya maida kansa kasa, Abba ya ce "Zata ci gaba da karatunta a gidanka" Ajiyar zuciya Yusuf ya sauke ya ce "Insha Allah Abba, nayi alkawari" Abba ya ce "To masha Allah, Allah yayi albarka, bari na amsa waya" Yusuf ya ce "To Abba" daga haka Abba ya mike ya fita. Rafi'ah na komawa apartment dinsu ta wuce dakinta taci gaba da kukanta, abinda yake kona mata rai yadda Ikleemah keta washe baki tana kallan Yusuf, sannan shima yace mata bazai zo ba ya tashi ya zo, tana tina wadannn abu biyun saita fashe da kuka. Har Abba y gama making calls dinsa ya shigo Yusuf ko abu daya baici ba, Abba ya ce "Baka ci komai ba Son" ya dan girgiza kai ya ce "I'm full Abba, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi" Abba ya ce "Ameen, a huta gajiya" daga haka Yusuf ya fita a parlorn, very gentle ya dinga tafiya harya iso gate ya fita, ya shiga motarsa ya mata key ya bar layin, sai murmushi yake, kana kallansa kasan he's so happy. [7/29, 6:47 AM] Zarah: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_