← Book details Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 45 OF 59

Sashe 45

Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 9 min read

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_37_

A bakin gate yayi parking as usual, dashboard ya bude ya dauko chequebook da biro yayi rubutu sannan ya yage paper din yasa a pocket dinsa, wani dan karamin box ya dauko sannan ya dauki envelope din ya fito a motar ya rufe, gently ya karasa bakin gate din ya tura sannan ya shiga, few people ne a tsakar gidan kowa da abinda yake wasu na zaune akan mat, wasu kuma nata backyard ana girki, wasu manyan mata ne akan tabarma suna zaune sai hira suke, kana kallansu kaga dangin su Ummi ne sai kanwar mahaifiyarsu da ita kadai ta rage musu wacce suke kira da Gwaggo, ko ba'a fada ba kamanni sun nuna, tsugunawa Jawad yayi ya ce "Ina yinin ku" a tare duk suka amsa da fara'a ya mike ya shiga cikin gidan, Ummi ce zaune a parlor da wasu mata biyu, ya zauna akan carpet yana murmushi, Ummi ta ce "Is it you Jawad? Dama kana nan?" murmushi yake yana gyara hulan kansa ya ce "Ina nan Ummi, aiki ne ya min yawa yanzu" ta ce "To Allah ya taimaka" ya ce "Ameen, ya hidima?" Ta ce "Alhamdulilah, let me get something for you" daga haka ta mike, gaishe da sauran matan yayi suka amsa masa, ba jimawa Ummi ta fito a kitchen da warmers a hannunta ta wuce parlorn Abba, bayan ta fito ta ce "Ka shigo ciki Ahmad" tashi yayi a hankali ya wuce parlorn Abba ya zauna akan carpet ya fara danna wayarsa. Shigowa Ummi tayi ta zauna ta ce "Kaci abincin ko, bari Rafi'ah ta kawo maka kunu, ko baka sha?" kansa ya dan sauke kasa ya ce "Ina sha, amma dai na koshi da abincin" Ummi ta ce "To bari a kawo maka kunun" daga haka ta fita a parlor. Upstairs ta wuce ta shiga dakin Rafi'ah, a kwance ta sameta tana waya, tayi saurin hanging wayar tana kallan mahaifiyartata, Ummi ta ce "Kije ki dauki kunu ki kaiwa Jawad, yana parlorn Abbanki" a hankali ta mike ta dauki himar dinta ta saka sannan tabi bayan Ummi ta fito, tana saukowa ta wuce kitchen ta dauko flask din sannan ta shiga parlorn Abba, very gentle ta karasa gabansa ta ajiye flask din, suna hada ido tayi saurin dauke kanta ta nemi waje ta zauna gefenshi, a hankali ta ce "Ina yini" ya ce "How are u?" ta ce "I'm fine" ya ce "Ya shirye shirye?" Kanta na kasa ta ce "Alhamdulilah" daga haka ta mike ta fita a parlor ya bita da kallo. Mug ya dauka ya bude flask din sannan ya debi kunun ya saka cube din sugar guda 2 sannan ya dauka spoon ya juya ya fara sha a hankali. Few minutes ya gama sannan ya ajiye cup din, Ummi ne ta shigo parlor daukan abu, ya danyi kasa da kansa ya ce "Ummi zan tafi Cyprus gobe insha Allah" dagowa tayi tana kallansa ta ce "Tooh zaka kara nisa kenan, daga wajen aiki ne suka tura ka?" Ya ce "Ehh" ta ce "To Allah ya tsare hanya, ya dawo da kai lafiya, are u staying long?" Ya ce "Noo, just 2 months" ta ce "Aida yawa Jawad, Allah dai ya taimaka ya tsare" ya ce "Ameen", daukan abinda zata dauka tayi sannan ta fita a parlor, so yake yace mata yana san yaga Rafi'ah amma ya kasa, gashi he is eager to go home.
After 15 minutes Rafi'ah ta shigo parlor, sai data dan tsaya ganinsa dan a tinaninsa ya wuce, ta sunkuyar da kanta ta wuce dakin dake parlor, ba jimawa ta fito da wani dan bucket a hannunta, Jawad ya ce "Idan kin gama kizo" juyawa tayi ta kalleshi sannan ta fita ta kaiwa Gwaggo bucket din ta dawo, a hankali ta karasa inda yake ta zauna, ya mika mata envelope din ya ce "Mummy ta bayar a baki" ta kar6a sannan ta ce "Thanks" daga haka ya ciro box din da cheque ya mika mata ya ce "And this is for you" ta dago ta kalleshi sannan ta kar6a, kallan cheque din ta dinga yi, ta kara kallansa ganin 100k ajikin cheque din, sauke kanta tayi kasa ta bude box din a hankali, ta dan zaro ido ta ce "Azurfa?" Ya daga mata kai ya ce "I hope it will size you?" Murmushi tayi ta fara zira ring din a hannunta na dama, ta juyo hannun tana kallansa ta ce "Yayi kyau sosai, thank u so much" kallan dogayen fingers dinta kawai yake, ta cire ring din ta maida shi box dinsa sannan ta ce "I'm so much greatful, nagode sosai Allah ya saka da alkhairi" a hankali ya dago yana kallanta ya ce "I know u have more than that, so no need to say thanks, and i'm wishing u a happy marriage life, try your best and be the best wife ever" a hankali ta ce "Insha Allah" still looking at her ya ce "Gobe zan tafi Cyprus bazan samu daurin auran ki ba" duk jikinta sanyi yayi ta ce "Allah ya kiyaye, ya kaika lafiya" ya ce "Ameen" daga haka ya mike ya dauki key din motarsa, tashi tayi tabi bayansa har suka fito a gidan, ta rakashi har mota tana mishi Allah ya kiyaye, silently ta tsaya a bakin mota ta ce "I'm lost of words Ya Jawad, nagode sosai da sosai, Allah ya saka, i'm happy with the gift" murmushi ya danyi ya ce "Ba komai, thanks too" rife motar tayi sannan ta shiga gida shi kuma ya tada motar ya bar layin. Tana shiga compound Gwaggo ta ce "Shine angon ne Fatima?" Turo baki tayi tana kallan kakartata ta ce "Ba shine bane fa Gwaggo" Gwaggo ta ce "To shi wannan din waye? angon baizo ya gaishe niba fa, baisan kanwar kakarki tazo bane" dariya ta danyi ta ce "Keda zamu tafi tare, ai an maki dakinki" daga haka ta wuce ciki ta barta a tsaye.
Washegari da sassafe Jawad ya gama shirinsa na tafiya Abuja, daga caan karfe 10 na dare zasu tashi zuwa Cyprus Mami na tsaye ta gama hada masa komai ta ce "Yanzu sai kaje Abujan zaka karasa kenan?" Ya ce "Ehh" ta ce "To saura karkaje ka gaishe da mutanen gida, nasanka yanzu zaka ce aiki ya maka yawa" murmushi ya danyi ya ce "Ai a caan zan sauka tinda yau zan wuce" ta ce "To Allah ya kiyaye, ya kuma tsare hanya" ya ce "Ameen", Sadeeq ne ya fitar mishi da komai zuwa mota, bayan sun fito parlor Mummy ta fito da dambun namanta cikin dan karamin bucket ta ce "Allah ya tsare Ahmad, ga dambun naman" kar6a yayi ya ce "Nagode Mummy" ta ce "To Allah ya tsare" daga haka ta koma part dinta Mami ta bita da harara, shi dai sauke kansa yayi kasa ya fice a parlor, Mami tabi bayansa ta ce "Dambun naman ne bazan iya maka ba sai ka fadawa duniya an maka" dan murmushi yayi ya ce "It's nothing ai Mami, duk daya ne" harara ta 6alla masa ta ce "Allah ya tsare" daga haka ta koma cikin gida ba tare data ga tafiyarsa ba. Da Yamma liss aka fara shirin waleeman da Mummy ta hada, ita ce komai akan gaba, karfe 4 mai make~up tazo ta fara yiwa amarya, Ameera na gefe ta gama make~up dinta tana daura dankwali, bude kofar akayi Mummy ta shigo ta ce "Wai har yanzu baku gama ba?" mai kwalliyan ta danyi murmushi ta ce "An gama Hajiya" Mummy ta kalli Rafi'ah dake kyalli ta ce "Masha Allah" daga haka ta fita a dakin, by 4:30 sun gama komai da komai, a compound din cikin gidan aka jera kujeru akai decorating wajen, Babbar malama aka dauko ta wa'azantar da mutune akan rayuwar zaman aure, da yawa mutane sun karu ba kadan ba, bayan ta gama aka fara cin abinci sannan aka raba snacks, daga karshe akai hotuna kowa ya watse. Da dare musalin karfe 10 Rafi'ah na zaune a dakinta ita da Ameera da wasu friends dinsu na islamiyya su biyu, Mummy ta shigo ta ajiye musu warmer din abinci ta ce "Rafi'ah Gwaggo tace bata ganki ba tin bayan waleema" limshe idanuwanta tayi ta ce "Ina daki, bayan dazu data ganni da make~up tace min abu kamar aljana" dariya Ameera ta dinga yi tana kallan Rafi'ah, Mummy ta ce "Ai kadan da aikin Gwaggo, Yusuf din ya aiko kayan da zaki sa goben?" Rafi'ah ta ce "Yace zai kawo da safe" Mummy ta ce "Ok to shkn, zaizo ne ayi kamun dashi" Rafi'ah ta dan turo baki ta ce "Yace dai zaizo muyi pictures" Mummy ta ce "To ba damuwa na zata ai bazai zo ba ne danaji baki maganar ba" daga haka ta fita, Rafi'ah ta kalli Ameera ta ce "Ai sai yazo wajen kamun nan, ai da bikin matarsa shima yaje" Ameera ta dan yi murmushi ta ce "Kishi" duka Rafi'ah ta kai mata ta kauce tana dariya. Washegari ya kama friday, gidan biki ya cika da jama'a kowa nata hidima, Rafi'ah dai tattara nata nata tayi ta koma gidansu Ameera saboda mutane. Bangaren su Umma kuwa, mutane kadan ne a gidan, dan batayi wani gayya ba, gaba daya abin duniya ya isheta, sau biyu Jiddah na zuwa mata tana kuka, haka dai Umma ke lalla6ata ta koma gida. Gidan Ammin Khairiyya kuwa acaan duk 'yan uwa suka sauka, gidan ya cika da mutane kai kace a gidan Yusuf ya girma. Anty Amina ce zaune a dakinta tare da Anty Rahama, ta dan yatsune fuska tana kallan Anty Rahama ta ce "To ya zanyi Maman Ikleemah, kina gani dai abun nan yana nan ba'a tone ba" Anty Rahama ta ta6e baki ta ce "To sai asan abinyi a gaba ai, ba wai zuba ido zamuyi ba, su kuma 'yan uwanmu da basu iya zuwa birni ba duk sun cika gida, gidan Umman ma acike yake, kema naki acike, nifa idan na gaji kaaf mutanen parlorn nan saina koresu wallahi" Anty Amina ta gyara zamanta ta ce "Ga kazanta kamar ta fito fili, shima Yayah Muhammad din a hotel yace zai kwana yau" Anty Rahama ta gwalalo ido ta ce "Anya mun ta6a bikin da akai taro irin wannan kaf zuri'ar mu kuwa? Har Abban sunma ya rasa wajen kwana a gidansa sai hotel?" Anty Amina ta ce "To shine abinda yake damuna, gashi shi Mutumin Umma cewa yayi ko taro baza'ai ba gashi har gobe daurin aure" Anty Rahama ta ce "Mudai zuba ido, ba kince yana nan ba a binne?" Kai ta daga mat, Anty Rahama ta mike ta fita tana kallan mutanen parlorn da duk yawanci 'yan uwansu ne ta ce "Kuma wallahi duk matar data ci abinci ta share, haka kawai kun cikawa kanwata parlor da 'ya'ya 'yan kauye" wata 'yar uwarsu ce ta mike tana kallansu ta ce "Ke Rahama ki kiye bakinki, gidankine da zaki finga yiwa mutane iyayi kina fada musu magana" Anty Rahama ta ce "Amma ai gidan kanwatane kuma gidan Yayana" matar ta mike tana tafa hannu ta ce "Indan ta wannan ne muma ai dan uwanmu ne, saboda haka duk inda muka ga daman zama a gidan nan zama zamuyi" wata mata ce ta tashi tana kallanta ta ce "Dan Allah Safiya kiyi hakuri kibar kulata, ita har tanada bakin magana, shekararta nawa a gida babu aure, ga zandareriyar budurwar 'yarta banda rashin kunya bata iya komai ba" Cakumeta Anty Rahama tayi ta ce"Har ni zaki cewa bazawara, yanzu sai naci kaza-kazanki a gidan nan wallahi" mutanen dake zaune a parlor suna ta bada hakuri, da kyar dai Anty Rahama ta saketa ta shige daki tana zage-zage.
Chapter 45 · 0% Book details