← Book details Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 34 OF 59

Sashe 34

Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 7 min read

ta ce "I missed u Anty" Rafi'ah taja hancinta tana gyara mata scarf dinta ta ce "I missed u khairiyya, how are u?" Ta ce "I'm fine, Yaya yace i'm spending the day with u" sai lokacin ta kalli Yusuf dake kallanta ko kiftawa babu, ta sauke kanta kasa ta ce "Ina yini Dr" ya ce "Fine sweetheart, ya hutu?" Ta ce "Alhamdulilah" ya ce "SS3 zamu shiga ko?" Tayi saurin rife fuskarta tana murmushi ta ce "Ni ka daina tsokala na" ya ce "No i'm counting my days" zaro ido tayi ta ce "So soon?" Ya ce "Ehh mana, aiba yawa lokacin" ita dai murmushi kawai tayi, ya sake kallan fuskarta ya ce "Bayan awa biyu zan dawo na dauketa, and i want to talk to u idan na dawo" a hankali ta daga masa hannu ta ce "Ohk till u come back" ya ce "Thank u" daga haka yayi reverse ya bar unguwar, Khairiyya ta kalli Rafi'ah ta ce "Anty kawai sai ki boyeni mu kwana" Rafi'ah ta zaro ido ta ce "So kike yau Amminki tazo ta zaneni" Khairiyya tayi murmushi looking happily, Rafi'ah ta kama hannunta ta murda handle din suka shiga, kallansu kawai Ummi take har suka karasa shigowa, Khairiyya ta zauna a kan carpet tana kallan Ummi ta ce "Ina yini" Ummi ta ce "How are u?" Ta ce "I'm fine" kallan Rafi'ah tayi dake daukan abu akan dinning ta ce "Who is she?" Kanta na kasa ta ce "Cousin din Dr ce" Ummi ta ce "Ohk, tashi ki zauna kan kujera mana, what's your name?" A hankali ta ce "Fatima Zarah, amma Ammina da Daddynah used to call me Khairiyya" Ummi ta danyi murmushi ta ce "Good". Bayan Rafi'ah ta gama hada mata fruits salad ta mika mata ta ce "U take this Baby, and what will i cook for u" Khairiyya ta kar6a bowl din tana murmushi ta ce "Na koshi da abinci Anty, but i like this" daga haka ta dauka tea spoon dake gefen bowl din ta fara sha, Rafi'ah na zaune harta gama shanyewa, ta mike ta ajiye bowl din akan dinning, Rafi'ah dake kallanta ta ce "Ko in kara maki?" Ta girgiza kai, kama hannunta Rafi'ah tayi suka haura upstairs, bayan sun shiga dakinta Khairiyya ta limshe ido ta ce "Anty is this ur room, very neat and it's smelling nice" Rafi'ah dai murmushi kawai tayi, Khairiyya ta daga kanta tana kallan hotunan Rafi'ah dake jikin wall tin tana 'yar karama har izuwa yanzu, Rafi'ah ta ce "Khairiyya ko in kawo miki fried rice?" Zaro ido yarinyar tayi ta ce "Anty nifa bana cin abinci sosai da dai Yaya Sameer kika ce, shine Ammi tace ko a office ci kawai yake, shi kuma Yaya Faruk wai bayacin spaghetti" murmushi kawai Rafi'ah take tana kallanta, ta sake cewa "Allah Anty Yaya Sameer yana da ci, zai iya cinye abincin cikin gidan nan" Rafi'ah na dariya ta jawo laptop dinta ta ce "Which cartoon do u want to watch?" Cike da farinciki Khairiyya ta ce "Yess Anty, i love watching Angelina ballerina" Rafi'ah ta shiga YouTube tayi searching sannan ta saka mata, bayan ta fara kalla ta mike ta ce "I'm coming dear, just 5 minutes" daga haka ta fita a dakin. A awa biyun da Khairiyya tayi wajen Rafi'ah taga kulawa sosai, duk abinda tace tanaso Rafi'ah zata bata, har 500 ta bawa Mustapha ya siyo mata chocolate, bayan Yusuf ya kira yana waje Rafi'ah ta kashe kallan tana kallan Khairiyya ta ce "Yaya is outside Khairi" Khairiyya ta rungume Rafi'ah ta baya ta ce "I will miss u Anty" kama hannunta tayi suka fita ta kaita har dakin Ummi ta ce "Zata tafi Ummi" Ummi ta bata packet din sweet sai ribbom da bead, ta dan rusuna tana dariya ta ce "Nagode" Ummi ta shafa kanta ta ce "A gaishe da Mama" da toh ta amsa tana ta dagawa Ummi hannu, bayan sun fito a dakin Rafi'ah ta ce "Wait here" daki ta koma ta dauko mata ledan chocolate dinta sai dan karamin tirare cikin wani kwali, ta hada mata chocolate da sweet din waje daya sannan tasa mata tiraren cikin ledan bead din ta ce "The perfume is also for u" Khairiyya ta wara ido ta ciro shi tana shinshinawa ta ce "Anty irin kamshin dakinki da jikinki, i love it, thank u Anty" shafa kanta Rafi'ah tayi sannan ta kama hannunta suka sauko downstairs, bayan sun fita a parlorn suka nufi bakin gate, yana tsaye jikin motarsa as usual, Khairiyya ta shiga nuna masa abubuwan hannunta, ya kalli Rafi'ah da kanta ke kasa ya ce "Thanks for everything love" ta danyi murmushi ta ce "Mind not, i will miss her much" Yusuf ya dan shafa kansa ya ce "To muje ki rakani mu kaita gida" ta ce "No, kaje dai ka dawo" ya ce "Pls, aiba nisa ba kince kinsan area ba" a hankali ta ce "Toh" ya bude mata front seat yana murmushi ta shiga, daga haka ya zagayo seat dinsa yayi wa motar key suka wuce, 5 minutes ya kaisu gidan Ammi, Yusuf ya juya yana kallan Khairiyya ya ce "Kije ciki Khairiyya zan maida Anty gida" kamo hannun Rafi'ah tayi ta ce "Thank u Aunt, baza kuje nima kiga Ammina ba?" Ta ce "Noo, some other time Khairi, zanzo kiyi ta bani labari" daha haka ta sauka a motan tana daga musu hannu ta shiga gate, juyowa Yusuf yayi yana kallan Rafi'ah dake murmushi. Jifa jifa suke hira har suka kusa isowa gida, ya samu dai dai kasan wata bishiya yayi parking ya juyo yana kallanta, nan da nan kirjinta ya hau bugawa, ya sakar mata murmushi ya ce "What?" Ta ce "Naga kayi parking a nan, and the street is very quite" Kamo hannunta Yusuf yayi yana kallan idanta ya ce "I want to say something Fatima, but pls don't judge me wrong" dago kanta tayi tana kallanshi, ya ce "Sure nasan u are my happiness, u cause alot of changes in my life Fatima, i don't know how much i luv u, and insha Allah i will continue caring till my last breath" sauke kanta tayi kasa tayi shiru, ya kara kamo dayan hannunta silently ya ce "Kafin na hadu dake akwai wacce nake soyayya da ita, she's in my house, her name is Jiddah, and i promise to marry her too" kanta na jikin kujera tana jinsa amma ko dago kanta ta kalleshi bata yi ba, ya matsa kusa da ita ya ce "I hope zamu zauna tare dukkanmu?" Daga masa kai tayi, ya ce "Noo, u speak" a hankali ta ce "I'm hopping for d best, Allah yasa shine alkhairi" baisan lokacin daya rungumeta ba, tayi saurin janye jikinta tana turo baki, bai ta6a tinanin iya abinda zata ce ba kenan, ya kamo hannuta yayi kissing soft hand dinta ya ce "U are d best Rafi'ah, ke dabance a cikin mata, i luv u so much Fatima" murmushi ta danyi ta juya tana kallan waje ta cikin glasses din motar, ya tada motar yana kallanta ya ce "Bari mu wuce kar Ummi ta neme ki" daga haka yaja motar, har suka iso gida bata ce komai ba, sai da taga yayi parking ta ce "Nagode, Allah ya kiyaye hanya" ya kara kamo hannunta ya ce "Are u angry with me Fatima?" Ta girgiza kanta trying hard not to cry ta ce "Why will i Dr, Allah yasa haka shine alkhairi" daga haka ta zame hannunta ta fito a motar. Tabbas ita kadai tasan abinda taji a zuciyarta a sanda yake mata zancen Jiddah, but ya zatai, a yanzu babu wanda takeso fiye da Yusuf bayan iyayenta, haka Allah ya tsara mata me mata zata aura, so her own is to pray for d best, tana shigowa gate hawayen daya taru a idanta ya gangaro, Jawad dake tsaye a parking lot ya nufota yana kallanta ya ce "What's it? Why are u crying" matsawa tayi gefe zata wuce ya kamo hannunta suka koma gate, lekawa yayi ya hango motar Yusuf daya kusan kaiwa titi, ya juyo yana kallanta ya ce "Meya faru?" Ta girgiza masa kai, ya ce "Tell me, koya maki wani abu ne?" Ta girgiza kai tana saan kwace hannunta amma ta kasa, ya kara jaanta zuwa parking lot suka nufi backyard din gidan, yana rike da hannunta kawai yaji tayi gefe zata fadi, yayi saurin rikota zuwa jikinshi yana kallan numfashinta dake shirin sarkewa, ta dafe kirjinta hawaye naci gaba da sakko mata, yana jiyo yadda zuciyarta ke bugawa da sauri da sauri, ya kai hannunshi bayanta yana patting dinta to make sure she remain calm.
Chapter 34 · 0% Book details