← Book details Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 13 OF 59

Sashe 13

Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Cikin quick light steps ta shigo compound din nasu, ta dan kalli apartment din Anty Amina sannan ta ta6e cute mouth dinta ta nufi entrance din gidan, Ummi ce kadai zaune a parlo tana kallo, Rafi'ah ta saukar da kanta ganin irin kallan da Ummi ke mata, ji tayi ta ce "Where are u from?" Wani katan abu daya tsaya mata a wuya ta hadiye kafin ta ce "Shopright" Ummi ta dinga kallanta sannan ta ce "And why did u came back alone? didn't u know that they spent more than 20 minutes before u came in" a hankali ta ce "Naje daukan perfumes ne, so kafin na dawo na samu sun taho" Ummi ta ta6e baki ta ce "Is ok" daga Rafi'ah ta wuce upstairs da fargaban abinda zai faru idan har Abba yaji tacewa Antinsu mai aiki ce. Direct dakinta ta shiga ta kwanta akan bed tana sauke ajiyar zuciya, calmly ta danne side din da zuciyarta yake saboda heartburn data faraji, ta limshe idanuwanta to make sure it's not taking long, ji tayi kamar an kara mata wanda takeji akan da, ta fashe da matsanaicin kuka tana kwalawa Ummi kira, juyi ta farayi tana yarfe hannu, dayan hannunta kuma yana kan heart dinta dake mata zafi kamar zata fasa kirjin ta fito. Tin tana hawaye harta dawo she's crying loud calling Ummi and Abdul. Ummi na zaune a parlo taji kawai she's not comfortable with her daughter's absence, tasan the next abu da zatai to bacci ne, hakan yasa ta mike ta nufi upstairs, Immidiately tana gama hawa Rafi'ah ta saki wani irin kara hade da kiran Abba, Ummi ta bude dakin da saurin tayi kanta tana salati, dagota tayi jikinta tana kallan idanta dake limshe ta ce "Rafi'ah!" tana bude idanuwanta hawaye suka shiga gangaro mata, a hankali ta dago hannun Ummi ta dora akan chest dinta ta ce "It's hurting me Ummi" daga ta tayi kamar baby girl ta rungumeta suka fito a dakin, suna fitowa sai ga Abba da hawowansa kenan yana waya, cikin tashin hankali ya ajiye wayar akan sofa yana furta "Subhanallah" daga haka ya kar6eta in a hurry ya fara sakkowa steps da ita, komawa daki Ummi tayi ta dauko hijab dinta sannan ta sakko. Ko kafin ta fito har Abba yasa Rafi'ah a mota, bayan Ummi ta shiga yaja motar suka fita a gidan zua Clinic din da suke zuwa. Suna isa cikin gaggawa aka turo bed aka daurata akai sannan aka wuce da ita ciki. Dr. Saleem, Dr. Aryan da kuma wasu turawa biyu ne a kanta to make sure they give her quick assistance, Aspirin doctor Aryan ya saka mata a baki, as usual ta fara chewing a hankali harta hadiye sannan aka bata nitroglycerin ta sha, after then aka mata injection din papaverine to reduce the pain and discomfort beyond her chest to orther part of her upper body, few minutes da mata alluran ta samu tayi bacci, Dr. Aryan ya kalli sauran doctors din dake kanta ya ce "I think it's successful" wani bature a cikinsu ya ce "By God grace" daga haka suka fita gaba dayansu suka jawo kofar to let her rest. Suna fitowa Abba ya karasa wajensu ya ce "How is she Doctor?" Doctor Aryan ya cire hand gloves din hannunsa yana kallan Abba ya ce "It was successful, insha Allah within 1 hour zata tashi" Abba ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Thank u" daga haka ya koma inda Ummi ke zaune, daka ganta kasan tana cikin tashin hankali, Abba ya kamo hannunta yana massaging just to make her calm ya ce "Relax please, kiyi ta mata addu'a" ta goge dan hawayen dake makale a idanta ta ce "I don't want to loose Rafi'ah Yallaboi" ta karashe maganar cike da damuwa, Abba ya ce"The best thing is du'ah Ummu Rafi'ah, u know God plan the best, it is a test from God, kuma ina fatan zamuci wannan jarabawa insha Allah" a hankali Ummi ta ce "Allah yasa". Anty Amina ce zaune a parlorn ta tana shan fresh yoghurt sai yayarta dake zaune a gefenta tana sauraronta, bayan ta dasa aya matar ta zaro ido hade da kundumo ashar ta ce "Baki fasawa yarinya baki ba? Ita har tana da bakin da zata kiraki da 'yar aiki? Wallahi tallahi Amina kinyi asara, ko uwarsu ce ta fada miki haka bakya tsigale taba ballanta wannan taniniyar yarinyar" Anty Amina ta ajiye glass cup din hannunta ta ce "Nifa Anty Rahama wani abun mamaki na gani that's why i totally forgot her speech, nifa tsohon saurayin Nusaiba na gani ya mata magana" Anty Rahama ta ce "Wacece Nusaiba?" Gyara zama Anty Amina tayi ta ce "Kawata da muka gama karatu tare, wallahi tana sanshi yana santa ingaya maki wata 'yar uwarsa ta shiga tsakani suka rabu, ni kuma dama fa.. Tin kafin nayi aure kyau yakemin, fatana dai ba saurayinta bane, wallahi Anty Rahama bakiga kyansa ba, kamar shi yayi kans... " tsawa Anty Rahama ta daka ta ce "Lallai Amina na yarda kin fara hauka, ina ruwanki da wani saurayi caan da mijinki" ta 6ata rai ta ce "Anty Rahama hauka kuma?" Ta ce "Hauka mana Amina, da kinsan irin tuggun da muka hada nida Umma akan Ya Muhammad ya aureki da baki fadi haka ba, ina gashi muna 'yan wansa na jini amma akace ya nemeni yaki, haka na hakura nayi wannan tsinannen auren da babu komai a cikinsa sai wahala, me za'ai da talauci Allah na tuba" Anty Amina sai kallanta take bata ce komai ba, Hakan yasa Anty Rahama ta kamo hannunta ta ce "Ko kin manta da Ummanmu da mahaifinsa uba daya suke, to haka mukaita kai kawo kauyen Masko har Allah yasa da kansa yaje ya sami Gwaggo Allah ya jikan rai yace yana sanki da aure, ke wahalar da muka sha wallahi bazai misaltu ba, amma gaki shekara 3 har yanzu ko 6ari baki ta6a yi ba" Anty Amina ta ta6e baki ta ce "To Anty kikasan ko shine baya ai... " katseta Anty Rahama tayi ta hanyar cewa "Kuul dama!!! da baya aihuwa ya haifi Rafi'ah da Abduljalal? Ki dai zauna dai, kina gani duk dukiyar nan su kwashe su barki da dan karamin fili" Anty Amina ta mike ta ce "To ai haihuwar ta Allah ce, duk magungunan da kike kawomin ina sha amma shiru har yanzu" Anty Rahama ta ce "Maza bani abinda zan samu in wuce na bar Umma ita kadai Ikleemah ta fice" daki Anty Amina ta shiga ba jimawa ta fito da sarkan gold ta mikawa Anty Rahama ta ce "Ga dai wannan" Anty Rahama ta washe baki ta ce "To barka, sai a siyar aci gaba da nema maki maganin haihuwa, ina dalili shekara 3 fa kenan babu labari" daga haka tayi kasa kasa da murya ta ce "Ni inaga ma wannan kishiyar taki ce tasa miki hannu, dan taga dake ake tafiya Abuja a barta a Kano" Anty Amina ta ce "Nima dai abinda nace kenan, amma koma menene yazo karshe" Anty Rahama ta nufi kofar fita ta ce "Muna nan dake zakiji labari, to nidai na tafi" Anty Amina ta daga mata hannu ta ce "To sai anjima" daga haka Anty Rahama ta fita ita kuma ta dawo ciki. kwance take jikin Ummi tana ta faman sauke ajiyar zuciya, Ummi ta kamo hannunta tana kallan idanta ta ce "How are u daughter?" A hankali ta ce "Da sauki" Ummi ta gyara mata scarf din kanta ta ce "Allah ya baki lafiya", bude kofar dakin akai Abba ya shigo Abdul na biye dashi, suka karasa kan gadon suna kallanta cike da tausayi, jikinta Abba ya ta6a ya ce "Mamana, ina ke maki ciwo yanzu?" Silently ta ce "My chest Abba, amma kadan kadan yake" Abba ya durkusa dai dai fukarta ya ce "Soon zai daina Mamana, zanje gida na dawo me zan kawo maki?" Ta danyi smiling sannan ta ce "Shawarma Abba" ya shafa kanta ya ce "To Insha Allah" Abdul ya kamo hannunta na hagu yana kallanta ya ce "Get well soon Anty, Allah ya baki lpy me daurewa" kallansa tayi trying hard to control herself ta ce "Thank u love" limshe idanuwanta tayi dan ita kadai tasan abinda takeji deep down, damma da aka mata alluran ya rage mata radadi da ciwo, Abba ya kalli Ummi ya ce "Lie her down and pray Madam, after then itama tayi sallah tayi addu'a sosai kinji Mamana?" Kai ta gyada masa ta ce "To" Ummi ta kwantar da ita ta ce "Allah ya kiyaye, amma Abdul kar ya dawo ya zauna kawai tinda kaima komawa zakayi ai" Abba ya ce "Me zai hana muzo tare mu koma, ai shima yanaso yaga condition dinta" Ummi ta ce "To sai kun dawo" daga haka suka fita ita kuma ta shiga toilet danyin alwala. Yusuf ne zaune a office din Dr. Aryan, bayan ya mishi bayanin abinda ya kawo shi Dr. Aryan ya ce "Allah ya sauwake" daga haka ya kira Dr. Hisham ya sanar masa yadda sukai, on the other side Doctor yace ya kar6a test din nasa sannan ya rubuta masa sabbin magani, after yayi hanging wayar ya kalli Yusuf sannan ya ce "Let me have the test" Yusuf ya mika masa test din, bayan ya duba ya ce "Allah ya sauwke, bari nayi ma wata patient injection idan na dawo saina rubuta maka drugs din, nasan by now she's awake" Dr. Aryan ya karashe maganar yana kallan agogon dake manne a bangon office din, mikewa Yusuf yayi dan sauri yake ya wuce gida, gaba daya he looks so tired, Dr. Aryan ya ce "Can't u wait?" Yusuf ya ce "Let me have the injection saina mata i'm also a medical doctor" daga haka ya ciro ID card dinsa ya mikawa Dr. Aryan, kar6a yayi yaga sunansa, asibitin da yake aiki da year din daya fara aiki sai field dinsa daga karshe, murmushi Dr yayi ya ce "Masha Allah, ashe ina tare da babban likita ne, nice to meet u Yusuf" daga haka ya mika masa allurar Yusuf ya fara hadawa, Dr. Aryan ya kalleshi still smiling ya ce "Me yasa amma baka za6i field din cardiologist ba {Likitan Zuciya}, kodan ciwanka
Chapter 13 · 0% Book details