← Book details Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 30 OF 59

Sashe 30

Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Washegari bayan sallan asuba Rafi'ah ta sauko downstairs ta shiga kitchen, yunwa takeji bata wasa ba, dan rabanta da abinci tin jiya data dawo a school, cup ta dauka ta debi ruwan zafi sannan ta hada tea, ta bude fridge ta dauko bread ta zauna kan kujera ta fara sha, bayan ta gama ta dafa indomie tasa a warmer sannan ta koma upstairs, tana kokarin bude dakinta Ummi ta fito, ta dan sunkuyar da kanta ta ce "Ina kwana" Ummi ta ce "Lafiya, what did u want for breakfast?" Dago kanta tayi tana kallan Ummi ta ce "I already cooked indomie" Ummi ta ce "To aje a shirya" wucewa tayi cikin dakin tana fadin "Insha Allah". Yusuf ne zaune a parlor yana shan tea, sai kiran number Rafi'ah yake amma taki picking, ya danyi murmushi ya ajiye phone din a gefensa dai dai nan Jiddah ta sauko da plate a hannunta, sai side bag dinta da laptop, ta ajiye plate din akan dinning ta karasa gefensa ta zauna, juyowa yayi yana kallanta ya ce "Good morning madam" ta dan kalleshi ta ce "Ina kwana" ya ce "Lafiya, jiya baki tsaya munyi hira ba why?" Ta6e baki tayi ta ce "Bayan kai kake bani labarin waccen yarinyar" Yusuf ya dan zaro ido ya ce "To kiyi hkr, yanzu dai yaushe zamuje gidansu ku gaisa" ta dalla masa harara ta mike ta ce "Ba dai dani ba" kamo hannunta yayi ya ce "Dake mana, bari na gaishe da Umma sai mu fita na ajiyeki a school" ta danyi murmushi tana kallansa, shima din kallanta yake, ya sauke murya kasa a hankali ya ce "U look beautiful Jiddah" ta dan boye fuskarta a bayan laptop ta ce "Kaima kayi kyau Yaya, but jiya kafi kyau" sake hannunta yayi yana murmushi ya ce "U wait me here" daga haka ya wuce upstairs. Da sallama ya shiga dakin Umma, tana zaune gaban mirror taci tsadadden lace, sai powder take shafawa, ta juyo tana kallansa ta ce "Yauwa Yusuf dama yanzu nake cewa Khadija ta maka magana kafin ka fita" zama yayi yana kallanta ya ce "Ina kwana Umma" ta ce "Lafiya kalau, zanje gidan Hajiya Saratu, idan ka tashi a aiki ka biya ka daukoni" a hankali ya ce "To, kenan bada mota zaki fita ba?" Ta ce "Ehh, Khadija zata saukeni yanzu" ya ce "To insha Allah" daga haka ya mike ya fita a dakin. Yana saukowa ya samu Jiddah tsaye tana jiransa, ya dauka key dinsa da lab coat yana kallanta ya ce "Let's go" daga haka tabi bayansa suka fita, hira sosai Jiddah ke masa har suka iso school dinsu, yayi parking yana kallanta ya ce "Study hard Jiddah" ta danyi murmushi ta ce "Insha Allah Yaya" daga haka ta daga masa hannu ta fita a motan. Sadeeq ne ya fito a part dinsu yana jaan trolley, ya dan kalli Jawad dake zaune shiru a parlor ya ce "Good morning" Jawad ya dago yana kallansa ya ce "Morning" daga haka ya limshe idanuwansa ya jingina kansa jikin sofa, bayan few seconds Ikram ta fito, ta dan tsaya tana kallan Yayansu kafin a hankali ta ce "Yaya" bude idanuwansa yayi yana kallanta ta ce "Ina kwana" ya ce "Lafiya, how are u feeling?" Ta ce "Naji sauki, Mami tace ka sameta a ciki" da kai ya amsa mata sannan ta koma ciki, ya mike ya shiga part dinsu hade da sallama, a parlor ya samu Mami tana ta zuge Jakar kayanta, ya zauna yana kallanta ya ce "Gani" bayan ta gama zuge jakar ta dago tana kallansa ta ce "Dama na yanke shawara ka koma gidan Kawu Audu kafin na dawo" ya dago da sauri yana kallanta ya ce "Why Mami?" Ta masa wani kallo ta ce "Is an instruction i'm giving u Ahmad, idan ka dama ka tsallake karka bi" ya sauke kansa kasa baice komai ba, Mami ta ce "I'm just spending two weeks there, idan ka tattara kayanka ka tafi banasan ka sake lekowa gidan nan sai idan na dawo, dan ba zaka zama driver din matar ubanka ba" ba tare daya dago kansa ba ya ce "But what if Abi call me" harara ta galla masa ta ce "Wannan kuma ya rage naka" daga haka ta mike tana gyara zaman sarkan Gold dinta ta yafa veil dinta ta fito, jawo trolley dinta yayi yabi bayanta har zuwa parking lot, Sadeq ya kar6a yasa a boot, karasawa yayi wajen motar yana kallan Mami ya ce "Allah ya tsare" ta ce "Ameen" Ikram na kallansa ta ce "Yaya till we come back" ya daga mata hannu sannan ya koma cikin gida bai tsaya yaga tafiyarsu ba. Da yamma Rafi'ah na shigowa dakinta ta ga phone dinta na haske, ta dago wayar tana kallan screen din, ganin Yusuf ne tayi dan karamin tsaki ta ajiye wayar, daukan laptop tayi ta fito a dakin, ta zauna kan kujera tana kallan Ummi ta ce "Abba yace idan anyi hutu zan bishi Abuja" Ummi ta kalleta kafin ta ce "Ba inda zakije" dan zaro ido tayi tana kallan Ummi ta ce "Nifa ba ruwana da matarsa, kawai inasan zuwa ne" ba tare da Ummi ta kalleta ba ta ce "Waya ce maki tare zasu koma?" Ta bude hannayenta alamar bata sani ba ta ce "Kawai nayi tinanin tare zasu koma ne" Ummi ta dan harareta ta ce "Saboda ke kika haifeshi ko?" dariya ta farayi ta ce "To ai dama ni mamanshi ne" Bude kofar parlorn akai Abdul ya shigo da sallama, Ummi dake kallansa ta ce "Why are u in a hurry?" Ya wuce dakinsa da suri ya ce "Ummi akwai match" Rafi'ah taja tsaki ta ce "Akwai wahala dai, wahalalle kawai" da shirinsa na zuwa ball ya fito, sai kamshi yake kayan kuma sun masa kyau ba kadan ba, Rafi'ah ta ce "Yanzu zai dawo duk doyi" ko kulata baiyi ba ya dauka table water a fridge ya fice, few minutes da fitansa Mustapha yayi knocking, Ummi ta ce "Waye?" Mustapha ya ce "Nine Hajiya, wai Yusuf ne yake sallama da Rafi'ah" sosai kirjin Rafi'ah ya buga, ta dan zare ido tana kallan Ummi kafin ta sauke kanta kasa, Ummi ta ce "Kace tana zuwa" Mustapha ya amsa da toh sannan ya juya, kallan Rafi'ah Ummi ta sakeyi for the second time ta ce "Wa kika cewa Yusuf zaizo yau?" Ta dan kara zare ido ta ce "Wallahi Ummi i don't know he's coming, nima bansan zaizo ba" Ummi ta mike ta ce "This should be the last, banasan haka, idan zaizo u let me know" a hankali ta amsa da toh, Ummi ta ce "Sai ki tashi kije ai" ta mike duk jikinta a sanyaye ta haura sama, wayarta ta dauka taga 16 missed call dinsa sai text messages guda 5, ajiye wayar tayi ta dauka veil dinta ta yafa sannan ta sauko, walking slowly ta fita a parlor tana turo baki harta fita gate. Yana tsaye jikin motarsa yayi folding hannayensa, har ta karaso ta tsaya a gefensa murmushi yake, ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Thank God u came out, how are u Baby?" ta juya kanta gefe bata ce komai, ya ce "Pls talk Fatima, or have i wronged you?" Juyowa tayi ta dalla masa harara, Yusuf ya shafa gashin kansa yana kallanta ya ce "Did..u just eye me Rafi'ah?" ta sake jujjuya idanuwanta tana turo baki, ya ce "Ohk, if that would cool your heart keep eyeing me" shiru tayi bata ce komai ba sai jujjuya ring dinta take, ya danyi murmushi ya ce "Kin gama hararan nawa kuma kin hakura?" ta daga masa kai, ya ce "Good, how are u then?" girgiza kanta ta hauyi a hankali, nan da nan idanta ya ciko da ruwa, Yusuf ya ce "What happened again Rafi'ah, or are u sick?" Ta girgiza masa kai ta ce "I'm not sick, is just u that offended me yesterday" zaro ido Yusuf yyi yana kallanta ya ce "But u just finished eyeing me, ba kin rama ba" ta turo baki tana goge hawayen idanta ta ce "To dan meyasa kake kallan Ikleemeh data kai maka abinci" with surprise Yusuf yake kallanta, ya ce "Who's she?" Ta ce "Jiya bata kai maka abinci ba" har lokacin kallanta yake da mamaki ya ce "To kiyi hakuri insha Allah i promise i won't smile at her again" kanta na kasa tana ta jujjuya ring dinta, ya ce "To kimin murmushi" ta noke kafada, ya ce "Dan Allah Rabi'ah ta" ta dago tana kallansa ta ce "I'm not Rabi'ah" ya danyi dariya ya ce "Haka wancen mai gadin yace min, wai sunanki Rabi'ah" sai lokacin ta danyi murmushi ta ce "That's how he used to call me" ya ce "Then can i contribute" ta kara dariya ta ce "So u want us to fight again?" Yusuf yayi dariya ya ce "Noo, and we are not fighting Allah ma ya kiyaye" a hankali ta ce "Ameen" tana dariya. Zaune yake a parlor yana ta jujjuya tea din hannunsa da spoon saboda yayi sanyi da wuri, Mummy ce ta fito a part dinta tasha lace me kyau, sai kamshi take bugawa, kana kallanta kaga babbar Hajiya, Jawad ya dan sunkuyar da kansa ya ce "Ina yini" ta ce "Lafiya kalau Jawad, su Mami sun tafi ina bacci bamuyi sallama ba" da kai kawai ya amsa, ta ce "Are you not eating food? Gashi fa akan dinning" ya juya yana kallan kan dinning sannan ya ce "I will eat ltr" ta ce "To shikkenan, zanje gidansu Rafi'ah sai dare zan dawo" ajiye glass cup din yayi akan center table ya ce "Let me drop u" Mummy ta ce "A'a ka zauna kasha shayinka Jawad, u don't have to worry zan iya driving ai" bin bayanta yayi yana murmushi ya ce "A'a zan kaiki Mummy" ta tsaya tana kallansa ta ce "To karna baka wahala anjima kuma" ya ce "A'a zan daukoki ai ba abinda nake" Mummy ta ce "To shikkenan muje" ya bude mata back seat ta shiga sannan ya zagaya seat dinsa yayi wa motar key, bayan sun hau titi Mummy ta ce "Abi yace kaci gaba da aiki ko?" Ya ce "Ehh" ta ce "To Allah ya sanya alkhairi"
Chapter 30 · 0% Book details