← Book details Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 4 OF 59

Sashe 4

Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 4 min read

sorry, and insha Allah i won't repeat such thing again" Ummi ta ce "Better, kin kira Anty Haliman ne?" Ta kara turo baki ta ce "Na kirata dazu, nifa wallahi kice mata ta dainamin zancen aure inba hakaba zan daina kiranta duka duka kowa ma ya huta" Ummi ta ce "To menene damuwanki da zancen aurenta? Wallahi koda wasa kar naji kin daina kiranta, banda shashanci irin naki auran za'a miki yanzu? Ki bita kawai a hankali" Rafi'ah ta share guntun hawayenta ta ce "Kuma harda cewa wai nafisan dangin Abba da ita, ni meye ruwana dasu banda gaisuwa daya zama dole" Ummi ta ce "Ki daina min hawaye dama, koma me zata fada u have to listen, ita kadai nake dashi duk duniya, bayan ni baku da wata uwar data wuce Anty Halima" a hankali ta ce "I know Ummi but ni banason yadda Mummy take abu sometimes, komai sai tayi magana haba" Ummi ta ta6e baki ta ce "And i asked u to cook kikaje kika nemi gado kika hau bacci ko?" ta yatsine fuska ta ce "Zanyi yanzu" Ummi ta ce "It's impossible in jira sai kin gama baccinki na jaraba kafin kiyi abinci, na gama rice kije ki rakasa stew din and if u like pls let it burn" daga haka Ummi ta mike ta dauka scripts dinta ta haura upstairs. Kitchen ta wuce ta gauraya stew din sannan ta fito ta wuce upstairs zuwa dakinta, Hijabs dinta guda 3 ta dauko duk color daya sannan ta sakko, Abdul ta samu yana zaune yana cin banana, ta karasa kusanshi ta ce "Abdul pls help me and wash my Hijabs, kaga gobe zanje school kuma Thursday akwai hadda" ya juyo yana kallanta ya ce "Let me finish watching this match, i will wash ltr" ta shagwa6e fuska ta ce "Haba Abdul, kawai kaje ka zuba ruwa a washing machine kasa liquid detergent shine sai anjima that's all it's fah" ya ce "Anty banfa ce bazan wanke maki ba, wai ma meyasa ba kisa an kai laundry ba" ta zaro ido ta ce "Da Mustapha sai yayi sati bai kar6o kayanba ni inada Islamiyya jiranshi zanyi, just tell me idan baza kai ba" tashi yayi ya kar6i hijabs din yana kallanta ya ce "Is that all?" Ta bashi light hug ta ce "Thank u dan kanina me kama da Mummy" daga haka ta fashe da dariya, yaja tsaki ya ce "Ni bana kama da ita, kiba ne kawai kamar ita" bin bayanshi tayi har backyard tana ta dariya ta ce "Allah kuna kama" ya ce "That's what people said, amma ai ni bana fada irinna Mummy, jiya fa dana kirata we spent more than 1 hour muna waya, duk kuma complain takemin a kanki" a wani balcony dake wajen ta zauna ta ce "Na kirata ai yau, ta daiyi fada kam, ni dama idan ta gama Umranta ta dawo Nigeria ta wuce Bauchi mu huta" Abdul yayi dariya ya ce "Gidansu anan kice su wuce Bauchi" ta ta6e baki ta ce "To gidanta kam sai bayan wata wata zan ringa zua". Haka sukaita hiran Mummy har kayan ya gama turning ya tsaya, ta kalli Abdul ta ce "Dan Allah kayi spinning Abdul" ya ce "Komai zan maki ne wai" ta ce "Pls, kaga Salma Umar kaninta har nails dinta yake yanke mata idan yayi tsayi, kaga nima yayi tsayi zaka yankemin ko Abdul dina" Murmushi sosai yayi ya tashi ya fara kwashe hijabs din, duk duniya bayan Abbansu da Umminsu ba wanda ya keso sai luvly sister dinshi, he hate seeing her crying, he hate seeing her unhappy, duk wani abu a duniyar nan da zaiyi turning dinta upside down baya sonsa, wani lokaci ji yake inama lalurar da Allah ya dora mata ya dawo kansa. Ji yayi kawai ta tashi a firgice, ya juyo yana kallanta ta ce "What's that Aunty?" Kamar zatai kuka tana kallansa ta ce "Oh my God, it's burnt, it's brunt i know, Allah na manta dashi ne" daga haka ta zura da gudu tayi hanyar kitchen Abdul ya bita da kallo yana kyalkyala dariya.
Chapter 4 · 0% Book details