← Book details Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 5 OF 59

Sashe 5

Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 4 min read

*Attention pls 🙏🏻*

*This is to inform u that i may not be able to be updating everyday, I'm still in school so sai ranar da kuka ganni kawai, but i promise u that i will try my best to be entertaining u insha Allah, so expect no date of posting, u can see me any day/time. Sannan littafin bana kudi bane na wanda ke da ra'ayin karanwa ne 🥰*

*The page is dedicated to Fadila Madaki* 😍
[6/9, 11:00 AM] Teemarh: *_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

*BY FATIMA* _{Real~Teemarh}_

_5~6_

Anty Khadija ce zaune a babban parlon su da glass cup a hannunta tana shan exotic, lokaci~lokaci ta kan daga kanta ta kalli series din da ake a TV, bayan ta shanye na cikin cup din ta dago kanta tana kallan mahaifiyarta dake zaune a gefenta ta ce "Umma bafa kice komai ba?" Cike da damuwa matar da aka kira da Umma ta juyo tana kallanta, Anty Khadija ta ce "Dole ne fa Umma mu tashi tsaye, wallahi tallahi Yusuf ya kawomin budurwarsa har office dina, i'm still in a state of shock Umma, wai Yusuf da budurwa, lallai kam this is impossible wallahi" Umma ta ajiye remote din dake hannuna ta juyo tana kallan Anty Khadija, sai lokacin ta samu damar motsi, ta kirkiro murmushin takaici ta ce "Ba sai yayi auren ba idan shi yake da iko, indai ina raye rayuwar Yusuf ba zata ta6a kyau ba wallahi, sai dai ya kare rayuwarsa a haka, idan yaso ciwan zuciyar ya kashe shi" daga haka ta mike ta fara haurawa stairs, Anty Khadija taci gaba da chewing gum dinta ta ce "Atoh, indai ba'a dau mataki ba kam komai zai lalace" daga haka ta dora kafarta daya akan daya taci gaba da shan exotic dinta.
kasa dago kanta tayi tana ta wasa da fingers dinta, sai bayan Ummi ta gama mata fada ta ce "Pls don't let me angry again, wallahi zan manta da baki da lafiya na miki duk abinda naga dama" a hankali ta ce "Kiyi hakuri" Ummi ta ce "Ki wuce ki gyara kan dinning" tabi ta gefe a hankali ta wuce zuwa parlor ba tare data bari sun hada ido da Ummi ba. Karfe 8 bayan an idar da sallan isha Yusuf ya shigo parlor, milk shadda ce a jikinsa ta sha aiki, tayi masifar amsar jikinsa kamar dama saboda shi akayi ta, kallo daya Umma ta masa ta dauke kanta, ba yabo ba fallasa ya dan saki fuska ya ce "Sannu da gida Umma" a hankali ta ce "Sannu" Anty Khadija ta ce "Doctor sai yanzu?" ya ce "Wallahi Anty, nayi meeting ne shiyasa na dawo late" ya karashe maganar yana cire lab coat din jikinsa ya nufi dakinsa, Anty Khadija ta bishi da harara kasa kasa ta ce "Wicked man" Umma ta ce "Not only wicked" Anty Khadija ta ta6e baki looking into her mother's eyes ta ce "Ni wallahi Umma a duniya idan akwai wanda na tsana ya biyo bayan Yusuf, duk da nunawa nake ina san shi ina kaunarshi amma bakiga da yadda nasa ya kawomin budurwarta saba" Umma ta harari kofar dakinsa ta ce "Yanzu haka ma wajenta yaje zaice wani meeting yayi, indai ina raye kaida farinciki kunyi sallama, aure kuwa sai dai yaga anayi" Anty Khadija ta ce "Sai fa kinyi da gaske kin kara cusa masa tsanar rayuwar aure, ni dama i just wanted to know ko yana da budurwa yasa na matsa masa, kuma na ganta, fara sool, gata yarinya da ita" Umma ta ce "Ina nan dake shida kansa zaice baya santa wallahi, banda shi ba ma yaji da ciwan dake daminsa zai jajibowa kansa soyayya, ai insha Allahu wannan yarinya itace ajalinsa" Anty Khadija tayi murmushi ta ce "Allah yasa, kinga idan ya mutu ai wancen tsohon zai daina mana maganarsa kowa ma ya huta" Umma ta ce "A juri zuwa rafi dai" kiran daya shigo wayarta ne yasa tayi shiru ta dauka wayar ta kara a kunne, bayan ta gama answering call din ta ce "Wai yaushe Jiddah zata dawo ne Umma?" ta ce "Duk sanda kika dawo da ita, dama bake kikace ta tafi a gidan ba" Anty Khadija ta ce "I'm thinking about something, why not muyi amfani da Jiddah ta hanyar rushe soyayyar Yusuf da waccen yarinyar" Umma tayi murmushi ta ce "Haka ma yayi" daga haka Anty Khadija ta mike ta nufi upstairs tana dialing phone number din Jiddah.
Chapter 5 · 0% Book details