Sashe 11
Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
kuka ta jawo wayarta tayi dialing phone din Mummy, bugu biyu ta dauka tana "Yau an tinoni kenan?" Jin kamar kuka yasa ta ce "Subhanallah, are u crying Rafi'ah?" Cikin kuka ta ce "Koba Anty Amina bace" Mummy ta ce "Menene kuma ya faru? Tazo ne?" Hawayenta ta share kafin ta ce "Jiya sunzo da Abba, kinga yanzu ya gama min fada wai banje na gaisheta ba, danaje kuma na gaisheta tana kallona taki amsawa, wai kuma Abba yace saina rakata shopping, gaskiya ni i can't, i so much dislike her Mummy, kinga fa ita bata zo ta gaishe da Umminmu ba amma Abba yake tilastamu mugaisheta" Anty Halima ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Wipe your tears, ina dalili zaki dinga kuka akan kishiyar uwarki, ki barta caan da mungun halinta, tinda Abbanki ne yayi magana ki rakata, amma idan ta miki ki mata kema, ban yarda ki raga mata ba wallahi, duk wannan asarancin na Zainab ne, ita dan fadan nan ma na mata bata iya ba, wallahi ban yarda kiyo halinta ba, ina dalili keda gidan ubanki a dinga takura miki" Rafi'ah ta turo baki ta ce "Ni banma san dalilin da zaisa na raka taba" Mummy ta ce "Makirci ne irinna mata, ki dai kula da duk wani takunta, aniyarta ta bita caan, kuma koda wasa karki daukar mata kaya ai ke ba 'yar aikinta bace, idan na dawo ma kika koma gidana kikai auranki ina zata ganki" Rafi'ah tayi saurin hanging call din ta tashi ta fito a dakin, da Ummi taci karo zata shiga dakinta, ta 6ata rai ta ce "Ummi kinji wai sai in rakata shopping" Ummi ta ce "And so? Wani abu ne zai ragu ajikinki ko me? wallahi da nasan bakije kin gaisheta ba da sai ranki ya 6aci a gidan nan, ina zaman zamana kin jawomin magana yana fadin ninake kyaleki, saime idan kin gaisheta" ta ce "Ummi to ita gaisheki take?" Ummi ta daka mata tsawa ta ce "Kindly disappear here, wallahi zan 6ata maki rai Rafi'ah" barin wajen tayi hawaye na zuba mata. Bayan ta sauko ta wuce Abba dake zaune a parlor ta fita compound din gidan, ta karasa parking lot ta jingina da mota ta wani hade rai. Kusan ten minutes tana tsaye kafin ta fito walking slowly tana ta chewing gum, an sha kwalliya kai kace gidan biki zata, Mustpha yayi saurin bude mata back seat jikinsa na rawa, bayan ta shiga ta ce masa "Ka cewa wannan yarinyar ubanta baice mata tare zamu tafi bane?" Rafi'ah ta dago kanta da sauri jin abinda tace, ta kara folding hannayenta tana tsaye jikin motar Abba, Mustapha ya karasa kusanta a hankali ya ce "Hajiya karama ke ake jira" ta dalla masa harara ta juya kai gefe, Abba ta hango ya fito da waya kare a kunnensa yana answering call, hakan yasa tayi saurin shiga motar tana ta turo baki Mustapha yaja suka wuce. Tafiyar minti 20 sukayi kafin suka iso shopright, bayan Mustapha yayi parking suka sauka suka karasa ciki, ita dai Rafi'ah sai binta take tana dalla mata harara ta gefen ido, almost 1 hour suna zagaye amma abu guda 4 kawai ta dauka, kuma ita da kanta ta rike basket dinta, ta dan saci kallan Rafi'ah ta ta6e baki ciki ciki ta ce "Sai kin gaji da yawo yau munafuka" suna tsaye a wani waje wani dan saurayi yazo wucewa, ya danyi murmushi kafin ya ce "Excuse pls Madam" Anty Amina ta matsa tana binsa kallo ya shige, juyowa yayi ya kalli Rafi'ah sannan ya kara kallanta, hade ran da tayi yasa ya juya ya tafi abinsa dan da niyyarsa ya mata magana. suna tsaye awajen sukaji ance "Fatima" Rafi'ah tayi saurin juyowa tana murmushi, wara manyan idanuwanta tayi ta ce "Doctor" yana rike da hannun Khairiyya ya karasa gabanta ya ce "How are u?" Ta ce "Fine, is this your sister?" Ya danyi murmushi yana kallan Khairiyya ya ce "Yes, she is" Khairiyya dake rike da Baby doll dinta ta ce "Good Afternoon" Rafi'ah ta shafa kanta ta ce "How are u little girl? U are so cute" Yusuf ya cusa dayan hannunsa a pocket dinsa as usual ya ce "Thank u, are u leaving now?" Ta girgiza kai ta ce "Actually no, and i came with driver" ya ce "Alright, that's good" sai lokacin idansa ya sauka akan Anty Amina dake gefen Rafi'ah tana rike da basket, tin zuwansa ta kura masa ido ko kiftawa babu, kallan Rafi'ah yayi a hankali ya ce "Are u together with her? I mean the lady besides u" Rafi'ah ta daga masa kai ta ce "Yess, my housemaid" jin haka yasa Anty Amina ta gwalalo ido tana kallan Rafi'ah ta ce "I don't understand, who's your housemaid here?" Ta kallai Yusuf sannan ta kalli Anty Amina ta ce "Let's move from here pls" Yusuf ya dan matsa gefe sannan tabi bayansa itama, sororo Anty Amina tayi tana kallan Rafi'ah, daga haka ta cije baki ta saki basket fin hannunta fuuuu ta bar wajen cikin sauri. Dariya sosai Rafi'ah ta kyalkyale dashi harda kama ciki, sai yanzu abinda ta fada yayi mungun bata dariya, Tsayawa kawai Yusuf yayi yana kallanta with confusion, ta kai minti 5 tana ta kyalkyala dariya kafin ta kalli Yusuf ta ce "Anywhere thank u much" ya danyi shiru sannan ya ce "Are u sure she's your housemaid?" Ta ce "Of course, kasan idan suka waye sai a hankali, wai yanzu fishi tamin, dama tana ta rokona kar watarana na copsa mata", Yusuf yayi murmushi ya ce "And u did?" Sake dariya tayi ta ce "Why will i not Doctor" ya sauke ajiyar zuciya yana kallanta, Sweet da chocolate ta kwasarwa Khairiyya ta biya kudin sannan suka fito, sai bayan sun fita ta mika mata ledan ta ce "This is yours little Baby?" Khairiyya ta kalli Yusuf sannan ta kar6a ta ce "Thank u" Rafi'ah ta kama hannunta ta ce "What's your name?" A hankali ta ce "Fatima Khairiyya" Rafi'ah ta dan wara ido looking smiley ta ce "Woow ashe namesake dina ne" dai dai lokacin ta kalli inda sukai parking taga ba motarsu a wajen, Yusuf dake kallanta ya ce "Where are they?" Ta ce "May b they've gone" ya ce "Ohk, let me drop u home" tabi bayansa har suka isa inda motarsa take, back seat ya budewa Khairiyya bayan ta shiga ya budewa Rafi'ah front seat ta shiga sannan ya zagaya seat dinsa ya sawa motar key, suna hawa saman titi ya kalli Rafi'ah dake murmushi ya ce "Who's she? I mean the woman?" Ya kara tambaya for d second time, silently ta ce "Stepmother" tana rife bakinta ta sheke da dariya tana kai kanta kan cinyoyinta, surprisingly enough Yusuf yake kallanta ya ce "Do u mean your Daddy's wife?" Ta daga masa kai still laughing ta ce "Nima ramawa nayi, haka kawai ta fito dani just to make me angry, munkai awa muna zagaye amma wadannan abin daka gani a basket su kadai ta dauka" ta kara turo baki ta ce "Ai dani take wallahi" Yusuf couldn't hold his laugh, yayi dariya kafin ya ce "Zaki sha fada wajen Daddy ai" ta ce "Ba fada ba? Aini ba yanzu na saba jin fada ba" yayi nodding kansa ya ce "Kin saba kenan?" Ta ce "Noo" ya sake kallanta ya ce "Since from the first day i saw u nayi noticing u are stubborn" ta danyi murmushi ta ce "And it isn't true, ina rama abinda akamin ne kawai that's all" ya maida hankalinsa ga tuki ya ce "Wane area kike?" Ta ce "Hotoro GRA" daga haka ta fada mishi house number din. Anty Amina na komawa gida apartment dinta ta nufa ta kasa zaune ta kasa tsaye, ita abinda Rafi'ah ta fada bai dameta sosai ba kamar kamannin Yusuf, tabbas bazata ta6a mantawa dashi a rayuwa ba, amma da dukkan alamu bai gane taba, a hankali ta ce "Kaddai saurayin Rafi'ah ne?" Daga haka ta lalibo wayarta cikin hand bag dinta ta fara neman phone din Abba. Bugu daya ya dauka ya ce "I will call u ltr i'm busy now" daga haka yayi hanging call din, a bakin titi Rafi'ah tace Yusuf ya ajiyeta, tayi masa godiya sannan ta shafa kan Khairiyya ta ce "Bye little girl" Khairiyya ta daga mata hannu sannan ta juyo tana kallan Yusuf ta ce "My house isn't far from here, so nagode sosai" ya danyi murmushi ya ce "Mention not" daga haka ta shiga cikin layin walking very slowly tana auno fadan da Abba zai mata, tasan duka kam is impossible tinda ba ta6a mata yayi ba. Cikin sauri Anty Khadija taja birki ganin Rafi'ah, if she could recall itace yarinyar da Yusuf ya kai mata office dinta, kafin tayi parking ta fito tuni Rafi'ah ta tura gate ta shige gida, ta dinga kallan dankareren gidan kafin taja motarta tayi gaba, motar Yusuf ta gani akan junction ya tsaya suna gaisawa da wani, lokaci daya jikinta ya bata cewar shi ya ajiye Rafi'ah yanzu, ganin yadda yake ta fara'ah suna gaisawa da mutumin ya tabbatar mata da cewa Yusuf yana cikin farinciki, abinda ta tsana ta ganshi a ciki kenan, tayi mungun tsanar ta ganshi yana murmushi, taja wani dogon tsaki sannan taja motarta ta tafi a wajen ta ce "Ba dai naga gidansu ba, muje dai zua" daga haka ta kara speed din motarta tayi hanyar gida.