← Book details Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 20 OF 59

Sashe 20

Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 4 min read

_I LUV U FANS_ 😄

*SHARIK HAYATI*

_08103810398_

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

*BY FATIMA* _{Real~Teemarh}_

_21~22_

Karfe uku da rabi Ummi ta shigo dakin Rafi'ah ta tashe ta a bacci, tayi mitsi~mitsi da ido tana kallan Ummi ta ce "Abdul din bai dawo ba shine na kwanta" Ummi dake kallanta ta ce "Abdul Baffa ya kirashi, ki tashi ki shirya Mustapha ya kaiki, shi yaje daga baya" turo baki tayi ta janye duvet din jikinta ta ce "But Abba said we should go together" Ummi ta wurga mata harara ta ce "To karki shirya ki sauko, continue arguing with me" tana dasa aya ta fita a dakin taja mata kofar, Rafi'ah ta sauke ajiyar zuciya kafin ta mike ta shiga toilet, few minutes ta fito da towel a jikinta, ta zauna gaban mirror ta shafe jikinta sannan ta bude press dinta ta dauko atampa ta saka, das~das dinkin ya zauna a jikinta, tayi combing hair dinta sannan ta daura head tie dinta ta saka hijabi iya knees dinta, babu ko powder a fuskarta amma tayi kyau sosai, ta dauka side bag dinta da phone sannan ta sauko downstairs. Ummi ce kadai a parlor da laptop a gabanta, Rafi'ah ta zauna gefenta ta ce "Na shirya" Ummi ta dago tana kallanta ta ce "Ko powder ba zaki shafa ba Rafi'ah?" dan bakinta ta turo ta ce "Ni haka nakeso" Ummi ta ta6e baki ta ce "Ga turare ki kaiwa Umma, my regards to them" ta karashe maganar tana mikawa Rafi'ah ledan da turaren yake ciki, kar6a tayi ta mike ta ce "Sai na dawo" Ummi ta ce "Ki gaishe su, bayan Magrib zai koma ya dauko ki" a hankali ta ce "Toh" sannan ta fita a parlor. 10 minutes with some seconds ya kaisu gidan Umma, Mustapha yayi parking a waje ta masa sallama sannan ta fito ta shiga gidan, ba kowa a compound din sai mota kwaya daya a parking lot, ta karasa entrance din gidan ta murda handle din kofar ta shiga da sallama, babu wanda ya amsa mata sai ido da suka zuba mata duk tasu, dan basuyi zatan zuwanta gidan ba, dama mostly da Abba suke zuwa. A hankali Rafi'ah ta karasa cikin parlor ta zauna a kan carpet ta ce "Ina wunin ku?" Ba yabo ba fallasa Anty Rahama ta ce "Lafiya kalau" Anty Amina kuwa kota daga kanta ta kalli inda take. Bayan 10 minutes Anty Rahama ta kalli diyarta dake kwance kan sofa ta ce "Ikleema tashi kuje ki nuna mata toilet dina ta wanke min" with surprise Rafi'ah take kallan Anty Rahama, tashi tayi tana gyaran wuyan hijab dinta ta ce "Dama Abba cewa yayi nazo na gaishe da Umma, ga wannan inji Ummina a bata" daga haka ta nufi kofar fita, Ikleema ta ce "Ai gara da kika tafi gayyar tsiya" Rafi'ah ta juyo tana kallanta ta ce "Ga tsiya kam ai kina cikin ta" ganin Anty Rahama ta taso tana kunduma zagi yasa taja musu kofar da gudu ta nufi gate ta fita, cikin sauri ta karasa bakin titi ta tsare me Napeep ta shige, sai sauke ajiyar zuciya take tana huci, bayan minti 2 mai Napeep din ya juyo yana kallanta ya ce "Ina zakije 'Yammata?" A hankali ta fada mishi inda zai kaita sannan ta kifa kanta tana kokarin dai dai ta numfashinta. Bayan ta iso gida ta cire 500 a jakarta ta bashi ya bata change sannan ta shiga gida, tana bude kofar parlor Ummi ta ce "Zo nan Rafi'ah" baya ta dan ja ta ce "Wallahi Ummu ba abinda na musu" Ummi da ranta ya gama 6aci ta ce "Of all abinda na fada miki baki jiba Rafi'ah sai da kikaje kika jawomin magana" Rafi'ah ta dan zaro ido ta ce "I swear Ummi ni ban ce musu komai, bafa dasu nake ba, nida Ikleema nake" Ummi ta ce "I'm that kind of mother who doesn't talks but kika kaini karshe billahil azeem u will regret" Rafi'ah dake tsaye bakin kofa ta share guntun hawayenta ta ce "Ai dama nasan Abba zasu kira suce na zagesu, kuma wallahi ni ba dasu nake ba, Ikleemah ce ta fara cemin gayyar tsiya" daga haka ta fashe da kuka ta tsuguna a wajen, Ummi taja tsaki ta ce "Tinda kinsan dama neman fada suke data zageki ai saiki mata shiru, gashi nan yanzu sun hada karya da gaskiya sun gayawa Abba, sai kuma kisan abinda zaki ce masa ya sauko" daga haka Ummi ta mike ta shiga kitchen, tashi Rafi'ah tayi ta share idanta ciki ciki ta ce "Wallahi duk wanda ya hadani da Abba shida Allah" Ummi da fitowanta a kitchen kenan ta ce "Ke dai kika sani kuma, and don't involve me in this case, ko sunana ban yarda ki kira ba, banasan abinda zai 6ata min rai ina zaman zamana" Rafi'ah ta sake tare hawayen idanta ta wuce dakin Abdul.
Chapter 20 · 0% Book details