Sashe 22
Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
take kuma?" Ummi ta ta6e baki ta ce "Ina zan sani Anty" Mummy ta ce "Allah ya kyauta" daga haka ta shiga motar Mustapha yaja suka bar gidan. Minti 15 ya kaisu gidan Mummy, suna horn aka bude gate din, Mustapha yayi parking suka fito sannan ya musu sallama ya juya, bin bayan Mummy Rafi'ah take har suka iso entrance din gidan, Mummy ta murda handle din ta shiga Rafi'ah tabi bayanta, Abi ne zaune a parlonsa yana kallo, ya danyi murmushi ganin Rafi'ah ya ce "Future Barrister" ta boye fuskarta tana dariya, dan bata manta sanda take haukar ita lawyer ce, har zare take daukowa tana daurawa mutane a kafa wai shine handcuff, Abi yayi dariya ya ce "Ina dai baki fasa zama barristern ba?" Zama tayi a kasa still smiling ta ce "Ina yini Abi" ya ce "Lafiya kalau Fatima, how are u and them" a hankali ta ce "Kowa lafiya" ya ce "Ya jikinki kuma?" Ta ce "Da sauki sosai" ya dan kalli Mummy ya ce "Ya kuka samesu?" Ta ce "Duk lafiya suke" tana rife bakinta mahaifiyar Jawad ta fito daga side dinta, ta wani hade rai, Rafi'ah ta ce "Ina wuni" ciki ciki ta ce "Lafiya" Mummy ta kalli Rafi'ah ta ce "Tashi ki shiga ciki Rafi'ah" mikewa tayi ta shiga bangaren Mummy, Abi ya tashi yana gyara babban rigarsa ya ce "Madam zan fita fa" ta ce "Zuwa ina?" Ya ce "Nace Sadeeq yazo muje shopping, naga ba komai ne akwai a gidan ba" ta ce "Allah ya kiyaye hanya" daga haka ta ya fita ita ma ta mike ta shiga bangarenta. Bai fi 10 minutes da fita ba Jawad ya shigo gidan hannunsa rike phone sai car key dinsa, direct side din Maminsa ya nufa, Ikram ce kadai zaune a parlor tana kallo a system, ta dan dago kanta ta kalleshi ta ce "Sannu da dawowa Yaya" ya ce "Sannu, ina Sadeeq?" Ta ce "Sun fita da Abba" mikewa yayi zai fita yaji maganar Mami ta bayansa, ya juyo yana kallanta ya ce "I thought kin fitan ai" ta dalla masa harara ta ce "Ka sameni a dakina yanzu" daga haka ta juya ta koma ciki, kusan minti biyu yana tsaye kafin ya zura hannayensa cikin aljihun wandansa ya nufi dakin ta, yana shiga ya tura kofar ya rufe ya tsaya jikin mirror, ta ce "Sai nace ka zauna kenan?" zama yayi akan stool din dake wajen, Mami da ranta ya gama 6aci ta ce "Maimakon da ka kai matar uban naka ka dawo ka kaini saika nemi waje ka zauna" ya dago kansa yana kallanta ya ce "Naje court ne Mami, na samu urgent call around 9, Anty kuma Abi ne yasa ni na sauketa a gidan kanwanta" Mami ta ce "Ai dama kai duk inda zakai suna nan kake xua, da yace ka sauketa why not go and leave her, in yayi magana kace ka manta" a hankali ya ce "Kiyi hakuri" taja tsaki sannan ta mike, shima mikewa yayi ya ce "Zan kaiki din ne?" Ba tare data kalleshi ba ta ce "Zaman jiranka zanyi, Sadeeq dake neman lada ai ya kaini" sunkuyar da kansa yayi ya ce "Sai anjima" daga haka ya fita a dakin. Yusuf ne tsaye gaban mirror yana gyara zaman hular kansa, farar shadda ce ajikinsa tayi bala'in masa kyau, sai kamshi yake, ya dauki key din motarsa da wayarsa ya fito a dakin, Anty Khadija ce kwance a parlor tana gyangyadi, jin kamshin turarensa yasa ta zabura ta bude ido, sai da ta saki murmushi kafin ta ce "Doctor daga nan kuma sai ina?" Ya dan kalleta sannan ya dauke kai ya ce "Somewhere" bai jira cewarta ba ya fice ya jawo mata kofar, yana zuwa parking lot yasa key ya bude motarsa ya shiga, kunnata yayi yana jira tayi warming dan yau tun safe ba inda yaje, ko sallar juma'a ma a unguwa yayi baiyi nisa ba. Jiddah ce ta shigo gidan duk a gajiye, kana kallanta kasan daga school take, suna hada ido ta saki murmushi ta karasa inda yake ta ce "Yaya sannu da dawowa" a hankali ya ce "Sannu kema" ta ce"Umma tace ka bada kudi a fara hada min lefe nago..." Kallan daya watsa mata yasa tayi shiru tana kallansa, ya ce "Akai forcing dina dai, tin farko ai nunawa sukai basa so, saboda haka nima na hakura, u go and find someone but not Yusuf" Kallansa kawai Jiddah take with expression, she's just lost of words, nan da nan idanuwanta suka kawo ruwa ta ce "Amma kasan ina sanka Yaya, wallahi bazan iya rayuwa babu kai ba" jaan motarsa yayi ya wuce ya barta tsaye a wajen, kuka me karfi ta saki ta nufi cikin gida da gudu tana kiran Umma. Sai da Yusuf ya tsaya yayi sallan la'asar sannan ya karasa gidan Mummy, dai dai kofar gidan yayi parking bayan ya duba house number, bayan yayi parking ya fito ya jingina jikin motarsa ya fara kiran wayar Rafi'ah, suna zaune ita da Mummy suna hira kiran ya shigo, ta mike ta dauka wayar sannan ta shiga daki, ya ce "I'm outside dear" ta ce "Alright gani nan" daga haka ta ajiye wayar ta daukar well ironed himar dinta ta saka, powder kawai ta shafa da lip stick sannan ta fito rike da wayarta a hannu ta ce "Mummy bari naje waje" Mummy ta washe baki ta ce "To ya shigo compound mana" Rafi'ah ta dan zaro ido ta ce "Kaiii Mummy class mate dina ne fa" Mummy ta ce "Hmmm, shi class mate din ba zai shigo cikin gida ba sai ya tsaya a bakin gate" ita dai Rafi'ah bata ce komai ba ta fita a parlorn, tana fitowa ta samu Ikram a parlorn Abba tana zaune, suna hada ido kowacce ta dauke kai Rafi'ah ta nufi kofar fita. Tin fitowarta Yusuf yake murmushi yana kallanta, bayan ta karaso tasa tafikan hannayenta ta rife idanta ta ce "Ni kadaina kallo na" ya danyi murmushi ya ce "U look more beautiful in hijab, kinyi kyau sosai" a hankali ta ce "Kaima kayi kyau" ya ce "Sure?" ta daga masa kai, ya ce "To ai baki kalleni ba kuma" sai lokacin ta bude fuskarta ta kalleshi sannan ta ce "Da gaske kayi kyau" ya ce "Thank u so much, how is Mummy" ta ce "She's fine" ya ce "Khairiyya na gaisheki, she always asked for you" Rafi'ah ta dan turo baki ta ce "Ba kaki kawota ba" ya ce "Sai kinje kin gaishe da Amminta, kinga by then small mum dina ta sanki sai itama in kawota taga Antynta" Rafi'ah ta danyi mirmushi ta ce "To sai wataranan" ya ce "Allah ya kaimu, Amma wannan karan idan Abba yazo zan sameshi na fada mishi" da sauri ta ce "Me?" Ya ce "Ina neman izini a bani ke" tayi saurin rife fuskarta bata ce komai ba, ya ce "Ko wajen Mummy zan kama kafa?" Ta girgiza kai kawai tana murmushi. Sun kai minti 30 tsaye a wajen suna hira, ita dai Rafi'ah sai uhmm ko murmushi duk shi kadai yake surutun, ya lankwashe kansa irin yadda tayi ya ce "To sai yaushe zamu sake haduwa Baby" ta kyalkyale da dariya ta ce "Aini ba haka nake magana ba" ya ce "Ko, to bari na sake gwadawa" ya dan shagwa6e fuska just like she used to ya ce "Ni dai banaso mu kara kwana 2 ban ganki ba" dariya sosai ta kyalkyale dashi harda sunkuyawa, dai~dai lokacin Jawad ya bude kofar gida ya fito, ya kura musu ido yana kallansu, Yusuf dake murmushi ya ce "Serious haka kike, and i like it" ta tsaya da dariyar da take cewa "That's what u said dai" ya ce "Allah kuwa, sai munyi waya ko, i have to go, zan je gidan abokina" ta ce "Alright safe" Yusuf ya ce "Waye wancen?" Ya karashe maganar yana kallan inda Jawad ke zaune, suna hada ido ya hade rai ya kauda kansa gefe, Rafi'ah ta ce "Dan gidan ne" ya ce "Ohh Mummy tana da rival ne?" Ta ce "Yess, but ya fara auren Mummy kafin mamansu, shi ne babba" Yusuf ya dan daga kafada ya ce "Ohk, yanzu sai yaushe?" Ta ce "Sanda kace" ya ce "To sai munyi waya" ita da kanta ta bude masa kofar motar, bayan ya shiga ta rife sannan ta durkusa tana kallansa ta glass ta ce "Allah ya kiyaye, ka tafi very gentle" Yusuf yayi murmushi ya ce "Thank u LIFE PARTNER" ta sunkuyar da kanta tana murmushi ta matsa jikin motar tana daga masa hannu ta nufi cikin gidan. Yusuf yayi reverse yana ta dariya, yana juyawa ya dagawa Jawad hannu, dauke kansa ya sake yi ya maida gefe, bayan Yusuf ya wuce ya bi motarsa da wani irin kallon da baza'a kirashi da harara ba. Daga haka ya mike ya shiga cikin gidan, a parlorn Abi ya zauna ya kurawa TV ido, Mami ta fito tana kallansa ta ce "Kai ba abinda zaka dauka ne na tafiyar?" Ya dago kansa yana kallanta ya ce "I'm not going" Mami ta masa kallan kama isa kafin ta ce "Wannan kuma karyane wallahi, kafata kafarka a gidan nan, sai dai idan kaje Abujan kayi ta zama a daki" Tashi Jawad yayi ya fice a parlor, Mami ta bishi da harara ta ce "Wawa kawai, wallahi ba dan a gida na haifoka ba cewa zanyi canzamin kai akayi" daga haka ta koma dakinta tana dialing wayar Abi.