Sashe 37
Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 6 min read
gashi idan ciwan ya tashi saita fita a hayyacinta, batasan ma waye a kanta ba, ni tsorona kar tazo ta ya6a mana wani kalan cutan mu shiga uku, kinga wancen zuwanta ma Ikraam kwana tayi da zazza6i" Haj. Kareema dake sauraron Mami ta ce "Ai gara kuyi nesa da ita" Mami ta ce "To kinga, ina dalili zata dinga min zarya a gida kaalan ta cuci 'ya'yana ta ya6a musu ciwo". Rafi'ah na zaune gefen Mummy tana matsa mata kafa ta ce "Doctor yace zaizo gaisheki, kuma wai zai kawo maki maganin ciwan kafa, inaga wanda kike shafawa zaki barshi ki gwada wannan" Mummy ta mike zaune ta ce "To Allah ya kawo shi, Yusuf akwai hankali da nutsuwa dan Allah Rafi'ah karki watsa masa kasa a ido, ya soki tsakani da Allah, ki zauna da matarsa zuciya daya, ba ruwanki da kishiyarki ce kiyi iya kokarinki a kanta, i know u are good in caring but pls ki dage kinji Mamana" tana murmushi ta daga kanta ta ce "Insha Allah Mummynah, mezan dafa miki?" Mummy ta ce "Yanzu dai tinda nayi wanka ki hadamin tea, amma lipton kawai da lemon tsami banda sugar" Rafi'ah ta ce "To bari naje" daga haka ta mike ta fito a parlorn Mumny, yanzu kam ba kowa zaune a parlorn Abi, ta wuce kitchen ta dauka mug ta dauraye sannan ta debi ruwan zafi a flask tasa liptopn, tana bude fridge Mami ta shigo, cikin sauri ta ce "Ke dakata" Rafi'ah ta dago kanta tana kallanta, Mami ta rufe fridge din ta ce "Ba kowa ake bari ya bude fridge dinba, ga cututtuka sunyi yawa a duniya, kowa saiya da6a hannunsa a handle din ya bude, irin haka ai sai a dauki cuta" gefe Rafi'ah ta koma tana kallan yadda take goge handle din Fridge din da towel, bayan ta gama ta gefar da towel din ta bude fridge din tana kallan Rafi'ah ta ce "Me zaki dauka?" A hankali ta ce "Leman tsami" Mami ta dauko leman tsami daya ta ajiye mata a kan drawer ta ce "Dama daga yau kina kiyayewa duk abinda kikasan in kin ta6a wani zai ta6a wajen ki barshi kawai, ga mai aiki ki sata tana miko miki" sauke kanta tayi cikin cool voice dinta ta ce "Mami nifa banda wani cutar da za'a dauka" wani kallan rashin mutunci Mami ta mata ta ce "A hakan, ki kalleki fa, to nidai bazance komai ba, amma dai ki kiyaye duk abinda na fada miki, ciwan zuciyar da akace idan mutum yana dashi ka ta6a guminsa kaima saika kwasa fa?" tana rife bakinta ta fice a kitchen din Rafi'ah ta bita da kallon mamaki, kallan leman tsamin ta dinga yi kafin ta dauka ta wanke sannan ta dauki wuka ta yanka shi biyu, tana matsawa cikin tea din wasu hawaye masu zafi suka shiga sakko mata, yanzu har itane za'a ce bazata ta6a waje ba kar ta shafa musu cuta, to cutan me take dashi bayan ciwan zuciya? Shikuma tasan heredity ke kawoshi mostly, dan itama a familyn Abbanta ta gada, Jin kamar footsteps a bayanta yasa tayi saurin goge idanta ta dauka tea spoon, tana juyowa suka hada ido da Jawad, tayi saurin sauke kanta kasa tabi ta gefensa ta fita. Tana kaiwa Mummy tea din wayarta ya hau ringing, ta ciro a jaka sannan ta daga call din, "Ok" kawai tace sannan ta kalli Mummy ta ce "Yazo" Mumny ta ce "To ki shigo dashi parlorn Abi ba sai ya shigo ciki ba" ta ce "To" sannan ta zura hijabinta ta fita, a bakin gate ta sameshi ya jinginu da motarsa hannunsa rike da key, yaci manyan kaya yayi kyau sosai, ta sauke kanta kasa ta ce "U are welcome" ya ce "Thank u Baby, what's wrong with ur eyes?" Ta ce "Daxu abu ya fadamin" ya ce "Ayyah sorry, hope ya fita?" Ta daga masa kai, ya ce "Alhamdulilah", ta dan kalleshi ta ce "Ka shigo ku gaisa" ya ce "Ohk" daga haka ya bude mota ya ciro carton din Malt da leda cike da Apple, yana shigowa gate man ya kar6eshi, da sallama suka shiga parlorn, gate man ya ajiye abubuwan sannan ya fita Yusuf ya zauna kaan carpet yana kallan hoton Jawad dake manne a wall, ba jimawa Mummy ta fito Rafi'ah na biye da ita, tana murmushi ta zauna, ya sauke kansa kasa ya ce "Ina yini Mummy?" Ta ce "Lafiya Yusuf ya aiki kuma" ya ce "Alhamdulillah, ya karfin jiki?" Ta ce "Jiki yayi sauki, Allah ya saka da alkhairi" a hankali ya ce "Ameen" sannan ya ciro maganin ciwon kafan ya ajiye mata a gefe. Sun dan jima kafin Mummy ta shiga ciki, Rafi'ah ta zagayo ta zauna kusa dashi ta ce "Ya Anty Jiddah fa?" ya ce "Tana nan lafiya, yaushe zamuje wajen Ammi ne, ta damu kije mata" a hankali tayi murmushi ta ce "Ko ranar Monday inna dawo a school" ya ce "To Allah ya kaimu" mikewa tayi ta nufi fridge din parlor ta bude ta dauko mirinder da coke sannan ta dora akan tray ta dauki glass cup, tana juyawa Mami ta fito daga part dinta, ta dinga kallanta kafin ta ce "Ke wai wacce irin dabbar yarinya ce, ba ance miki karki sake ta6a mana fridge ba" still tayi waje daya jikinta na rawa, Mami ta kar6a tray din hannunta ta ajiye akan dinning ta ce "Haba, mace kamar mayya, aiko maye yana gane magana wani lokaci" Yusuf dai na zaune yana bin Mami da kallo, Rafi'ah ta koma ta zauna a hankali duk jikinya a mace, ganin sun hada ido da Mami ya ce "Ina yini" ta dalla masa harara, Yusuf ya mike yana kallan Rafi'ah da kanta ke kasa ya ce "Dear, i'm going" daga haka ya nufi kofa, kallan Rafi'ah Mami tayi ta ce "Dama karuwancin naki ba iya gidanku ya tsaya ba harda gidan mutane?" Caak Yusuf ya tsaya jin abinda ta fada, nan da nan hawaye suka shiga sakkowa a idan Rafi'ah, Yusuf ya juyo a hankali yana kallan Mami ya ce "Mama niba mazinaci bane, kuma abinda kika fada saam bai dace ba, saboda baki da shaidar abinda bakinki ya furta" Mami ta ta6e baki ta ce "Idan kai ba mazinaci bane ai ita kowa yasan nata, to tinda tare na ganku ai zance duk kanwar ja ce" Yusuf ya dinga kallan Mami with much surprise ya ce "Mama!!!", bude kofar akai Jawad yayi sallama, Mami ta saki kuka ta zauna akan kujerar dinning, Jawad ya karasa kusanta da sauri ya riko hannunta ya ce "What's wrong Mami?" Ta dago fuskarta hawaye sha6e sha6e ta ce "Wallahi wannan bawan Allan ne Jawad ya cimun mutunci, daga gani ma shaye~shaye yake, saboda kawai nace bako baka gaisuwa ne" nan da nan Jawad ya mike ya daga hannu yayi kaan Yusuf, Rafi'ah ta fashe da kuka, dai dai nan Mummy ta fito a part dinta da sauri har kamar zata fadi...