Sashe 55
Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 5 min read
kuka me cin rai. Haka Rafi'ah taci gaba da hakuri, tin daga ranar duk maganar da zatai masa sai dai ya daga kai koya girgiza mata kai sai kace kurma, amma idan da Jiddah ne sukanyi hira wani lokaci, wani lokaci kuma zai kulata amma ba sosai ba, Rafi'ah kuwa babu abinda yake hadasu, yanzu a parlor ma yake kwana indai a dakinta yake, wani lokaci tayi kuka harta godewa Allah, wani lokaci kuma tayi hakuri amma ko kadanne saita zubar da hawaye, a haka har ta cika wata daya a gidansa duk ta kara ramewa tayi farii sosai saboda damuwa, kuma koda wasa bata gayawa kowa a gida ba. Ranar Saturday da yamma tana zaune a main parlor aka fara knocking, ta mike a hankali ta karasa kofar sannan ta bude, rungumeta Khairiyya tayi ta ce "Oyoyo Anty" itama rungumeta tayi tana kallan Ammi ta ce "Sannu da zuwa Ammi" Ammi ta shigo parlorn tana murmushi ta ce "Sannu Fatima" Rafi'ah na rike da hannun Khairiyya ta ce "Have a seat Ammi" Ammi ta zauna akan kujera, zama Rafi'ah tayi a kan carpet ta ce "Ina yini?" Ammi ta ce "Lafiya kalau Fatima, fatan duk kuna lafiya?" Ta ce "Alhamdulilah Ammi" mikewa tayi ta shiga kitchen Khairiyya ta biyota, abinci ta kai wa Ammi da fruits sai dambu da Mummy ta aiko mata jiya, bayan ta gama jere mata ta dauko fanta guda biyu da cups ta ajiye mata, Ammi ta danyi murmushi ta ce "Sannu da kokari" ita dai murmushi kawai take kanta na kasa, Khairiyya ta zuba abincinta ta fara ci, Rafi'ah na kallanta ta ce "Yaushe zaki zo mana hutu?" Khairiyya ta ce "Soon Anty, muna gama exams zanzo, jss3 zan shiga fa" Rafi'ah ta danyi murmushi tana kallanta ta ce "Masha Allah, i wish u all d best" "Shiru Rafi'ah baku zo mana ba muma bamu zo ba" dagowa tayi jin muryar Ammi, with smile on her lips ta ce "Ammi ai yanzu baya dawowa da wuri sai yamma sosai shiyasa, kuma har weekend fita yake" kafin Ammi tayi magana aka bude kofar, ya shigo yana kallansu sannan ya nemi waje ya zauna, silently ya ce "Sannu da zuwa Ammi, ina yini?" Ta ce "Lafiya kalau, yanzu nake tambayarka ai, baka kaita ba kai baka zo ba muma kuma shiru" dan shafa kansa yayi yana murmushi ya ce "Wallahi Ammi aiki ne yamin yawa yanzu, amma insha Allah zamu zo" ta ce "To Allah ya kaimu" Khairiyya na kallansa ta ce "Yaya ina yini" ya ce "Lafiya Ammina, karfa ki cinye mana abincin mu" ta danyi murmushi ta ce "Ai Anty Fatima zata dafa maka wani" kallan Rafi'ah dake zaune ya danyi sannan ya dauke kai ya ce "Sai dai ke ki dafa min ai" ta danyi murmushi taci gaba da cin abinta, Yusuf ya ce "Ammi ke ba xaki ci abincin ba?" Ta ce "Alhamdulilah Yusuf na koshi" ya ce "Sameer ya tafi ko?" Ta ce "Ya tafi Dubai sai bayan wata biyu kuma" Yusuf ya ce "Ayyah, ya sameni a office jiya ai, so munyi sallama" ta ce "Haka yake cemin, shine nace ai yau bari nazo tinda kunki zuwa" cire hular kansa yayi ya ce "Zamuzo Ammi, Jiddah taje gida za tayi kwana biyu" Ammi ta ce "To Allah ya dawo da ita lafiya, na zata ai tana ciki ta ki fitowa ne" ya dan zaro ido yana murmushi ya ce "Never, ai ba zata jiki tayi shiru ba" Ammi ta ce "Hakan kake gani" daga haka ta kalli Khairiyya ta ce "To idan kin gama ciye~ciyen ki tashi mu tafi, dan idan magrib yayi driving wahala yake min" Yusuf ya ce "Har yanzu Ammi" ta ce "Har gobe kuwa Yusuf bana samun nutsuwa" daga haka ta mike, tashi Rafi'ah tayi ta ce "Mungode Ammi" Ammi ta ce "Ba komai, sai kunzo din" Khairiyya ta kama hannun Rafi'ah ta ce "Anty sai na zo hutun" Rafi'ah ta ce "Sai kinzo" Hijab dinta ta dauka akan kujera ta saka sannan tabi bayansu, har mota suka rakasu, Yusuf nata murmushi har suka tafi, juyowa yayi zai koma cikin gida suka hada ido, sai da kirjinta ya buga tayi saurin dauke kanta, ita tama manta raban da yayi mata murmushi ko magana, kusan sati uku da kwanaki kenan, sai daya shige ya rufo kofa sannan ta shiga itama. Da dare Yusuf na kwance a parlor ta fito sanye da Hijab ta zauna gefensa, a hankali ta ce "Doctor" ya bude idanuwansa yana kallanta, ta ce "Gobe zanje follow up clinic, maganina ya kusan karewa" sauke idansa yayi a kanta ya ce "Wa zai kaiki?" Sai yau ya mata magana bayan sati uku da suka wuce, ta kauda kanta gefe hawaye taap idanta ta ce "Cab" maida kansa yayi gefe ya limshe ido, ta tashi ta koma daki tana goge hawayen idanta, dama tasan yanzu duk duniya ba wanda ya tsaneta kamar Yusuf, babu abinda yake 6ata mata rai irin rashin magana da yake mata, fashewa tayi da kuka ta jawo wayarta akan drawer zata kira Mummy, kawai kuma ta fasa ta gefar da wayar a kasa, kuka sosai take tana kiran sunan Abbanta, da tasan haka rayuwar aure yake da tin tini bata yarda da Yusuf tayi aure ba, gaba daya yanzu ta tsani kanta da komai nata, cikin kuka ta ce "Nina jawowa kaina, Ummi dan Allah ki yafemin, bansan haka zai faru dani ba, i'm tired with this misrable life na gama gajiya" shiru ta danyi jin an bude kofar dakin, ta dago kanta a hankali ganin wanda zai shigo.