Sashe 21
Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
_Two weeks ltr_ Ummi ce Zaune a kitchen tana hada coleslaw cikin bowl Abdul na 6are maggi a gefenta, bayan ya gama ya mika mata ta ce "Keep it there" a kan drawer ya ajiye ya dawo gefenta ya zauna, dai dai lokacin Rafi'ah ta shigo kitchen din, ta dan tsaya bakin door ganin sun gama aikin da suke, karasawa ciki tayi tana kallan Ummi ta ce "Wai meyasa bazata sauka anan ba Ummi?" Ummi ta ce "Da gidanta dan meyasa zata sauka a gidanku" Ta dan turo baki ta ce "To nidai caan zan tafi" a takaice Ummi ta ce "Abba yace babu me zuwa, tinda zasu kai karfe 12 kafin suyi landing, kuma itama cewa tayi ku zauna gobe da safe zata zo" Rafi'ah dake kallan Ummi ta ce "Har sai gobe zamu ganta" Ummi ta dalla mata harara ta ce "Keep shut quite now, ke bakisan tara ki nake bako Rafi'ah? tinda muka fara aikin nan kika tafi kika kata waya baki dawo ba sai yanzu, kinzo kuma kin isheni da surutu, better mind ur words, bari kuma Abba ya dawo ki masa bayanin da uban wa kike waya da bazaki gayamin ba" a hankali ta sunkuyar da kanta ta ce "Kiyi hakuri" Ummi bata ko kalleta ba taci gaba da abinda take. Bayan ta gama ta hada komai cikin basket ta bawa Mustapha ya kai gidan Mummy da yake akwai mai aikinta a gidan. Ganin ba kaisu caan gidan za'ai ba yasa Rafi'ah tayi sallan ishanta ta shiga daki ta kwanta, harta fara bacci phone dinta ya fara ringing, ta dauka a hankali ta kara a kunne hade da sallama, Yusuf ya dan zaro ido jin muryarta ya ce "Are u sleeping Baby?" Ta dan turo baki ta ce "I'm tired that's why" ya ce "Sorry, kinyi wa Mummy abinci ne?" Ta danyi murmushi ta ce "Sure" ya ce "Ohk let me leave u rest" ta ce "Uhm, till tomorrow" ya ce "Byee" tana hanging wayar ta kasheta duka duka ta koma baccinta. Washegari tinda Rafi'ah tayi sallan asuba tayi wanka, bayan ta shirya tayi dialing number Mummy, bata dauka ba har kiran ya katse. Karfe 7:30 Mummy ta iso gidan, Abdul ya mike jin horn ya leka ta window, dan murmushi yayi yana kallan Ummi ya ce "It's Mummy" daga haka ya bude kofar ya fita da sauri, rungumeta yayi yana ta bubbuga bayanta looking happy ya ce "You are welcome mother" Mummy ta kama hannunsa ta ce "How are u, ya sai tsayi kake?" Abdul ya danyi dariya yana kallan saurayin dake tsaye jikin motarsa ya ce "Ina kwana?" Cike da fara'a ya ce "Lafiya kalau and u?" Abdul ya ce "Also fine", Mummy ta juyo tana kallansa ta ce "U come in Jawad" daga haka suka nufi entrance din gidan tana rike da hannun Abdul, Suna shiga ciki Ummi ta rungumeta ta ce "Sannu da zuwa Anty, ya hanya?" Mummy ta ce "Alhamdulilah, ya muka sameku?" Ummi dake murmushi ta ce "Lafiyar kowa kalau" sai lokacin Jawad ya tsuguna bakin kofa ya ce "Ina kwana" Ummi ta ce "Lafiya kalau, Jawad, kaine yau a gidanmu" ya danyi murmushi yana shafa kanshi, Mummy ta ce "Ai ba zaman kasar yake ba, shima day before yesterday ya dawo daga Ukraine" Ummi ta ce "Ayya, kayi masters kenan" ya daga mata kai yana murmushi, Mummy ta ce "Yanzu zai ci gaba da aiki ba" Ummi ta ce "Masha Allah that was great, yasu Mamanku?" Yayi kasa da kansa ya ce "Suna nan, gobe zasu wuce Abuja" yana rife bakinsa Rafi'ah ta sauko a guje ta rungume Mummy kam kam, Mummy ta shafa bayanta ta ce "How are u daughter?" A hankali ta dago kanta ta ce "Fine Mummy, ya hanya?" Mummy ta ce "Masha Allah" daga haka ta kara rungume Mummy tana murmushi, Ummi ta mike tana kallan Jawad ta ce "Ka zauna kan sofa mana" Rafi'ah ta dago kanta jin an kira Jawad, suna hada ido ta dauke kanta tana kallan Mummy ta ce "Abbana ma ya kusan dawowa, saura kwana uku" Mummy ta ce "Munyi waya ai jiya, ga Jawad baku gaisa ba" Rafi'ah ta dan turo baki ta ce "Shida bayawa mutane magana, in munje sai yayi ta hade rai da fishi" Mummy ta dan zaro ido ta ce "Wai hakane Jawad?" Shidai baice komai ba yayi murmushi yaci gaba da danna phone dinsa. Breakfast Ummi ta jera musu akan dinning ta ce "Anty Halima ga abinci, Jawad u come forward". mikewa Mummy tayi ta koma dinning ta zauna, Rafi'ah ta dawo gefenta ta ce "Let me serve u Mummy" daga haka ta dauka plate ta fara zuba mata abinci, few minutes Mummy ta gama breakfast dinta, ta mike tana kallan Jawad dake danna waya har lokacin ta ce "Bismillah Jawad" ya tashi a hankali ya ce "To" Mummy ta wuce upstair tana fadin "Ina Zainab din take ne". Jawad na zama akan dinning ya kalli Rafi'ah dake cin chips and egg ya ce "Can't u great?" Ta dan 6ata fuska ta ce "Bayan baka ma mutane magana a gidanku" ya ce "To ai yanzu gidanku nazo" a hankali ta ce "Morning" ya ce "How are u?" Ta ce "Fine", kusan minti 10 basu kara cewa komai ba, Jawad ya ajiye cup din tea yana kallanta ya ce "Ya jinki kuma?" With surprise ta dago tana kallansa, taya yasan bata da lpy to? Jin tayi shiru yasa ya ce "Allah ya kara sauki", suddenly phone dinta dake gefensu ya fara ringing, Jawad ya kalli screen din sannan ya kalleta, daukan phone din tayi ta wuce kitchen, bayan tayi picking tayi sallama, Yusuf ya ce "How are u Baby? I just saw ur text now" ta danyi murmushi ta ce "Yanzu ka tashi kenan?" Ya ce "Of course, fatan sun iso lpy?" Ta ce "Ehh Alhamdulilah" limshe idanuwansa yayi murya caan kasa ya ce "I want to see u Baby" ta sunkuyar da kanta tana murmushi ta ce "Ohk, anjima zanbi Mummy gidanta sai kazo caan" cike da farinciki ya ce "Woow thank u luv, mezan kawo maki?" Ta saki murmushi ta ce "Nothing" ya ce "No say something pls" a hankali ta ce "Khairiyya" ya dan zaro ido ya ce "Ba yanzu ba, but i promise she would come one day" turo baki ta danyi ta ce "Pls Doctor, inasan na ganta ne?" Ya ce "I promise u zan kawota watarana kinji Baby" ta ce "To" ya ce "Hope you're not angry" ta kara sakin murmushi ta ce "No" ya ce "Alright by what time zanje caan din" ta dan juya idanta kamar yana gabanta ta ce "I think after Asr" ya ce "Ohk, which area?" ta fada masa sunan anguwan da kuma house number, Yusuf ya ce "Understood, thank u so much love" rife fuskarta tayi da tafin hannunta ta ce "Sai anjima" ya ce "Bye" daga haka yayi hanging wayar, tashi yayi ya janye duvet din jikinsa ya tsaya gaban mirror, farar riga ce a jikinsa sai tree quarter ash colour, comb yasa ya taje gasjin kansa sannan ya dauki laptop dinsa ya fito a dakin, Da sauri ya tsaya ganin Umma a parlor da Anty Khadija suna ta daddaga kayan da umma ta siyo na lefe, Yusuf ya dauke kansa ya ce "Ina kwana Umma" cike da fara'a ta ce "Lafiya Yusuf, kaga dai kayan dana fara siyowa" ba tare daya kalli kayan ba ya ce "Sunyi kyau" Umma ta taso da wani tsadadden lace a hannunta ta ce "Kaga wannan ai yayi kyau ko Yusuf, ko kuma kafisan red color?" A hankali ya ce "It's ok" Umma ta koma ta zauna ta ce "Atoh, jidda fara ce idan aka tara mata jaa ai ba kyau zatai ba" shidai bai ce komai ba ya wuce kitchen ya hada tea sannan ya fito ya koma daki, Anty Khadija ta kalli Umma dake jera kayan cikin akwati ta ce "Umma wai fara'ar me kike tayi ne?" Umma tayi murmushi ta ce "Khadija kenan, ke bakisan idan ana son buri ya cika sai an saki fuska ba, kema dai ki lalla6ashi ku shirya, hanya daya kenan da jidda zata samu ta shiga gidansa ba wata caan daban ba" Anty Khadija ta dan ta6e baki ta ce "Ai wallahi bai isa ya auri wata caan daban ba, kisha wahalar rainonsa sannan yaje ya auri wata ta moresa" Umma ta ce "Kema dai kya fada, gara ya auri za6ina ta yadda zata bini sau da kafa mu mallakeshi" murmushi Anty Khadija tayi ta mike tana kashewa Umma ido daya ta nufi dakinsa. Mummy ce zaune a dakin Ummi suna hira, Ummi ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Amma tin daga ranar bai kara tashi ba" Mummy ta ce "Allah ya kara mata lpy" Ummi ta mike ta ce "Yanzu kenan Maman Jawad Abuja zasu koma?" Mummy ta ce "Haka ta tsara masa wai zasuje hutun sati biyu kafin a koma school" Ummi ta ce "Allah ya kyauta, ya kannen Jawad din?" Ta ce "Duk suna nan, sai shegen taurin kai da rashin kunya irinna uwarsu, nidai bana shiga harkarsu dan kakkarya yara ba abu me wahala bane a wajena, Jawad ne kawai me hankali a cikinsu, Sadeeq kam ba'a magana, ita kuma wancen sa'ar Rafi'an rashin kunyarta yafi karfinta, ana gobe zamu dawo ma sai da uban yayi mata dukan tsiya" Ummi dake saurarenta ta ce "Allah ya shirya mana" Mummy ta ce "Ameen" daga haka suka hau hirarsu ta yaya da kanwa. Karfe uku Mummy tace wa Rafi'ah ta shirya zasu tafi, ta dauka handbag me dan girma tasa kayanta kala hudu aciki, Ummi dake kallanta ta ce "Kwana nawa zakiyi ne?" Ta ce "Sunday zan dawo da daddare, kwana 2 kenan" Ummi ta ce "Ki fadawa Abba dama, and make sure u don't forget ur drugs" ta ce "To", bayan ta gama shirya kayanta ta kira Abba ta fada masa, ya mata Allah ya kiyaye, har bakin mota Ummi ta rakasu, Mustapha ya bude motar Rafi'ah ta shiga, suna tsaye bakin motar Anty Amina ta shigo gidan, ta kauda kanta gefe tayi apartment dinta, Mummy ta bita da kallo ta ce "Ita dan kiban ma da matan manya suke ita batayi, daga ina