Sashe 18
Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Washegari da sassafe Ummi ta tashi ta fara hadawa Abba breakfast, tana cikin aiki taji an danna bell, ta wanke hannunta a sink sannan ta fito a kitchen ta bude kofar parlorn, Abba ya saki murmushi yana kallanta ya ce "Ina Mamana, hope ta hadamin breakfast" Ummi ta bashi hanya ya shigo ta ce "Indai Mamankan nan ne ai sai dai ka tafi da yunwa" Abba ya zauna kan sofa ya ce "Baki tasheta ba kawai Madam" Ummi ta danyi murmushi ta ce "Morning" ya ce "Morning, ya kwanan yaran?" Ta ce "Kowa lpy, karfe nawa zaku tashi?" Abba ya ce "By 9, baki gama bane?" Ta ce "Saura kadan" daga haka ta koma kitchen ta dauko flask din shayi ta ajiye masa akan dinning. Ba jimawa ta kammala duk wani abinda yake da bukata ta jera masa sannan ta wuce upstairs, a parlor ta sami Rafi"ah na kwance akan kujera tayi rub da ciki, Ummi ta ta6a jikinta to make sure she's fine, tashi tayi ta zauna tana goge idanta silently ta ce "Ina kwana" Ummi ta ce "Lafiya, ki tashi kije Abba yana kasa" mikewa tayi a hankali ta wuce downstairs still tana goge siraran hawayen dake zubo mata time by time, Abba kadai ta samu zaune a kan dinning yana cin abinci, ya miko mata hannunsa na hagu ya ce "Come on Mamana" Rafi'ah ta saka hannunta daya cikin nasa ta karasa gefensa, har lokacin bata yarda sun hada ido ba, Abba ya zaunarta gefensa ya ce "How was your night?" silently ta ce "Fine, Abba tafiya zaka yi?" Ta karashe maganar tana san yin kuka, Abba ya shafa kanta ya ce "I'm sorry daughter, very soon zan dawo kinji, kinga tin last two week ya kamata na koma to ban samu ba saboda kinyi rashin lafiya, i hope u are not crying" ta sauke kanta kasa tana tare hawayen idanta, Abba ya share mata idanta tass, bayan haka ya tura plate din abincin gabanta ya ce "Let's eat together" daga haka ta dauka fork ta faracin abinci. Suna cikin ci Abdul ya fito daga dakinshi, manyan kayane ajikinshi da sukai mataukar kar6enshi, yaja kujera ya zauna yana kallan Abba ya ce "Morning" Abba ya ce "How are u?" A hankali ya ce "Fine" daga haka shima ya dauka plate ya fara serving kansa, sai kallan Rafi'ah yake yana dariya kasa~kasa, bayan ya fara cin abincin ya ce "Ina kwana Anty" Bata amsa shi ba saima harara data dalla masa, Abba ya danyi murmyshi ya ce "Can't u respond? Haba Mamana" mayar da kanta tayi gefe ta ce "Abba dariya fa yake min" Abba ya ce "To Abdul ka daina mata dariya, maza amsa masa gaisuwar da yayi" calmly ta ce "I'm fine" Abdul yayi dariya zaiyi magana Abba ya masa alamar yayi shiru, daga haka ya mike ya ce "Let me see ur Mum upstairs". A daki Abba ya samu Ummi tana waya da Anty Halima, ganinsa yasa ta ce "Zan kiraki anjima" daga haka tayi hanging wayar tana kallansa ta ce "Har kun gama?" Abba ya zauna gefenta ya ce "Ehh, na miki transfer ko kin gani" ta ce "Ehh na gani just few minutes from now, Allah ya kara budi ya kuma kiyaye hanya" Abba ya ce "Ameen, idan akwai wani abu u let me know" ta girgiza kai ta ce "Ba komai yanzu kam" ya ce "Alright, Amina na nan itama, nace mata ta jira next idan na dawo sai mu koma" Ummi ta ce "To" ya mike yana kallan agogon dakin ya ce "Yaran nan idan sun dawo a islamiyya akai su gidan Umma su gaisheta, naso muje but Allah baiyi ba" Ummi ta ce "To insha Allah" Abba ya mike ya ce "I think i have to go Ummu Rafi'ah" Ummi ta daukar masa karamar traveling bag dinsa ta ce "Allah ya sauke ku lpy", suna saukowa Abdul ya kar6i jakar a hannun Ummi sannan ya fita da ita zuwa mota, Rafi'ah ta mike ta ce "Allah ya kiyaye Abba" ya ce "Ameen Mamana, hope ba zaki kuka ba?" Ta daga masa kai ta ce "Ehh Abba" daga haka ya kama hannunta, Ummi dake kallansu ta ta6e ta ce "Safe flight" ya ce "Ameen, Ameen" daga haka suka fita Ummi ta dawo ciki. har bakin mota Rafi'ah ta rakashi tana ta mishi bye bye, Abdul ya leka motar yana kallan Abba ya ce "Allah ya kiyaye Abba" Abba ya ce "Ameen, ayi ta kokari ayi ta karatu, Allah kuma ya muku albarka" a hankali Rafi'ah ta amsa da Ameen sannan ta rife masa kofar mota, hannu suka dinga daga masa har Mustapha ya fita da motar. Rafi'ah na komawa parlor ta turo baki ta zauna gefen Ummi ta ce "Abba ya tafi" Ummi ta ce "Da kin bishi ai, ki tashi ku fara shirin islamiyya" Rafi'ah ta ce "Ummi ya Abba bai tafi da Anty Amina ba" Ummi ta ce "You can call him and ask" ta kara turo baki ta ce "Ni wallahi banaso ta zauna damu, gara ta tafi caan gidan Umma" Ummi ta ta6e baki ta ce "Sai ki koreta ai idan zamanki take" Rafi'ah ta kwanta ta ce "Sai tai ta yima mutane kallan banza" cikin tsawa Ummi ta ce "Cewa nayi ki tashi kiyi shirin islamiyya ko?" ta mike da sauri ta wuce upstair. Da yake atampa ne ajikinta zulelen himar dinta kawai ta saka ta shafa power da lipstick, tayi kyau sosai da sosai, daga haka ta dauka side bag dinta me dauke da Qur'an da sauran littafai sannan ta dauka phone dinta ta jefa a ciki, tana saukowa ta samu Abdul gefen Ummi yana rokonta ta bashi mota, Ummi ta mike ta ce "Idan baza ku hau keke Napeep ba kar kuje islamiyyan" Abdul ya ce "Ba ina fita dake ba, dan Allah ki bani" ta ce "Dani kace ai Babana, amma bazan baka mota daga kai sai Rafi'ah ba" daga haka ta ajiye musu 1k ta ce "Gashi idan kuna da niyya" Rafi'ah ta dauka kudin ta nufi kofa ta ce "Malam ka taso mu tafi" daga haka ta fice yabi bayanta yana gyara hulan kansa, Anty Amina ce zaune gefen Ummanta tana sauraren abinda suke fada, bayan ta dasa aya Anty Rahama ta mike tana tafa hannu ta ce "Wallahi Umma bata isa ba, ninasan shiga tayi ta fita tasa yace bazai tafi da Amina ba" Umma dake zaune kan kujera ta ce "Ai kuwa kanta tayi wa, dan wallahi yanzu zata san ba'a ta6amin 'ya'yana a zauna lafiya" Anty Amina ta share hawayen idanta ta ce "Abin haushinma Umma saida na shirya kawai jiya da daddare yake cemin na zauna saiya kuma dawowa, kuma Umma nasan matarsa ce silan komai, ni kuwa ban masa girki ba wallahi" Umma tayi wani shu'umin murmushi ta ce "Nace miki kanta tayiw Amina, zata gane ba'a ta6a min zuri'a a kwana lafiya" Anty Rahama dake huci ta ce "Idan batai wasa ba saina 6atar da 'ya'yan da take takama dasu, idan yaso ta mutu kowa ma ya huta, da kyar idan tafiya aikin da take ba bin maza take ba" Anty Amina ta kwantar da kanta a cikinyar Umma ta ce "Dama mana, bakiga sai kudi take samu ba, banda haka ya za'ai ace kwanan nan ta canza mota sannan ba'a fi wata hudu ba har ta siyar ta sayi wata" Anty Rahama ta ce "Uhmm kinji ko Umma, idan ba maza take bi ba nawa ake bawa malaman jami'a da har take tara kudi haka" tashi Umma tayi ta bar musu parlor saboda phone dinta dake ringing a cikin daki. A hankali ya bude kofar dakinsa ya fito, kananun kaya ne a jikinsa sunyi masifar yi masa kyau, gashin kansa sai sheki yake, Umma ce kadai a parlon tana zaune, ta dago kanta ta kalleshi sannan ta dauke kai ta wani hade rai, Yusuf ya zauna a kan kujerar dake opposite dinta ya ce "Ina kwana" kamar ba zata amsa ba sai kuma ta ce "Lafiya" daga haka ya mike ya nufi kofa zai fita ta ce "Ka dawo ka zauna" dawowa yayi ya zauna ya zuba mata ido yana jira ta fadi abinda zata ce, kusan minti 3 yana zaune bata ce komai ba ya danyi kasa da kansa ya ce "Umma ina jinki" ta dora kafarta daya akan daya kafin ta ce "Banga ka turo kudin dana ce maka ba" ya sunkuyar da kansa ya ce "Ehh ban manta ba, akwai gyaran da zanyi a gidana wannan month din, sai dai ko next month na tura miki" Umma ta ce "To baka isa ba, saika bar gyaran gidan idan ka gama hadawa Jiddah lefe sai kayi" Yusuf ya sauke ajiyar zuciya ya ce "To, nawa zan tura miki yanzu" ta ce "300k, sai na fara dasu kafin wani watan" dago kansa yayi yana kallanta with disturb, Umma ta ce "Ko baza kai ba nasan abin yi" a hankali ya ce "Zanyi" daga haka ya mike ta ce "Ina kuma zaka naga yau Sunday" ya ce "Zanje gidan Mubarak ne, matanshi ta haihu yesterday night" Umma ta ta6e baki ta ce "Haka dai, yawan banzan baya karewa" shikam tin tini ya fita a parlon dan dama bai tsaya jin me zata ce ba, yana isa parking lot ya shiga motarsa ya kifa kansa akan kujera, kusan minti 10 yana haka kafin ya mike ya sawa motar ya fice a gidan. Duk yadda Rafi'ah zatai saida tasan yadda tayi ta bada haddanta da wuri, karfe 11 da minti 10 kiran Yusuf ya shigo wayarta, ta dauka a hankali tayi sallama ya ce "I'm outside" daga haka tayi hanging wayar ta mike ta dauka jakarta, durkusawa tayi gefen malaminsu ta ce "Ya Sayyadi Yayan nawa ya zo" ya dago yana kallanta ya ce "Allah ya kiyaye" ta ce "Ameen" daga haka ta mike ta fita a class din. Tin da ta fito Yusuf yake kallanta harta tsallako titi ta karaso inda yake tsaye, yayi folding hannayensa yana murmushi ya ce "Ashe zaki iya fitowa" ta danyi murmushi kanta a kasa ta ce "Good morning" ya ce "Morning, how was ur night?" Silently ta ce "It was fine" ya bude mata back seat ya ce "You