← Book details Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 42 OF 59

Sashe 42

Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 9 min read

_08103810398_
[7/31, 10:43 AM] My Imaan: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_34_

Shiru Abi yayi bayan Jawad ya fita, he can't believe this is what Jawad is seeking for, in dai kuwa hakan ya tabbata zaifi kowa farinciki, tashi yayi yana kallan clock din dake jikin wall sannan ya wuce dakinsa. Jawad bai tsaya ko ina ba sai gidan Kawu, bayan ya shiga gidan parlorn Kawu ya fara shiga ya gaishe shi sannan ya wuce dakin Mama, suna zaune ita da Mami bayan sun gama breakfast suna dan hira, Jawad na shigowa Mami ta hade rai kai kace ba ita ke hira tana dariya ba, a hankali ya zauna a kan carpet yana kallan Mama ya ce "Ina kwana" ta ce "Lafiya kalau Ahmad, ya mutanen gidan?" Ya ce "Kowa lafiya" daga haka ya dan kalli Mami ya ce "Good morning mother" ciki ciki ta ce "I'm fine" ya ce "Masha Allah" Mikewa yayi Mama ta kalleshi kafin ta ce "Bari Muhibba ta kawo maka breakfast" dan shafa kansa yayi yaja baya ya ce "Nayi breakfast Mama, zan wuce kawai" ta ce "To Allah ya kiyaye" daga haka ya kalli Mami ya ce "Sai anjima" bata amsa shi ba saima harara data bishi dashi harya fita a dakin, Mama ta ce "Bafa hake ake yiwa d'a ba Hadiza, jaan sa zakiyi a jiki amma ba ki dinga masa fada haka ba, yanzu fisabilillahi Jawad me shekara 36 dinne zaki zauna kina masa fada kamar Ikram" Mami ta ta6e baki tana kallan Mama ta ce "Kinga shi Jawad idan damuwa ya shiga bazai ta6a fada min ba, sai yayi ta shiru shiru ke kyace na Allah ne, wani lokaci sai ya gayawa matar ubansa abu ni bai fadamin ba" Mama ta ce "The best solution kawai yayi aure" Mami ta dan zaro ido ta ce "Aini bana tinanin yana hira ma wannan yaran, tinda nake da Jawad bai ta6a kawomin wata yace ta gaisheni ba, ke ko a waya ne, kinga kuwa ai watakila an sa mana hannu, amma idan ba haka ba yaro shekara 36 ace har yanzu shiru, ba aiki ya rasa ba, ga gidansa nan a gine sai aikin yin gyara ba mata a ciki, aini lamarin Ahmad yan firgitani Anty Fatima" shiru Mama tayi tana kallan Mami, caan ta danyi murmushi ta ce "Idan kin koma gida sai muyi magana" Mami ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Toh". Cikin shirinta na islamiyya ta fito tana kallan Abdul dake kwance saman kujera yana bacci, dogon hijabi ne har kasa a jikinta sai nikab a hannunta, jin footsteps yasa ta juya da sauri, juyowa tayi ta kara kallan Abdul dake kwance ta ce "Ummi why is he still sleeping?" ta kamo hannunsa taji da zafi, Ummi ta ce "Bashi da lafiya, ki tafi kawai" duk jikinta sai yayi sanyi, ta durkusa tana kallan fuskar lovely brother dinta, saam itama bataso taga bashi da lafiya, Ummi dake kallan idanta daya kowo ruwa ta ce "Don't cry here Rafi'ah, ki tashi ki wuce Islamiyya" a hankali ta dafa goshinsa ta ce "Ummi what's wrong with him, ba'a je clinic ba kuma" Ummi ta kamo hannunta tana murmushi ta ce "Stop crying daughter, insha Allah he will recover soon, munje clinic kina bacci" Rafi'ah ta share dan guntun tears dinta ta ce "Zazza6i yake yi Ummi?" Ta ce "Ehh, amma da sauki kinga yayi bacci ma yanzu" a hankali ta mike tana turo baki ta ce "Kuma baki tasheni naje ba" Ummi ta ce "To kiyi hkr, yanzu dai ki tafi karki makara" calmly ta ce "To" daga haka ta dauka jakarta akan sofa ta fita zuwa parking lot.
Sai karfe 12 Jiddah ta farka daga baccin daya dauke ta, ta dinga bude ido a hankali harta ware su duka, bata ga kowa cikin dakin ba sai dai kuma taji karar ruwa a toilet, ta mike a hankali ta zauna tana tino incident din jiya, limshe idanuwanta tayi tana jin kaunar Yusuf har cikin ranta, tana nan zaune harya fito a toilet da towel daure a waist dinsa, Jiddah tayi saurin komawa ta kwanta ganin sun hada ido, gently ya karasa kan gadon yana shafa fuskarta ya ce "How are u Jiddan Yaya?" Boye fuskarta tayi a kirjinshi tayi shiru, ya bata light kiss a forehead dinta ya ce "Thank u wife, you make me feel comfortable yesterday night" sai a lokacin ta dan dago kanta tana kallan fuskarsa ta ce "Kafa jikani da ruwan jikinka Yaya" rungumeta yayi ya dinga shafa mata sauran ruwa dake hannunsa, ta danyi murmushi ta ce "Zan rama ai" hancinta yaja yana smiling ya ce "Zamuyi dambe kuwa" ta danyi dariya ta ce "I know how to deal with u" matsowa jikinta yayi ya kai bakinshi dai dai kunnenta ya ce "And u cried yesterday night, why didn't u deal with me" boye fuskarta tayi a jikinshi tana dariya kasa kasa, ya dagata yana kallan fuskarta ya ce "Go and bath" sauka tayi akan gadon ya dinga kallanta harta shige toilet, bin bayanta yayi ya bude toilet din yana kallan yadda ta yamutse fuska ya ce "What's that" a hankali ta ce "Yaya my lap" ya kamo hannunta ya ce "Sorry dear, bari na hada maki ruwan zafi" daga haka ya hada mata just like he did before, bayan ya gama ya juyo yana kallanta ya ce "Ai kinga yadda mukai dazu, so u do exactly, kar kuma ruwan yayi sanyi" ta ce "To" daga haka yaja mata toilet din, few minutes ya shirya cikin kananun kaya ya dauki key din mota, yana shirin fita ta fito a toilet, kallansa ta tsaya yi kafin ta ce "Where are u going?" Ya ce "I want to get us something for breakfast" daga haka ya fice a dakin tabi shi da kallo, haka kawai kuma ta tsargu dashi, gani take kamar wajen Rafi'ah zaije, duk jikinta babu kwari ta shirya, tana shiryawa ta koma kan gadon ta kwanta, phone dinta taji yana ringing a kan stool, ta mika hannunta ta dauka sannan tayi answering call din, Anty Khadija ta ce "Ke bazaki kira mutane ki musu ya gajiyar biki bane? Tin da asuba nake kiran wayarki baki dauka ba" Jiddah ta kumburo fuska ta ce "Ban tashi bane lokacin" Anty Khadija taja tsaki ta ce "To sai ki tashi yanzu, anjima zanzo" ciki ciki ta amsa sannan tayi hanging call din, bayan nan ta kira layin mahaifiyarta, tana dagawa ta fashe da kuka ta ce "Anty kinji wai Anty Khadija zata zo min gida, dan meyasa bazasu barni na huta ba, kwana na daya fa" Mahaifiyarta da suke kira da Anty ta danyi murmushi ta ce "Yi shiru Auta, kyaleta tazo, watarana da kanta zata dauke kafafuwanta a gidanki, yanzu aka fara" Jiddah ta share hawayen idanta ta ce "Shi kuma kinga ya fice ya barni, kuma nasan watakila wajen yarinyar nan zaije" Anty ta ce "To yaje mana, nace miki yanzu aka fara wasan" Jiddah tayi shiru tana jin zuciyarta na zafi, Anty ta tausasa murya cikin rarrashi ta ce "Haba Auta, kiyi hakuri na dan lokaci ne, yanzu ki koma kiyi baccinki, kima saki jikinki gida naki ne miji naki ne" murmushi ta danyi ta ce "Toh Anty nah" daga haka sukai sallama. Duk yadda taso ta koma bacci kasawa tayi, bayan minti 30 Yusuf ya shigo rike da ledan take away, bata amsa sallamar da yayi ba saima juya kai da tayi, ya shigo dakin yana murmushi ya ce "Na siyo miki favorite dinki love" juya kai gefe tayi ta danja tsaki, ya ce "What? Na miki laifi ne?" Kin kulashi tayi ta mike ta dauka wayarta zata fita falo ya jawo hannunta ta fado jikinshi ya ce "who are u hissing" kallansa ta dinga yi kafin ta kara hade rai ta ce "Sai kaje ka rungume ita wacce kaje wajenta" da mamaki yake kallanta jin abinda tace, ya ce "Ko kin fara hauka ne Jiddah? What are u saying?" zame jikinta tayi a fusace ta ce "Abinda kaji shina fada, kuma ni ba hauka nake ba tinda banyi abinda za'a kirani da mahaukaciya ba, kaida kaje wajen wata da auranka ai kai ya kamata a kira da wannan sunan" daga hannunsa yayi zai wanka mata mari sai kuma ya sauke kasa ya zauna bakin gado, ficewa tayi a dakin hade da jan tsaki ya bita da kallo, bayan few minutes ya fara karanto Al~qur'an kasa kasa saboda ya samu saukin abinda yake ji.
Bayan mintina kalilan ya mike ya fita parlor, zaune ya sameta a kan kujera tana kallo, ya zauna gefenta ya ce "What comes over u Jiddah? u just change all of a sudden" a hankali ta juyo tana kallansa sai kuma ta ce "Kaje wajen yarinyar ai nasani" ya kamo hannunta ya ce "What is ur evidence? Ina san ganinta kam banyi karya ba, but ai yanzu lokacinki ne, i can't leave u at this condition" harara ta balla masa ta zame hannunta cikin nasa, tana juya kanta ta fara hawaye, ya rungumeta ta baya ya ce "Sorry if i hurt u" juyo da ita yayi yana kallan fuskarta camly ya ce "This is our first day as couples Jiddah, pls don't let shaidan deceive u" a hankali ta kwantar da kanta akan kafadarsa tana sheshekar kuka, ya dinsha shafa bayanta yana rarrashinta, ita a duniya yanzu babu wadanda takejin haushinsu irin su Anty Khadija, idan ta tuna kullukan maganin da suka bata sai taji zuciyarta na zafi, itama yanzu dama ce ta samu kuma dole tayi amfani dashi, babu abinda zaisa ta yarda su shanye Yusuf ita ta tashi a babu, kara shigewa jikinsa tayi tana limshe ido, ya dan bubbuga bayanta ya ce "Are u not hungry?" ta girgiza masa kai, dago da kanta yayi yana kallan idanta ya ce "Why? Tin jiya bakici komai ba" ta sauke kanta a kirjinshi ta ce "I will eat ltr" ya kara dago kanta ya jawota jikinshi sosai ya ce "Then we will eat together ko?" Daga masa kai tayi, ya kai bakinsa kan nata ya fara bata hot and romantic kiss...
Horn Abi yayi Mustapha ya bude gate yana daga masa hannu, bayan ya shigo yayi parking sannan ya fito, da ladabi Mustapha ya gaisheshi sannan ya tambayi Abba, Mustapha ya ce "Bari a masa magana" daga haka ya nufi apartment din Anty Amina, ba jimawa Abba ya fito sukai musabaha, yana ta murmushi ya ce "U are welcome Honorable, bismillah ka shigo" daga haka suka nufi BQ, a parlor suka zauna sannan suka kara gaisawa, Abba ya ce "Bari a kawo maka abin sha" Abi ya ce "Alhamdulilah Engineer, ba dadewa zanyi ba i have an important meeting" Abba ya ce "Ohk ba damuwa, dama 'yan siyasa are always on meeting" Abi ya danyi murmushi ya ce "Dama wata magana ce ta kawoni, and i wish u will be happy with it" Abba ya ce "I hope so Honorable" Abi ya gyara babban rigarsa ya ce "Dama yau da safe d'an wajena Ahmad yazo min da magana ta cewa yana son 'yarka da aure, so shiyasa naga nazo na fara maka magana kafin komai" still Abba yayi yana kallan Abi with shock jin abinda yace, ya danyi murmushi ya ce "That is not a problem Honarable...
Chapter 42 · 0% Book details