← Book details Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 54 OF 59

Sashe 54

Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Shiru Yusuf yayi ya ci gaba da driving dinsa, bayan few minutes ta dan kalleshi sannan ta ce "I'm sorry if i hurt u" still baice komai ba, sai bayan minti uku ya ce "Not at all, i don't feel like talking anymore" jinginar da kanta tayi jikin kujera ta limshe ido, har sukaje gida babu wanda ya kara magana a cikinsu, a kofar gida yayi parking yana kallanta ya ce "Come down" ta ce "Why not kayi parking a ciki to?" Ya girgiza mata kai kawai, ta ce "But Abba zaiyi magana yana nan fa" ba tare daya kalleta ba ya danna horn, bayan Mustapha ya bude gate din ya shigar da motar sannan yayi parking. Fitowa tayi tana kallansa ta ce "Bari na fadawa Ummi tare muke" ya girgiza mata kai, kamo hannunsa tayi cike da damuwa ta ce "My Doctor is anything wrong with u? Kona maka laifi ban sani ba" limshe idanuwansa yayi ya ce "Uhm~uhm, baki min komai ba, kawai naji banasan magana ne, may be..." Shiru yayi ya bude idanuwansa yana kallanta, ta kai hannunta face dinsa ta ce "May be what?" ya girgiza kai ya ce "I'm having Headache kuma haushi nakeji" murmushi tayi ta rungumeshi ta ce "Allah ya baka lafiya" a hankali ya ce "Ameen" tana dago kanta ta hango Anty Amina da Anty Khadija suna tahowa, sai shewa suke suna tafawa, yadda take kallansa shima Yusuf haka yake kallansu, har suka karaso inda suke Rafi'ah na rike da hannun Yusuf dake zaune, ta dan sunkuyar da kanta ta ce "Ina kwanan ku" Anty Khadija ta washe baki tana kallanta ta ce "Amarya har kin fara fita ne?" Kafin tayi magana Anty Amina ta ce "Haba sati biyu fa, ai yaci ace tazo taga mutanen gida" Anty Khadija ta karasa wajen motar tana kallan Yusuf ta ce "Bashi da lafiya ne?" Rafi'ah da kanta ke kasa ta dan sake hannunsa ta ce "Ehh, kanshi ne yake ciwo" sai lokacin ya dago kansa yana kallansu ya ce "Good morning" a tare suka amsa gaisuwar, Anty Khadija ta ce "To Allah ya sauwake" daga haka suka nufi inda motarta take, murya caan ciki ta kalli Anty Amina ta ce "Kingani ko, alamu sun nuna abin ya fara aiki, aina fada miki daga yau komai zai dai dai ta" Anty Amina ta kamo hannunta ta ce "Gaskiya babu abinda zan iya saka miki dashi Khadija, Amma dama nayi alkawarin idan komai ya dai daita akwai filina da zan mallaka miki, nasan dai watakila kinfi karfinsa amma ai kyauta da dadi" Anty Khadija tayi murmushi tana kallanta ta ce "Gaskiya naji dadi sosai, yanzu dai ki koma komai ake ciki zan kira ki" Anty Amina ta daga mata hannu sannan ta koma apartment dinta ba tare data kalli inda su Rafi'a suke ba, dago kansa yayi ya ce "Move, zan rife kofar i'm going home" ta marairaice ta ce "Baza ka gaishe su ba?" Ya girgiza kai ya ce "Some other time, i can't stay here" matsawa tayi ya rufe kofarsa sannan ya tada motar yayi horn, juyawa tayi duk jikinta a sanyaye ta nufi apartment dinsu, tana hawa balcony ta juyo taga harya fita a gidan, bell ta danna sannan taja gefe ta tsaya, bayan minti 2 aka bude kofar, kallan budurwar data bude kofar tayi sannan ta shiga parlorn, Rafi'ah na murmushi ta rungume Umminta dake zaune akan kujera, Ummi ta shafa bayanta ta ce "How are u daughter?" a hankali ta dago tana kallan Ummi ta ce "I'm fine Ummi, ina Abba?" ta ce "He's upstairs" daga haka ta mike ta ce "Abdul fa?" Ummi ta ce "Yana dakinshi" upstairs ta wuce tana murmushi ta ce "Let me see Abba first" tana shiga dakinsa ta sameshi yana zaune akan stool, Abba yayi murmushi ganinta ya ce "Is this my Mum?" Itama murmushi tayi ta zauna a kan carpet ta ce "Ina kwana Abba" ya ce "Lafiya kalau Mamana how are u and everyone?" Ta ce "All fine Abba, tare muka zo amma kanshi na ciwo shine ya wuce gida" Abba ya ce "Subhanallah, i will call him ltr, Allah ya sauwake" ta ce "Ameen" mikewa tayi ta ce "A huta gajiya Abba" ya ce "Alright Mother" tana fitowa a dakin ta shiga dakinta, yana nan yadda ta barshi sai kamshi yake, ta kwanta akan gadon tana murmushi ta ce "I missed u bed" daga haka ta mike ta fita a dakin ta sauko kasa. Abdul na gefen Ummi yana taya ta arranging papers, ya dan zaro ido ya ce "Anty" ta rungumeshi ta ce "Ya kake, tashi min a gefen Ummina" dariya Abdul ya dinga yi yana kallanta ya ce "Ai ke mun kyautar dake, yanzu ni kadai ne ko Ummi?" ta shafa kansa ta ce "Exactly Babana, tashi dai ka bata wajen tinda ita bakuwa ce" turo baki Rafi'ah tayi jin ance mata bakuwa, Side hug Ummi ta mata ta ce "So ya kuke, i hope everything is going fine?" A hankali ta Jinginar da kanta ajikin mahaifiyarta ta ce "Lafiya kalau, amma ba shida lafiya ne" Ummi ta ce "Subhanallah, meya sameshi?" Cike da damuwa ta ce "Ciwan kaine, dama fa akan da yamma idan yazo daukana zamuje gidan Mummy" Ummi ta ce "Ki bari next time sai kije kawai" a hankali ta ce "Toh, mai aiki kika dauka Ummi?" Ta ce "Ehh, ko karna dauka" Rafi'ah tayi murmushi ta ce "A'a ai aiki zai maki yawa" Ummi tayi murmushi tana shafa kanta ta ce "I hope bakya saan jikin ki nan" ta ce "Noo, da sassafe nake komai Ummi" Ummi taja hancinta ta ce "Good kici gaba da haka kinji first born, watarana zaki ga amfaninsa" a hankali ta ce "Insha Allah" daga haka ta mike ta wuce kitchen. Da yamma Rafi'ah na zaune a dakinta duk ta shiga damuwa, ta kira Yusuf yafi a kirga amma ko daya baiyi picking ba, bude kofar dakin akai, tayi saurin juya kanta saboda idanta duk yayi jaa sakamakon kuka data yi, karasowa kusanta Ummi tayi ta ce "Idan bazaki tafi ba in kira Abbanki in fada masa, sau uku ina aiko Saudatu ta kira ki amma kinyi zamanki" mikewa tayi a hankali ba tare da kalli Ummi ba ta dauki Hijab har kasa cikin sauran kayanta sannan ta nufi hanyar fita, Ummi dake kallanta ta ce "Wait Fatima, wani abu na daminki ne?" A hankali ta girgiza kai, Ummi ta ce "Toh Allah ya kiyaye kije Mustapha ya kaiki, Abba kuma kya kirashi dan dawowarsa sai dare" slowly ta share hawayen daya sakko mata, ga zafin barin gida, ga damuwarta na halin da Yusuf yake ciki, gani take kamar yana nan kwance ba lafiya, cikin muryar kuka ta ce "Allah ya dawo dashi lafiya, na tafi" cike da tausayin Rafi'ah Ummi ta ce "Allah ya kiyaye" daga haka ta wuce dakinta. A hankli ta sauko a stairs din ta fita zuwa parking lot ta shiga mota, Mustapha yaja motar suka tafi, har sukaje gida ba tai magana ba, sai da yayi parking ta ce "Thank u" daga haka ta fito ta shige gate. Da sauri ta karasa entrance din gidan ta murda handle din kofar, still ta tsaya tana kallan Yusuf dake kwance yayi pillow da cinyar Jiddah, tayi saurin kauda kanta duk suka bita da kallo harta wuce part dinta, tana shiga ta turo kofar ta durkusa a wajen ta fara rera kuka, kusan awa daya tana zaune a bakin kofa kafin ta mike ta shige dakinta ta rufo kofa, tana nan zaune har akai magrib ta tashi tayi alwala tayi sallah har akai isha tana zaune akan sallayar, ta mike tayi isha sannan ta dauki towel ta shiga toilet tayi wanka, tana fitowa ta samu Yusuf a bakin gado yana zaune da laptop a gabansa, sauke kanta tayi ta nufi inda kayanta suke ta dauki night dress sannan ta koma toilet ta shirya, scarf ta saka bayan ta fito sannan ta karasa gefenshi ta zauna, a hankali ta ce "How are u now?" Ba tare daya kalleta ba ya ce "Better" tayi shiru tana kallansa, dago kansa yayi suka hada ido tayi saurin sauke kanta ta ce "Dan Allah kayi hakuri idan na maka laifi Doctor" girgiza kai ya danyi kafin ya ce "How many times zance miki bakimin laifi ba, ko kin daina fahimtar magana ne" hawaye ne tap a idanta jin yadda yayi maganar, cikin muryar kuka ta ce "U never shout at me, meyasa zakamin tsawa yau" hannunta ya kamo ta matso kusa dashi ya rungumeta very light, dan bai bari sun hada jiki sosai ba, ya ce "I'm sorry, i don't know what comes over me, haushin kowa nakeji yau, especially..." Shiru yayi yana rike da ita, ta dan sake shi tana kallansa ta ce "Ni ko?" Daga haka ta fashe da kuka, matsowa yayi ya kara rungumeta sosai ya ce "Bance ba, but haushi nakeji kawai" cikin kuka ta ce "Kayi addu'a mana" ya ce "Nayi" daga haka ya saketa ya kwanta akan gadon, share hawayen idanta takeyi tana kallansa ta ce "Or is it because nace matarka bata iya magana ba da safe?" Shi dai kallanta kawai yake, caan ya mike ya dauki pillow ya koma parlor ta bishi da kallo, duk yadda taso ta hakura karta bishi kasawa tayi, bayan 30 minutes ta leka parlorn ta sameshi saman kujera har yayi bacci, a nan wajen ta sulale ta fara kuka sosai. Washegari da sassafe ta tashi ta hada masa breakfast sannan tayi wanka, tana shigowa dakin ta sameshi ya shirya, ta danyi kasa da kanta ta ce "Good morning" kai kawai ya daga mata, daga haka ya dauki briefcase dinsa da statescope zai fita ta ce "Breakfast din yana kan dinning" ya girgiza kai sannan ya fita a dakin, bin bayansa tayi har suka fito main parlor, ya gama saka takalmi sannan ya dauki komai nasa zai fita ta ce "Doctor breakfast din fa" ba tare daya kalleta ba ya fice ya rufo kofar, Jiddah dake zaune akan dinning ta sheke da dariya, duk yadda Rafi'ah taso kar tayi kuka amma hakan bai yuwu ba, ta fashe da kuka ta koma part dinta, jikinta har rawa yake ta zube aKan gado tana
Chapter 54 · 0% Book details