← Book details Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 14 OF 59

Sashe 14

Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 6 min read

ma?" Yusuf yayi murmushi ya ce "Not interested, and self medication is not allowed" Dr ya ce "Kuma hakane, Allah ya sauwake, let me get the drugs for u, room dinta shine na kan corner, probably room 4" Yusuf ya ce "Ohk" daga haka yaci gaba da hada alluran. Ummi na fitowa a toilet ta kalli Rafi'ah data juya baya sannan ta dauki sallaya tayi hanyar fita, a hankali Rafi'ah ta ce "Ummi ina zakije" tsayawa Ummi tayi ta juyo tana kallanta ta ce "I want to pray outside Rafi'ah, ina nan corridor ko kinasan wani abu?" Girgiza kanta ta hauyi ta ce "No" daga haka ta limshe idanuwanta Ummi kuma ta fita. Yusuf na gama hada alluran ya fito a office din Dr. Aryan sannan ya nufi room din da Rafi'ah take, da sallama ya shiga room din ya karasa kan gadon, tana kwance ta juya bayanta idanta a limshe, ya karasa dab da ita ya leka fuskarta, zaro ido ya danyi yana kallanta surprisingly enough, jin kamar motsi a bayanta yasa ta bude idanuwanta ta juyo a hankali, ta zaro ido silently ta ce "who i'm i seeing?" Zama yayi a gefenta ya ce "How are u now?" Ta ce "Much better, how did u know i'm here?" Ya danyi murmushi ya ce "My heart told me u are here" ta saki murmushi me kyau ta ce"It's impossible" ya ce "Bakisan idan zuciya na san ganin abu tana searching ta gano in yake ba?" Ta danyi dariyar daya bayyana with teeth dinta kafin ta ce "So ita ta kawo ka kenan?" Ya ce "Sure! Yaushe kika samu attack" ta fara wasa da fingers dinta ta ce "Immediately i entered my house, so i slept to rest, kawai kuma sai na farajin somehow heartburn" Yusuf dake kallanta tin tini ya ce "Allah ya kara maki lpy, are u sure u are taking ur drugs?" Ta daga masa kai ta ce "Ina sha" daga haka ya mike ya ce "I'm giving u an injection now" ta dan matso bakin gadon ta mika masa hannunta, daga hannun rigar yayi yana kallanta ya ce"Kina tsoron Allaura ne?" Ta danyi smiling ta ce "Not that much, amma fa kar kamin da zafi" yana ta dariya ya goge wajen da spirit sannan ya caka alluran, ya dinga kallan fuskarta to see her reaction, sai ma yaga batai wani raki ba, cotton wool ya saka mata a wajen sannan ya ce "Sorry, insha Allah da safe zan shigo na gaisheki" ta ce "Ohk, thank u" ya daga mata hannu ya nufi hanyar fita, kafin ya bude kofar Ummi ta bude ta shigo, ya danyi kasa da kansa with full of respect ya ce "Ina yini Umma" Ummi ta ce "Lafiya kalau" daga haka ya fita a dakin ita kuma ta shigo tana kallan Rafi'ah da har ta sake kwanciya ta ce "Magani aka baki ne?" Ta girgiza kai ta ce "Injection" Ummi ta ce "Tashi kiyi sallah sai na hada maki tea ki sha" daga haka Ummi ta daga ta suka shiga toilet. Da sallama Abba ya shigo parlorn yana kallan Anty Amina dake zaune, ta amsa masa sallamar ranta babu dadi sannan ta ce "Inata kiran wayarka baka picking" Abba ya zauna yana kallanta ya ce "The phone isn't with me, Rafi'ah ba lafiya anyi admitting dinta dazu, so gobe da safe kije ki duba ta" ta dan hade rai ta ce "Zanje gida fa, banje na gaishe da Umma ba, kuma dama akwai abinda tamin inaso kaja mata kunne" Abba ya dago yana kallanta ya ce "But nace maki tana asibiti ko? And goben make sure kinyi branching kin gaisheta" bata ce komai ba ta wuce kitchen ta dauko masa ruwa da cup ta ajiye a gabansa sannan ta koma daki ya bita da kallo ganin fuskarta kamar an kunna wuta. Washegari wajajen karfe goma Anty Amina tazo asibiti, duk ranta a 6ace yake dama ba dan Abba ba da ba zuwa za tayi ba, a hankali ta bude kofar ta shiga ko sallama babu, kan kujera ta zauna tana kallan Ummi ciki ciki ta ce "Ina kwana" Ummi dake hadawa Rafi'ah tea ta ce "Lafiya" Anty Amina ta ce "Ya mai jiki" Ummi ta ce "She's getting better", bude kofar toilet Rafi'ah tayi ta fito, towel kadai ne a jikinta ta karaso ta zauna akan gado tana turo baki, ganin hararan da Ummi ke mata yasa ta danyi kasa da murya ta ce "Good morning" Anty Amina ta mike tana kallan Ummi ta ce "Sai anjima" daga haka ta bude kofar ta fita. Verseline Rafi'ah ta shafa sannan tasa riga da wando ta koma kan gadon ta kwanta, tinaninta Ummi zatai mata fada amma kuma sai taga akasin haka, Ummi ta mika mata tiree me dauke da tea sai bread da chips a gefe ta ce "Tashi kici abinci" Mikewa Rafi'ah tayi ta kar6a tiree din sannan ta faracin abincin, few minutes ta gama ci ta ajiye sannan ta goge hannunta da tissue ta kwanta, waya Ummi ta mika mata ta ce "Ga Anty Halima, jiya ta kira kinyi bacci" kar6an wayar tayi ta kara a kunne ta ce "Mummy" from the orther side Mummy ta ce "Daughter how are u?" a hankali ta ce "Da sauki sosai" Mummy ta ce "To adai dinga kiyayewa, ni dama hankalina bai kwanta ba da kikace zaki raka waccen matar shopping, wallahi badan kar Muhammad yace ina shiga hurumin gidansa ba da babu inda zaki, muka sani ma ko ita ta jawo miki ciwan ya tashi" dariya Rafi'ah tayi ta ce "Sai bayan fa mun dawo Mummy" taja tsaki ta ce "Ke dai kibar mace Rafi'ah, mata akan kishi babu abinda basayi, bari dai na dawo kasar fuskarki ma ba zata gani ba" Rafi'ah ta ce "To Allah ya kaimu" ta ce "Ameen" daga haka ta mikawa Ummi wayar. Bude kofar dakin akayi Yusuf ya shigo da sallama, Ummi ta amsa tana kallansa, ya karaso ciki ya dan tsuguna ya ce "Ina kwana Umma" ta ce "Lafiya kalau" ya ce "Ya mai jiki?" Ta ce "Da sauki, sai godiya" daga haka ya ajiye babban bakin ledan dake hannunsa ya dan kalli Rafi'ah data takure waje daya ya ce "How are u feeling?" A hankali ta sunkuyar da kanta ta ce "Da sauki" daga haka Yusuf ya juya ya ce "Allah ya sauwake, sai anjima" Ummi ta ce "To mungode Allah ya saka" daga haka ya fita ya rife kofar. Ummi ta kalli Rafi'ah ta ce "Who is he?" Dago kanta tayi ta ce "Doctor ne, shine ai wanda yamin injection jiya da daddare" Ummi bata sake cewa komai ba ta nemi waje ta zauna, Gwalalo ido Anty Khadija tayi ta ce "Yusuf nake gani a nan? Naga jiya yace yazo ya kar6i magani, in fact ai ba nan ake zuwa ba" ta wuce Nurse din da suke magana tare tabi bayan Yusuf, cikin few minutes ta karaso shi ta ce "Malam meya kawoka nan? Meyasa bakaje aiki ba?" Yusuf ya juyo yana kallanta ya ce "Nazo na duba abokina ne baiji dadi ba" Anty Khadija ta ce "To bari naje na ganshi, kaga ai zaiji dadi" daga haka ta nufi room din da Rafi'ah take, cikin sauri ya tare ta ya ce "Aiba dole saikin je ba, baima sanki bafa" Anty Khadija ta tsaya tana kallansa, ta karasa bakin kofar da sauri tasa hannunta akan handle din kofar zata bude Yusuf yayi saurin janye hannunta ya ce "Why won't u mind ur own business? Nace maki baima sanki ba".
Chapter 14 · 0% Book details