← Book details Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 36 OF 59

Sashe 36

Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Fifteen minutes ya kai Yusuf gida daga unguwar Rimi, bayan yayi parking ya fito rike da phone dinsa ya rife motar, yana juyawa suka hada ido da Jiddah dake tsaye tana sakar masa murmushi, tayi bala'in yin kyau sai kyalli take, a hankali ya zura hannunsa cikin pocket dinsa ya fara takawa gently har zuwa inda take tsaye, yayi kasa da murya ya ce "U look so cute Jiddah tah" ta kara sakar masa murmushi ta ce "Thank u Yayana, muje ciki kaga abinda na dafa maka" ya danyi murmushi yabi bayanta suka shiga parlorn, ba kowa a ciki sai TV dake ta aiki, ta zauna akan dinning tana kallansa ta ce "Here it is Yaya" ya bude karamar warmer yana kallan vegetable soup din data ji kayan hadi da nama, ya bude dayan yaga tuwon shinkafa, surprisingly ya juyo yana kallanta ya ce "So u have time to prepare this kike barina da yunwa Jiddah?" Ta farfara masa ido ta ce "Ai lokacin ina school ne yanzu kuma nayi hutu" daga haka ta mike ta fara serving dinsa, Yusuf ya dan shafa kansa yana kallanta ya ce "Hope haka zakina min a gidana?" Ta juyo tana kallansa sai kuma tayi murmushi ta ce "Accepted" hannunsa ya wanke ya fara cin tuwan yana kallanta, bayan few minutes ya kara kallanta yaga kallansa take, ya danyi murmushi ya ce "Naje wajen kanwarki yau, and u know what?" Nan da nan ta hade rai ta juya kanta gefe, ya ce "Ya akayi Jiddan Yaya?" Ta kara hade rai ta ce "Ni banasan zancen yarinyar" Yusuf ya wara ido yana kallanta ya ce "Really?" Ta daga masa kai, ya ce "To ai watarana tare zamu zauna, dan banda ra'ayin raba muku gida, kinga tun wuri gara ku saba, Fatima bata da matsala, she's kind and nice to stay with" Yana rufe bakinsa taja wani dogon tsaki, ya juyo yana kallanta ya ce "Why the hiss Jiddah?" A fusace ta ce "Then what's my business with her? nina ce banasan kana min maganarta akwai abinda na hada da ita ne" Yusuf ya wanke hannunsa ya dauki phone dinsa dake kan dinning ya ce "Ai kuwa ke kika hada abu da ita, tinda very soon zaku mallaki miji daya" mikewa tayi kamar zata tashi sama ta bar wajen ya bita da kallo. Kwana uku da faruwan haka Yusuf ya kira Abba ya sanar masa maganar auransa da Jiddah, bayan sun gama waya Abba ya sanarwa Ummi, ta nuna 6acin ranta karara a fili saboda bata ta6a tinanin haka ba, fitowa tayi a dakin Abba duk jikinta a mace ta wuce dakinta, Abdul na zaune yana kallo a laptop dinta, ta rife laptop din ya dago yana kallanta ya ce "Nayi sallah fa Ummi" zama tayi bakin gado ta ce "Kiramin Rafi'ah, kai kuma ka wuce" a hankali yace to sannan ya fita a dakin ya rufo mata kofa, fitowanta a wanka kenan tana goge jikinta Abdul ya shigo, ya tsaya bakin kofa ya ce "Anty, Ummi na kiranki" daga haka ya fice a dakin, cikin sauri ta shafa body lotion ta shirya cikin doguwar riga na atampa sannan ta daura dankwalinta ta fita zuwa dakin Umminsu, gently ta tura kofar ta shiga da sallama, Ummi dake zaune ta ce "Come here" sai da kirjinta ya buga ganin yanayin mahaifiyarta, a tsorace ta karasa ta zauna a kan carpet ta ce "I'm here" Ummi ta juyo tana kallanta ta ce "Da gaske ne Yusuf aure zaiyi?" Rafi'ah ta daga mata kai, Ummi ta ce "And that's what u choose for yourself?" Kanta ta sauke kasa bata ce komai ba, Ummi ta ce "Well, kiyi duk abinda kika ga ya dace Rafi'ah, har nawa kike da zaki auri me mata? Don't u see ur mates? Kowa kokari yake idan ya gama secondary school ya samu admission yaci gaba da karatu but ke aure kika sa a gaba" kanta na kasa duk tana sauraron mahaifiyarta, Ummi ta ta6e baki ta ce "Ya miki kyau, idan kinga haka kikeso fine, nidai addu'a shine nawa, kuma duk abinda ya faru dake mine is to say sorry" a hankali ta dago tana kallan Ummi ta ce "I'm sorry" Ummi ta ce "Noo u haven't wronged me Rafi'ah, ina jiye miki gaba ne, shi aure nutsuwa yake bukata da kwanciyar hankali, nasan kuma indai zakije gidan wata to dole ne zakiyi facing challenges, u are too young for that Rafi'ah, bazaki hakura dashi ba idan kika gama Allah ya kawo miki wani kiyi auranki" sai a sannan ta juyo dai dai saitin Ummi ta ce "Dan Allah Ummi kiyita min addu'a, i don't know what is coming over me, ina sanshi Ummi, kuma ita sun dade tare dashi, na miki alkawarin bazan ta6a neman fadan taba idan har Allah yayi shina aura, i promise u this Ummina, addu'ar ki kawai nake bukata" ajiyar zuciya Ummi ta sauke ta ce "Tooo, Allah ya za6a miki duk abinda yafi alkhairi" a hankali ta ce "Ameen" sannan ta mike ta fita Ummi ta bita da kallo. Shirye~ shirye sosai Umma take na bikin Jiddah, gidansu ma kansa saida aka masa paint from head to toe. Almost everyday Jawad ya kanje ya gaishe da Ummi, wani lokaci ya kawo Mummy su yini, duk da ba'a gida yake kwana ba duk safiya saiya biya ya gaishe da Mummy da Abi kafin ya wuce wajen aiki, ta bangaren Yusuf kuwa tinda ya gama gyaran gidansa Umma ta sa shi a gaba, yau tace ya kawo dubu dari, gobe tace ya kawo dubu hamsin, haka dai kullum, ko kadan kuma baya nuna gajiyawarsa akan hakan, duk abinda suka tambaya ya kam basu, sosai da sosai kuma yake kula da Rafi'ah, baya kwana biyu baije sun gaisa ba, waya kuwa kullum cikin yinta suke hakan kuma na kona raan Jiddah ba kadan ba, idan tayi magana sai yace ai ita kullum suna tare, a haka har biki saura sati daya, a ranar ne kuma Mamin Jawad ta dawo daga Abuja saboda Ikram zata koma school. Zaune take a gaban mirror tana waya aka bude kofar, tayi still tana kallan wanda zai shigo, ganin Ameera yasa ta sauke ajiyar zuciya dan a tinaninta Ummice, da yanzu ta hau fada, Ameera ta tsaya gabanta ta ce "Matar Doctor Yusuf" Rafi'ah ta danyi murmushi tayi hanging wayar ta ce "Matarsa na gidansu ai" Ameera ta ce "Kema very soon zaki zama ai" Rafi'ah ta sake murmushi ta ce "Daga ina kike" Ameera ta ce "Jiya bakije islamiyya ba, shiyasa nazo naga ko lafiya, kuma dazu nayi ta kiran wayanki baki dauka ba" Rafi'ah ta ce "Ohh, wayan na silent ne, kinsan Doctor used to called much, kuma Ummi fada take tayi wai ina waya da yawa, nikam kawai sai nasa a silent idan ya kira nayi ta wayana, yanzu ma akan idan na gama zan kiraki ne" Ameera ta ta6e baki ta ce "To aikuwa kamar a bakin Ummi" Rafi'ah nata dariya ta ce "Kamar da gaske". Hira sosai sukayi kafin Rafi'ah ta rakata har bakin layi sannan ta dawo gida, tana dawowa ta samu Ummi a parlor ta dawo a aiki, ta zauna tana kallanta ta ce "Sannu da dawowa" Ummi ta ce "Sannu, Anty Halima nata kiranki wai baki dauka ba why?" Rafi'ah ta duba phone dinta aikwa taga 6 missed call dinta, ta ce "I don't know she called" Ummi ta ce "Tinda yau saturday ki shirya Mustapha ya kaiki, batajin dadi ki tayata zama, gobe saiki dawo" dan zaro ido tayi ta ce "Meya sameta?" Ummi ta ce "Zazza6i take, yanzu nayi branching na duba ta" sama Rafi'ah ta wuce ta samu handbag din Ummi me dan girma ta saka kayanta da drugs dinta a ciki sannan ta canza hijabi ta sauko tana kallan Ummi ta ce "To zan tafi sai da safe" Ummi ta ce "Safe, zan kira Abba na fada masa" daga haka ta fita zuwa parking lot. Mustapha na zaune a balcony din Anty Amina yana kallan idan film a wayarsa, dama nan yake zama indai tana Abuja, Rafi'ah ta karaso kusanshi ta ce "Zaka kaini gidan Mummy yanzu fa" ya mike yana nade tabamarsa ya ce "To Hajiya karama, wallahi wani film nake kalla, yarinyar cikin film din kamar ke, har kama kuke Hajiya" Rafi'ah ta dan juya ido ta ce "Taya za'ai ina Nigeria kace ina kama da Indians" ya ce "Allah kuwa Hajiya, hancinku ma iri daya ne" Rafi'ah ta danyi murmushi ta ce "To zan hadaka da Doctor kuwa" Mustapha ya washe baki yana dariya ya ce "Allah sarki, ai jiya ma daya zo kafin ki fito hira muka sha, ya bani dubu uku, gaskiya kinyi sa'a Hajiya karama, akwaishi da kyauta, gashi fari kaal dan gaye, amma dai bafulatani ne ko?" Rafi'ah na shiga mota ta ce "Sai dai ka tambayeshi idan yazo" Mustapha ya ce "Ai mutumina ne bari ya sake zuwa, anya ba tattarawa zanyi idan anyi aure ba in koma gidanki" Rafi'ah ta ce "Zakawa Abba butulci kenan?" Ya saki murmushi yana jaan motar ya ce "Ai Abba ubane Hajiya karama, tinda nake ban ta6a ganin mutum me fahimta irin Alhaji ba, Allah ya biya shi da gidan Aljannah" a hankali ta ce "Ameen" sannan tayi picking call din Yusuf. Few minutes ya kaisu gidan Mummy, bayan yayi parking ta masa sallama sannan ta tura gate din gidan ta shiga, a hankali ta sauke kanta ganin Jawad na zaune akan farar kujera dake kan balcony, sai da ta iso dai dai saitinsa ta ce "Ina yini?" Ya ce "Lafiya kalau" daga haka ta shige ciki, Mami na zaune a parlorn da wata kawarta Hajiya Kareema, Rafi'ah ta dan rusuna ta gaishesu, Hajiya kareema ta amsa tana kallanta harta shige part din Mummy, a hankali ta zaro ido ta ce "Wannan yarinyar fa?" Mami ta ta6e baki ta ce "Diyar kanwarta ce, ni wallahi baso ma nake tana zuwamin gida ba, ciwan zuciya ne fa da ita" Hajiya Kareema ta zaro ido ta ce "Ciwan zuciya kuma? 'yar yarinyar nan dako 18 inaga bata cika ba" Mami ta ce "Atooh, ni dai cewa nayi ma ko HIV ne da ita suke boyewa, kiganta fa a bushe sai farar fata,
Chapter 36 · 0% Book details