Sashe 52
Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 4 min read
ai jiya" ta kara turo baki ta nufi kofa ya bita da kallo yana murmushi, baisan meyasa idan yana tare da ita baya gajiya da kallan abubuwanta ba, key din mota ya dauka ya fita, a parlor ya sameta tsaye tana jiranshi, tayi saurin kama hannunsa ta ce "Harda yawo ma zamuje ko Doctor" ya ce "Eh" rungumeshi tayi tana murmushi ta ce "When are we coming back?" Ya ce "Till night" ta danyi tsalle ta ce "Yess" daga haka suka fita zuwa parking lot Jiddah ta bisu da harara. Sai lokacin Anty Khadija ta koma gida, bayan tayi parking ta shiga parlor da sallama, Umma dake kallanta ta ce "Sai yanzu" ta ce "Ehh na biya clinic ne" Umma ta ce "To ya kukai?" Anty Khadija ta ajiye veil dinta akan kujera ta ce "Kamar dai yadda Malam ya fada hakan take, suma inaga da abinda suka kulla a kasa, shine ya hadu da wanda muke ya kasa bada result me kyau, gaskiya Umma sun mungun tsanar yarinyar" Umma ta danyi murmushi ta ce "Barka, kinga yanzu haduwarmu dasu, zasu bar komai a hannunmu, sai muyi yadda mukaga dama" Anty Khadija ta ce "Hakane, kuma Umma baza suyi tinanin sake wani abun ba, balle su toshe mana hanyar namu aikin" Umma ta danyi dariya ta ce "Dama Malam yace min bamu kadai bane" daga haka Anty Khadija ta mike ta haura upstairs. Yau ya kama sati 2 da bikin Rafi'ah, tin sassafe ta tashi ta shirya saboda Yusuf ya mata alkawari zai kaita gida yau, sosai tayi kyau ta yafa veil dinta akai, gefenshi ta koma ta zauna ta ce "Doctor" ya dauke kansa akan laptop ya juyo yana kallanta, ta ce "Pls na kwana mana kaji" dan zaro ido yayi ya ce "I can't sleep here without u, sai dai idan zaki bari jibi kwanan Jiddah sai kije ki kwana" kwantar da kanta tayi akan kafardarsa ta ce "Banaso" ya ce "To ba kwana, da daddare zan dauko ki" a hankali ta ce "Na yarda to, kuma sannan ni..." Shiru tayi ta fasa cewa komai, ya bata side hug ya ce "Now tell me, me zaki ce?" A hankali ta ce "Matarka ta daina shiga harkana tinda bataso mu zauna lafiya, kagani dazu na jona ruwa a kettle shine ta juyemin, hakama jiya ta daukemin Apple dina akan dinning kuma nayi magana tace wai in kwata idan zan iya" shiru yayi yana kallan lips dinta dake motsi, ta kai hannunta kan botton din rigarsa ta ce "Kuma Ummina tace karna sake nayi fada da ita, so kace itama ta daina min haka" bakinshi ya ajiye akan nata ya ce "Ai jiya na mata fada sosai, bazata kara ba" ta ce "To ai yau..." Shiru tayi jin bakinshi cikin nata, tayi saurin janye fuskarta ta matsa a gefensa ta ce "Ba yanzu zamu tafi ba" jinginar da kansa yayi akan gado ya limshe ido, kamar zatai kuka ta ce "Karfe 9 fa yanzu Doctor" bude idanuwansa yayi ya kamo hannunta ta dawo kusa dashi ya ce "Zanyi missing dinki Baby, i so much luv u, banasan naji bakya jikina" daga haka ya rungumeta tsam tsam a jikinshi, cikin rarrashi ta ce "I will miss u too, but ni kam ka tashi mu tafi" ya danyi murmushi ya ce "Tona tashi" ta kama hannunsa ta ce "Let's go" kashe laptop din yayi ya dauki phone dinsa da key din mota sannan suka fita. Jiddah na zaune a parlornsa tana shan tea, ya ce "Zan kaita gida na dawo" ta juya musu keya bata ce komai ba, har zasu fita ta ce "To meye damuwana da sai ka gayamin, aikin banza kawai" Rafi'ah ta juyo da sauri jin abinda ta fada, sai kuma tayi shiru, Yusuf ya bude kofar suka fita, yana jiwo tsakin da tai amma baice mata komai ba, har sukaje parking lot baiyi magana ba, bayan sun shiga ya tada motar Rafi'ah ta kamo hannunsa ta ce "Dan Allah ka daina fishi Doctor, i apologize on behalf of her" juyowa yayi yana murmushi yaja hancinta ya ce "I'm not angry dear" ta ce "But you're not smiling" ya ce "Ai nayi" ta ce "Ai saida nayi magana" shiru yayi ya danna horn gateman ya bude sannan suka fita, bayan sun hau titi ta dan kalleshi ta ce "I'm soryy to say ur wife doesn't have manners of talking".