← Book details Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 47 OF 59

Sashe 47

Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Zaune take akan sallaya tana addu'a misalin karfe 10 na safe, juyawa tayi jin ringing din wayarta, ta dago wayar tana murmushi ganin Yusuf ne, a hankali tayi picking call din ta kai kunne hade da sallama, on the orther hand Yusuf ya ce "How are u Baby?" A hankali ta ce "I'm fine" ya ce "I saw ur make~up yesterday, kinyi kyau sosai, i hope yau kifi jiya kyau" a hankali ta danyi murmushi ta ce "Insha Allah" ya ce "Zanzo na kawo miki kayanki anjima" ta gyara zamanta ta ce "I'm not at home" da mamaki ya ce "Kina ina?" ta ce "Gidansu friend dina Ameera, bayan layin mu ne" ajiyar zuciya ya sauke har sai data jiyoshi, ya danyi shiru sai kuma ya ce "Caan gidansu zanzo kenan?" Ta ce "Ehh, ina ga" ya ce "Alright, u send me the address, take care" ta ce "Ohk bye" hanging call din tayi taci gaba da addu'a, bayan ta gama ta mike akan carpet ta dan limshe ido dan bacci takeji bana wasa ba, daren jiya batai baccin kirki ba tai ta sallah tana addu'a hopping for the best marriage in her life. Jiddah ce zaune a parlornta tana share hawaye, tinda taji Yusuf yana waya kuka ya dinga cinta, bata samu sauki ba saida tayi kukan, tana nan zaune ya fito daga daki, ta gefen ido ta dan kalleshi, sai da kirjinta ya buga ganin kyan da yayi, sai sheki yake kamar shima am masa dilka lol, ya sha farar shadda da babbar riga sai ya fito as the groom he is, banda kamshi babu abinda yake, bude warmers din kan dinning yayi yaga babu komai, ya juyo ya kalleta tayi saurin dauke kanta, yana murmushi ya karasa gefenta ya bata side hug ya ce "Why the mood first wife?" fashewa tayi da kuka ta ce "Aure zakiyi ka kyaleni ko Yaya?, dan Allah ka fasa auran nan Allah zan iya mutuwa" limshe idanuwansa yayi jin yadda tayi collapsing a jikinshi, ya dinga shafa bayanta cikin rarrashi ya ce "I told u everything yesterday night Jiddah, alkawari nayi zan zauna daku biyun har karshen rayuwana, all i want is peace, ba aure zanyi dan hankalina ya tashi ba, and ba wai zanyi aure bane saboda bana sanki ba, ina sanki babu abinda kika gaza yimin a zamana dake, duk da ma satin nan kaff da yunwa kike barina amma dai na yafe miki" kara fashewa da kuka tayi ta ce "Bayan yarinyar rainin yawo ne da ita, gata karama amma sai rashin kunya, wallahi idan ta shigo gidana she will regret" ta karashe maganar tana share hawaye, rungumeta yayi tsam tsam cikin lallami ya ce "Amma ai tin farko na riga na gaya miki tare zaku zauna, sannan jiya da aka zo jere u did wrong, kin 6atamin rai kawai banyi magana bane saboda banasan hayaniya, ya za'ai ki rife kofar parlor bayan kinsan ta nan zasu shigo?" Rife idanuwanta tayi ta ce "To meyasa baka mata nata kofan ba?" Strictly ya ce "That's my wish, ba gidana bane? don't make me angry now, kuma yau kam kije gida, da daddare idan an kawo amarya u can come back, idan kinga dama ki kwana in kina so" kara fashewa tayi da kuka ta ce "Ni bazanyi attending auranka ba wallahi, bazanje gidan ba, sai dai na tafi gidan Anty na" zameta yayi a jikinsa ya ce "I don't permit u, idan baza kije gidanmu ba u can stay at home" daga haka ya dauki key din mota da kayan Rafi'ah a leda ya fita a parlorn, yana fita ta rushe da kuka ta durkusa akan carpet tana ta shiga 3. Umma ce zaune a gaban Malaminta sai zufa take, ya juyo kwaryar dake cike da ruwa yana nuna mata ya ce "Da karfe nawa ne auran?" Cikin rawar jiki ta ce "Yau Juma'a da karfe 2 idan an idar da sallah" girgiza kansa yayi yana kurawa ruwan ido ya ce "Ba lallai a daura auran ba" Umma ta share zufa tana kallansa ta ce "Alhamdulilah" da sauri ya dago ya kalleta ta ce "Allah gafarta Malam" ya juya jajayen idanuwansa ya ce "Mutanenmu na bukatar wata gudumawar Hajiya, saboda aiki sabo zasu yi" cikin sauri Umma ta ciro dubu 50 ta ajiye masa a gabansa ta ce "Indai aiki zaiyi ko nawa ne zan bayar Allah gafarta Malam" yayi wata kalar dariya ya ce "An gama Hajiya, sai dai ki zuba ido" mikewa Umma tayi tana murmushi ta ce "A huta gajiya" daga haka ta debi takalmanta a hannu ta fita a dakin. Anty Amina ce zaune a dakinta ta buga uban tagumi, duk jikinta yayi sanyi ganin awanni ya rage a daura aure , gashi so take ta tono abin tagani yana nan din amma gidan cike yake da jama'a ta ko'ina, duk ta rasa inda zata sa ranta gashi Anty Rahama ta koma gidan kawarta wai sai an fasa auran zata dawo tayi dariya, bude kofar dakin d akai yasa ta dago kanta, Ikleemah ta karaso dakin da kumburarrun idanuwanta da sukai jaa, zama tayi a gefen gado tana kallan Anty Amina ta ce "Saura awa 3 fa Anty, kunce min dani za'a daura amma har yanzu banji ana ango yace bayayi ba" fashewa tayi da kuka tana kallan Anty Amina. Ajiyar zuciya ta sauke ta kamo hannayenta ta ce "Kiyi hakuri mu zuba ido mu gani, ai yadda kika sha dilka da gyaran jiki dole ke zaki shiga gidan Yusuf, kima daina daga hankalinki muna nan zakiji komai anjima" cikin kuka ta ce "Fatana kenan Anty, dan idan na rasa Yusuf mutuwa zanyi Anty Amina, sai dai Ammina ta dauki gawana ko ku... " rife bakinta Anty Amina tayi ta ce "Kina hauka ne Ikleemah, menene na zancen daukan gawa kuma" share hawayenta tayi ta jingina kanta akan gado tana kuka kasa~kasa. Simple make~up Rafi'ah tayi ta saka atampa Ameera tayi mata daurin, sosai tayi kyau, sai kamshi take duk inda ta gifta, Ameera dake kallanta ta ce "Anya Doctor zai bari ki dawo gida Fatima? Masha Allah kin yi kyau" 'yar harara ta 6alla mata ta ce "Ina dai Babanku baya kasa?" Ameera dake dariya ta ce "Jiya fa nace miki yayi tafiya, amma anjima zai dawo, dan yace min zai iya samun daurin auranki" ta dauka veil dinta ta yafa ta ce "Ameera kaina ciwo yake" dafa goshinta tayi ta ce "To bakya bacci Fatima, taya baza kiyi ciwan kai ba" a hankali ta dan limshe ido ta ce "To ya zanyi Ameera, dole ne nayi addu'a sosai na roki Allah yasa a gama bikin nan lafiya, gaba daya na gaji so nake a gama kowa ya huta" Ameera ta danyi murmushi ta ce "Dama haka hidima yake ai, insha Allah lafiya kowa zai koma gida" a hankali ta ce "Ameen" tana rife bakinta phone dinta ya hau ringing, ta bude idanuwanta dake limshe tayi picking call din, Yusuf ya ce "I'm outside" ta ce "To" daga haka tayi hanging wayar tana kallan Ameera dake gaban mirror ta ce "Bari naje Khadija, su Maryam Sa'eed basu zo ba har yanzu" Ameera ta juyo tana kallanta ta ce "Soon zasu zo, dazu da kina bacci munyi waya, wai tailor ne bai karasa musu dinkin ankon ba" Rafi'ah ta ce "Alright, sai na dawo" Ameera ta ce "Ki gaishe sa" da toh ta amsa sannan ta fita a dakin, kannan Ameera ne kawai a parlor suna kallan power rangers samurai, ta danyi murmushi ganin yadda suke gaisheta ta ce "How are u people?" Suka ce "Fine" daga haka ta fita, tsaye suke shida Aliyu a jikin motarsa, ya dinga kallanta harta karaso inda suke, ta dan kalli Aliyu ta ce "Ina yini?" Ya ce "Lafiya kalau Amaryar mu, ya hidima?" Ta ce "Alhamdulilah" Yusuf ya gyara zaman hularsa yana murmushi ya ce "Ina yini Baby" rife idanuwanta tayi da veil dinta, ya ce "Kinyi kyau Allah, i feel like stealing you and run" harara Aliyu ya 6alla masa ya ce "Doctor ka daukeni karshen layin nan idan ka gama, zan shiga wajen Mukhtar" Yusuf ya ce "Ba damuwa" daga haka Aliyu ya kalli Rafi'ah ya ce "Amaryarmu sai anjima ko" ta ce "To nagode". Bude back seat Yusuf yayi ya ce "Pls enter Baby" ta sauke kanta kasa sannan ta shiga motar, zagayawa yayi shima ya shiga back seat yana kallanta ya rife kofar, ya jawo ledan kayanta ya ce "Ya miki kyau?" Ya zaro rigar yana warewa a hankali, ta dinga kallan hadaddiyar gown din ta ce "Yayi kyau sosai, thank u" ya ce "Mention not, meyake damunki?" tayi saurin sauke kanta kasa ta ce "Me kaga?" Maida rigar yayi cikin ledarta ya ce "Your eyes, bakya bacci ko?" Ta girgiza masa kai a hankali, kamo hannunta yayi murya caan kasa ya ce "Pls tell me dear" silently ta ce "I'm just having headache" Yusuf ya dinga kallanta with lots of disturb ya ce "Have u take any medicine?" Ta girgiza masa kai kanta na kasa, limshe ido yayi yana matsa hannunsa cikin nata jiin zafin jikinta, iya hannunta daya rike kawai yaji jikinta da zafi, dago kanta yayi yaga idanta tap da hawaye, ya kai hannunsa face dinta zai tare tayi saurin janye fuskarta ta ce "I'm not crying" ya ce "You are" ta ce "Kawai ina tinanin Ummina ne idan na tafi" jinginar da kansa yayi ajikin kujera yana kallanta, ji yayi kamar ya jawota jikinshi ya rarrasheta, ya sake hannunta ya ce "Are u taking ur drugs?" Ta ce "Ehh, dazu ma nasha" ya ce "Abinci fa?" Ta ce "Naci" ya ce "Allah ya kara miki lafiya, but don't stress yourself pls, u know ur condition more than anyone else, nasan dole zakiyi kewar Ummi but do a little Baby, kar ki bari ki samu attack today pls" tana ta jujjuya yatsunta ta ce "To" ya danyi murmushi yana kallan Henna hannunta ya ce "It's looks beautiful" ita dai bata bari sun sake hada ido ba, ya ce "Waya maki?" Ta ce "Wata ce" ya ce "Ohk, anjima da dare zan gani sosai da sosai" turo baki tayi ta kara sauke kanta, ya ce "Take ur clothe, Allah ya sauwake, but
Chapter 47 · 0% Book details