← Book details Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 31 OF 59

Sashe 31

Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 5 min read

a hankali ya ce "Ameen" yana rife bakinsa phone dinsa ya hau ringing ya dan juya ya kalla screen din, ganin Mami ke kira yasa wayar a silent yaci gaba da driving dinsa. 'Yar karamar yatsarta ta mika masa ta ce "then let's bet" Yusuf dake dariya ya ce "You will soon get used to the idea... So i won't bet on it" Rafi'ah ta danyi dariya ta ce "Kaji tsoro" shima dariyar yake ya ce "No, i'm not scared, but u know what?" tayi saurin girgiza masa kai, ya ce "When ever i marry you, you will stop wearing veil" ta dan zaro ido ta ce "Why Doctor" ya ce "U look more beautiful in hijab" rife fuskarta tayi da gyalen rigarta ta ce "Kaima ai manyan kaya yafi maka kyau" ya ce "To ai jiya nasa" ta ce "Yeah, nima kuma nasa Hijab" ya ce "Keda baki tsaya mun gaisa ba, kishi ya rufe maki ido" harara ta dan masa ta ce "I don't want" yana dariya ya ce "Ur wish is my command Hajiyata, is Abba at home?" Ta juyo tana kallanshi ta ce "Me zaka mishi?" Ya ce "Zance asa ranar auranmu ne" dan zaro ido tayi sai kuma ta ce "This is impossible" ya zura hannunsa a pocket dinshi yana kallanta ya ce "Fatima Abbanki mutumin kirkine, after Abbana he's the second person i can trust, he's a nice person i ever seen, he welcomed me happily, ya saurari bayanai na from d beginning till end and kinsan abinda yafi birgeni dashi?" Girgiza kanta tayi tana murmushi, Yusuf ya ce "He promised that..." Shiru yayi ganin mota tayi parking a gefensu, ya dan kalli Rafi'ah da itama motar take kalla, ganin Mummy ta fito a ciki yasa Yusuf ya karasa kusanta yana murmushi, har kasa ya durkusa ya ce "Ina yini Mummy" cike da fara'a ta ce "Lafiya kalau Yusuf, how is work?" Ya ce "Alhamdulilah" ta ce "Masha Allah" daga haka ta wuce cikin gida, tashi Yusuf yayi yana kallan Rafi'ah ya ce "Dear, i think i have to go, ko zaki zo muje shopping?" Ta dan girgiza kai ta ce "So kake Ummi ta kakkaryani?" dariya ya danyi ya ce "We are not going far" ta noke kafada ta ce "I'm not going anywhere" har lokacin Jawad na cikin motarsa yana kallansu ta cikin tinted glasses dinsa, after some seconds ya bude kofar motar ya fito, da fara'a Yusuf ya mika masa hannu, shima hannu ya mika masa suka gaisa, sai dai bai kalleshi ba, ya zame hannunsa ya nufi gate, Rafi'ah ta ce "I'm not saying i won't follow u anymore, watarana ai zamuje shopping din but not now" juyowa Jawad yayi ya kalleta kafin ya tura gate din ya shige. Yusuf ya ce "When is that time?" Ta ce "Idan na gama exams dina, and we are going with khairiyya" ya ce "Sure, zan kawota ranar Saturday ta gaisheki" cike da farinciki ta ce "Yess thank u Doctor" ya ce "Mention not, bana tafi dan naga kinfi son Khairiyya akai na" murmushi tayi me kyau kafin ta ce "And it's impossible, after Abbana da Ummina, Mummyna then it's you" daga haka ta boye fuskarta ta nufi gate ya bita da kallo yana murmushi, sai data shige sannan ya shiga motarsa ya bar layin. Da sallama ta shiga parlor'n tana kallan Mummy ta ce "Sannu da zuwa" Mummy ta ce "Yauwa Daughter" kallan Jawad tayi dake magana da Ummi ta ce "Ina yini" ya ce "Lafiya" Ummi ta kalli Rafi'ah dake kokarin daukan laptop ta ce "Ki kawowa Jawad abinci Rafi'ah" toh kawai tace ta nufi kitchen, Mummy ta mike tana kallan Ummi ta ce "Kuma baima ci abinci ba tinda safe" shi dai sunkuyar da kansa kawai yayi, Ummi ta ce "A dinga kula fa Jawad, are u not afraid of Ulcer" ya danyi murmushi kawai baice komai ba, Ummi ta ce "A dai kiyaye gaskiya" daga haka tabi bayan Mummy suka haura upstairs. Warmers din abincin ta dauko a kitchen ta dora akan dinning, ta koma kitchen ta bude fridge ta dauko drink da table water, tana fitowa ta sameshi zaune akan dinning din, ta ajiye abubuwan hannunta zata juya ya kamo hannunta, with shock ta juyo tana kallansa, idansa na kan warmers din abincin ya ce "Saurayi zaki bi ya kaiki shopping mall ko?" zame hannunta tayi cikin nasa ta ce "And so" Jawad ya dago kansa yana kallanta ya ce "Wannan mutumin da kike gani is just here to spoil ur life and use you, baso na tsakani da Allah yake miki ba, and ki bar ganin yana kaiki shopping malls stop thinking he will stop there, one day he will request for something else" zama tayi akan kujerar dake gefenshi ta ce "Ni bai ta6a kaini wani waje ba, and this is the first time he's asking me to go for shopping, i trust him and he's more than kind " bayan tayi shiru ya ce "So be careful with guys most of them are of that intention of spoiling young girls, ba kuma a cewa an yarda da mutum, the person very close to u can deceive you, so u take very good care of yourself" sauke kanta tayi kasa a hankali ta ce "Thank u" har zaiyi magana phone dinsa ya fara ringing ya ciro wayar a pocket dinsa yayi picking call din hade da sallama, Mami ta ce "Ai sai ka kira kaji ko mun isa lafiya ko? Amma shiru~shiru ba call, or are u happy for my absence Jawad?" A hankali ya ce "No, aiki ne ya min yawa ko gida ban koma ba, but you're on my mind to call" Mami tayi shiru kafin ta ce "To ka tafin gidan Kawun?" Ya ce "Till tomorrow ai ban koma gida ba har yanzu" ta ce "To shikkenan gobe da sassafe ka tattara ya naka ya naka ka bar gidan" silently ya ce "To Mami, a huta gajiya" ta ce "Yauwa, Allah ya kare min kai" daga haka tayi hanging wayar. Kallansa kawai Rafi'ah take jin karyar daya zuka, ya dago kansa yana kallanta ya ce "So is an advice" tashi tayi ta dauka laptop dinta dake kan sofa ta ce "Thanks for d advice" daga haka ta wuce sama ya bita da kallo.
Chapter 31 · 0% Book details