← Book details Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 43

Sashe 9

Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

08033748387.
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Fa’duwar gaba ce ta samu Umma ta rasa me zata cewa Baffa da ya zuba mata ido yana jiran ta tashi ta kira masa Nenen. “Ba ki ji ne?” Ya maimaita idanunsa cikin nata. Ta sunkuyar da kanta tana wasa da zoben hannunta kafin ta furta “Nene bata dawo ba, tana wajen Hajja saboda yanayin jikin Hajjan ba da’di.” Kallon da ya yiwa idanunta ka’dai sun isa ta shaida bai gamsu da abinda ta ce ba, bai mata magana ba ya d’au remote ya danna don kallon News. Itama shirun ta yi kafin ta Mik’e ta bar parlourn gudun kada ya sake jefo mata wata tambayar.

_____

Hankalin kowa a masarauta ya raja’a ne game da Tauraruwa da bikin Murad da ta fara tsarawa na kece raini. Duk da mutane sun matsu su ji labarin yarda aka yi ta mutu ta dawo musamman wa’danda suke da ruwa da tsaki a cikin kisan, sai dai Tauraruwa ta ja bakinta ta tsuke ta tsaya tsayin daka akan sai wancan lokacin ya yi. Maimartaba dai ta gutsira masa ka’dan daga sashen labarin ganin hankalinsa ya kasa kwanciya ya matsu da jin yarda aka haihu a ragaya. Mutane da dama cikinsu ya d’uri ruwa ganin kamar watan tonon asirinsu ya zo. Tauraruwa dai bin kowa take da ido tana sakar musu murmushin da sam suka kasa gane ma’anar fassararsa.

Yau ma tun safe ta sa aka dinga shigo da wasu manyan akwatina masu masifar kyau. Mai martaba dai ya dinga bin ta da kallo kafin ya furta “Wannan iyayen akwatinan na menene Tauraruwa?” Murmushi ta saki kafin ta furta “Na auren Murad ne, gobe In sha Allah za’a kai lefe gidan da na nema masa auren.” “Sun yi kyau sai ki kira Saddik’a ki gaya mata idan ma baki gayawa sauran ba.” Ta d’aga kai “Zan kira Saddik’a don ta cancanci na yaba mata game da rik’on da ta yiwa Murad ba mugunta kamar ita ta haifa min shi, nagode mata ina k’ara gode mata, amma Rahinatu kam yanzu muka fara tak’un sak’a da ita.” Ya jinjina kai kawai don shima abubuwa da dama Raheena na bashi mamaki. “Ki saka Jakadiya ta kirata.” Ta girgiza kai “Da kai na zan je, ko don na girma mata a matsayin Uwar rik’o Murad, na lura tunda na bayyana suka kasa shigowa sashenka kamar dama jira suke na dawo su bar maka ni.” Murmushi Sarki ya yi a zuciyarsa yana furta ba dole su tattara komatsansu su k’yale miki ragama ba, wa zai iya da jidalin ki Tauraruwa. Yana kallo ta fice daga d’akin cikin taku mai bayyana isarta. Duk inda hadiman sarkin suka ganta sai a zube a kai gaisuwa, ita kuma fuska a washe take amsa musu tana bin su da kyauta kamar yarda ta saba. Idan ta wuce kuwa har a zuciyarsu suke mata fatan nasara don suna ji da ita macece mai kyauta da tsananin tausayin talaka shi yasa sanda mutuwar ta ta riski kunnuwan jama’ar masarautar suka shiga tashin hankali sosai.

Ta gefen d’akin Raheena ta bi, cikin sa’a Raheenan na zaune a farfajiyarta suka ha’da ido da sauri ta d’auke kanta, Tauraruwa bata barta ba sai da ta k’arasa wajenta, cikin takun isa mai bayyana ta isa d’in ta ja kujerar gefen Raheenan ta zauna tana mata kallo k’asa k’asa wanda kai tsaye ke nuni da cewa “Ina nan ban tafi ba ya son ran ki?” Raheena kasa kallonta ta yi ta d’auke kanta zuciyarta na harba mata da sauri gani take kallon da Tauraruwar take mata kamar ta bankad’o wancan b’aragurbin sirrin nata ne. Murmushi ta saki kafin ta mik’e tana cewa “Hajiya Raheena, ya aka ji da hidima?” Kasa amsawa ta yi sai ha’diyar yawu take a hankali ta kasa amsa mata “Na san dama ba zaki amsa ba, sak’o guda zan baki ki gayawa muk’arrabanki mai guri yazo mai Tabarma
Sai ya na’de ya ba shi, kuma Tauraruwa dashen Allah ce ba abinda zai same ni sai ikon Allah!” Daga haka ta wuce ta bar Raheena na jefa mata hararar bayan fage.

Fulani Saddik’a kuwa a parlour suka sameta ita da Murad suna zaune magana suke a hankali da alama basa son wani ya ji. Turo k’ofar da tayi ne yasa suka yi saurin d’aga kai idanuwansu ya fad’a cikin nata. Murmushi ta sakar musu tana zagawa ta gefensu ta zauna daf da Fulani tana furta “Uwa da d’a mai ake tattaunawa ne? Na katse muku hanzari dama zuwa na yi nace miki ga lefen d’an ki can ki je ki gani…” Fulani Saddik’a ta jinjina kai tana kallon Murad da ya ha’de ransa sosai kamar bai tab’a dariya ba. Fulani ta ce “Murad baka ga Babarka ba ne baka gaisheta ba?” A fusace ya d’ago yana hura hanci murya a d’ashe ya ce “Ni ba ni da wata uwa da ta zarce ke da Nene.” Tauraruwa ta d’ago da sauri tana kallonsa kafin ta kalli Saddik’a da take shirin masa magana ta girgiza mata kai kawai alamar kada ta yi. A hankali ta ce “Murad ya fi ki gaskiya Saddik’a ban cancanci zama Uwa a wajensa ba, amma wacece Nene?” “Itace wacce ta yi nak’uda ta haife ni kika k’wace a wajenta.” D’if Tauraruwa ta yi, da alama maganar ta doki kwanyarta, ta ce “Ita Nenen ce ta gaya maka? A ina kuka ha’du?” “A gidan nan ko yanzu tana tare da ni.” Lumshe idanunta tauraruwa ta yi wani murmushi na sub’uce mata ta furta “A kira min Nene.” Da sauri ya mata wani kallo sai ya ji a zuciyarsa yana tsoron ha’da su kada ta je ta yiwa Nenen wani mugun abu. “Ba zan kirata ki cuceta ba, ki fa’di koma meye ni zan isar mata.” Murmushin ta sake yi tana kallon Fulani Saddik’a da take ta k’ok’arin dakatar da Murad daga rashin kunyar da yake yi. Hannunta ta d’aga mata ta ce “Ko rabu da shi time will tell zai gane tsakanin ni da wacce yake cewa itace Babartasa wacece Babarsa a zahiri, ki shirya mu je ki ga kaya ko kuma idan kin gama ki taho ki gani, sannan ki yi selecting wad’anda za su kai kayan, Murad a gaida Nene ka ce mata Tauraruwa Tana gaisheta ka cigaba da killaceta….” Ta fice tana sake jifansu da murmushi. A fusace Fulani ta kalleshi, “Me ka aikata Murad? Rashin kunya fa ka mata? Da gaske duk duniya baka da wata Baba sata wuceta ni kai na na shaida baka ga kamannin da kake da ita na kwabo da kwabo ba? Ko da Nenen ba kwa kama kamar yarda kake yi da ita.” Ya runtse idanunsa kawai baya ma buk’atar wata magana zuciyarsa a raunane take tun bayan duk iya bincikensa ya rasa wata shaida sahihiya. Mik’ewa kawai ya yi ya fice daga sashen ya nufi nasa gidan cikin
Motarsa a mugun speed zuciyarsa yake son ta huta daga binciken da yake mai wujijjiga masa kwanya.

Fulani Saddik’a ta je taga kaya ta saka albarka Tana duban Tauraruwa ta ce “A ina matar take?” Shiru Tauraruwa ta mata kafin ta ce “Y’ar Sarkin Yola ce.” Fulani Saddik’a ta saki ajiyar zuciya kawai ba tare da ta sake furta komai ba, duk da akwai tambayoyin fal a zuciyarta sai dai bata ga fuska a wajen Tauraruwar ba. Ta mik’e tsam da nufin fita daga parlourn kafin ta tsinkayi muryar Tauraruwa daga sama tana fa’din “Ina godiya k’warai da gaske akan rik’on da kika yiwa Murad Rabbi Ya saka a mizani, don haka har a yanzu ki k’addara ke ma matsayin Uwar Murad kike, gobe In sha Allah ki zab’i da wanda za’a je kai kayan lefen.” Fulani Saddik’a ta d’aga kai tana jin nauyin da k’irjinta ya yi da damuwar da zuciyarta take ciki suna raguwa a hankali suna bin iska, yanzu ta samu k’warin gwiwar cewa Tauraruwa bata zo da k’arfin ta don k’wace Murad daga hannunta ba kamar yarda zuciyarta take hasashe. Don haka ta ji duk wani k’udirin da ta niyyata na raba Murad da Tauraruwa ta sanya shi a gefe in dai Tauraruwa zata mata k’arar barinta har abada a mahallin Uwar Murad ba taga dalilin da ita zata kasa mata uziri akan dukkkan abinda take buk’ata ba, zata mata abidna take so za kuma ta tsaya tsayin daka har auren Murad a yi shi cikin nasara da sa’a. Ta fita tana jin zuciyarta wasai, Tauraruwa ta bi bayanta da kallo cike da tausayawa tabbas rashin haihuwa babbar jarrabawa ce da Allah ya kewa bayinsa da yake so idan ka dage ka ci jarrabawar sai ka samu tagomashi ranar alk’iyama da sakamako mafi kyawu.

Fulani Raheena kuwa zuwa lokacin ta fita daga hayyaacinta duk inda zaka ganta cikin tunani take na neman mafita, tabbas ta tabbata a tutar babu, dukkan k’udirinta da burinta yana neman ya rushe sakamakon rashin adalcin da mutanen can suke son mata, suna son su zame su tattara dukkan laifin a kanta. Lokaci guda ta zuge ta rame bata da lokacin kanta balle na Sarkin da ta tabbatar yanzu tunda Tauraruwa ta dawo shima baya buk’atarta.

An kai lefe an kuma karb’e su cikin girma da mutunci, Fulani Saddik’a ta ji da’din karb’ar da aka musu. Suka dawo suna bawa Tauraruwa labarin karamci da girma da arzikin mutanen su ake kira masu arziki ba y’an taka haye ba. Masu k’aryar arziki su dinga kallon mutum kallon hadarin kaji.

Zuciyar Fulani Saddik’a fresh ta shiga wajen Nene don isar mata da albishir d’in gidan karamcin da Murad zai yi aure. Nene ta ji da’di a ranta, a fili kuma ta sanyawa auren albarka tana fatan Ranar da Allah zai nuna mata Auren Jaheed da Najee haka. Fulani Saddik’a ta sake kwantar mata da hankali da cewa ta bar komai a hannun Allah In sha Allah gaskiya zata yi halin ta. Shiru kawai ta yi tana fatan duk sanda gaskiyar zata yi halinta Allah yasa a mata adalci a cikin dukkan hukuncin da za’a yanke mata.
Chapter 9 · 0% Book details