← Book details Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 43

Sashe 37

Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

08033748387.
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Shiru Najwa ta yi k’irjinta yana wani irin bugu da k’arfin gaske…. Murad kuwa da murmushin gefen kumatu yake binta yana hango yarda yarinta ta baibaye fuskarta da idanunta. “An mayar da auren mu yau! Baffa da Maimartaba sun sake d’aura mana aure ba tare da sanin Nene ba, kin san tunda na sake ki ba tare da na d’ora miki Idda ba dole ne sai an sake d’aura mana aure Jaheed ya shige min gaba wajen Baffa….” Ya fa’da yana d’an lumshe ido tuno yarda suka yi da Baffan sanda ya je gidan bayan ya bar wajen Najee daga d’akin Nene. Kallo guda Baffa ya yi masa ya d’auke kai wata fargaba tana shigarsa baya son tunanin da yake ya zama gaske, idan har ya tabbata haka ne za su bar yara su yi zaman zina ba tare da sun san me suka aikata ba. Ya saki ajiyar zuciya yana furta “Shigo Murad!” Ya shiga cikin nutsuwar da iya gangar jikinsa ne kawai yake nuna hakan banda zuciyarsa da take a tsorace da hukuncin da Baffan zai yanke masa baya son hukuncin ya zama daidai da na Nene. A gefen Baffan ya zauna a k’asa duk hana shi hakan da Baffan ya yi. Jaheed kuma yana daga d’aya gefen shi da Faruk. “Me yasa ka rabu da matarka?” Baffa ya jeho masa tambayar da ta kusa tarwatsa kwanyarsa. Wasa ya shiga yi da yatsun hannunsa kamar mace na gaban surukanta a ha’duwar farko. Baffa ya k’ura masa ido ganin yanayin da yake “Ina jin ka!” Ya fa’da da kakkaurar murya da yasa Murad saurin gyara zama ya fara bawa Baffan labarin tunda ga ganin farko da ya yiwa Najee cikin b’atacciyar kama da kuma ganinta da ya yi a kamanninta na asali ya kuma gayawa Tauraruwa ita yake so amma suka cigaba da b’oye masa gaskiyar lamari har ta kai ga ya furta saki cikin rashin sani…” Baffa ya jinjina wautar Najwa da ma su Tauraruwa gaba d’aya wa yake wasa da aure har haka kamar a shirin film.. A fili ya saki tsaki a lokacin kam duk wani laifin Murad da yake gani ya goge tas sai laifin Tauraruwa da su Nene har ma da Umma gaba d’aya, ko waye ma zai aikata abinda Murad ya aikata musamman da ya nuna masa hoton Najwa da b’atacciyar kama. “Kana son matarka har yanzu?” Da sauri Murad ya ce “Wallahi ina sonta Baffa.” Dariya Faruk da Jaheed suka saki. Baffa ma sai da ya murmusa yana kallon Murad ko bai rantse ba a idanunsa yake kallon tsantsar son da yakewa Najwa. “Zan mayar da aurenku yau, saboda haka musulunci ya shar’anta idan mutum ya saki mace ba tare da ya d’ora mata idda ba dole sai an sake d’aura musu aure don haka sai ka sake bada sadaki yanzu anjima zan saka a mayar da aurenku a masallaci…” Da sauri Murad ya gyara zama ya hau laluban aljihunsa duk wasu ku’di da suke ciki sai da ya fito da su bai lura da yawansu ba ya dank’awa Baffa. Baffa ya ce Jaheed ya karb’a yana furta “Allah ya sanya musu albarka, abu na gaba bana son ka gaywa iyayenka mata an mayar da aurenku ka ja bakinka ka yi shiru zan dai kira Maimartaba na sanar masa bayansu bana son ka sanar da sakarkarun iyayenka mata nima kuma zan ja bakina na yi shiru naga iya gudun ruwansu.” Farin cikin Murad kasa b’oyuwa ya yi godiya kawai yake zabgawa Baffa su Jaheed Suna tsokanarsa da yammacin ranar aka sake mayar da aurensu a masallacin gidan Baffan. Shine bayan Magriba suka nufi asibiti zuciyar Murad fal da farin ciki…
Chapter 37 · 0% Book details