Sashe 35
Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A zaune ta same shi a parlourn irin zaman da da zarar ka gan shi ka san wanda ya yi shi baya cikin kwanciyar hankali. Ya amsa sallamarta kafin ya bata izinin shiga. Kanta a sunne a k’asa ta shiga parlourn ta samu gefe ta rakub’e. A yanayin zaman da suka yi da Umman ya tabbatar mata zuk’atansu basa cikin sukuni. Tana shirin gaisheshi ta ji muryarsa cikin ginshira ya watso mata tambaya “A yaushe ya saketa ban sani ba Kuma me ta yi masa? Amsa ta zamo gaskiya zahiran..” Dukan da zuciyar Nene take yi a lokacin da kana kusa da ita tsaf zaka iya jin bugunta. “Ina jin ki..” “Ranar da ta tare…” Ya d’ago cikin wani irin rashin kuzari ya zuba mata idanunsa ya ce “Me yasa ban sani ba sai yanzu? Tana ina kuma?” Gumi ne sosai ya shiga tsatstsafo mata ta saka hannunta ta share duk da haka bai fasa zuba ba. “Ka yi hak’uri Baffa tana gidan Hajja da kai na na kai ta…” Sake ha’de fuskarsa ya yi sosai kafin ya d’an girgiza kai. Tana kallo ya zaro waya a aljihunsa numberr Faruk ya kira yana d’agawa ya ce “Faruk ka d’auko min Najwa a gidan Hajja.” Daga haka ya kashe wayar ya ce “Tashi ki je Allah yasa haka ya zama alheri garesu da mu baki d’aya.” K’afafunta sam kasa jinta ta yi a jikinta faranta da duk wani muradinta a lokacin bai wuce ta farka ta ji mafarki take ba gaske ba. Sai dai idanun da Umma ta zuba mata ya ankarar da ita gaske ne ba mafarki ba. Cikin sanyin jiki ta nufi k’ofa. “Ki shirya gobe zasu wuce da ke masarauta Allah ya baku zaman lafiya ya ka’de dukkan fitina..” Kasa amsawa ta yi tana jin a zuciyarta kamar da gatse Baffa ya yi furucin. Haushin Murad ya sake ninkuwa a zuciyarta ta k’udirce a ranta sai ta b’ata masa rai sosai ta yarda ko gaba aka ce ya sake aikata irin kuskuren nan ba zai sake ba.
Tana Fita Umma ta kalli Baffa shima d’in ita yake kallo. Kafin ta furta kalmomin da take hak’ilo wajen furtasu ya ce “Wa ma k’adarullahu hak’k’a k’adarihi… ba wani bawa da yake k’etare k’addararsa ki sanya wannan a zuciyarki sai ranki ya samu salama. Ba yinsa ba ne ba kuma ikonsa ba ne abu ne da yazo a cikin littafin K’addarrsa zai aureta zai kuma saketa, ba wani bawa da ya isa ya k’ulla ko ya raba aure sai Allah, Fatan da zamu yi Allah yasa hakan ya zama alheri garesu.” Wani irin sanyi Umma ta dinga ji yana kwaranya a zuciyarta duk wani turiri da hucin da zuciyarta take yi sai ta ji ta samu salama, zuciyar kuma ta yi sanyi kamar an zuba mata k’ank’ara. Ta saki ajiyar zuciyar da ta tafi da duk b’acin ranta a hankali ta furta “Khairan In sha Allah, Rabbi Tawakkaltu ilaika.” Baffa yana murmushi ya dinga kallonta ya san a irin kyan hali irin na Umma da wuya fushin nata ya sake k’etare ko saman idaniyarta balle ya ratsa zuciyarta. “Allahumma barik.” Ya furta a hankali yana jifanta da wani sahihin murmushin da ya sake narkar da b’acin ranta. Irin su Baffa ne ake kira da Salihan maza y’an Aljanna kamar Mijin Nazeefah 🥳
Nene dai har safe ta kasa sukuni zuciyarta gaba d’aya ba walwala ji take kamar itama ta hak’ura da nata auren sai dai ta san idan ta hak’uran Baffan zai iya yiwa abin wata fassara. Kafin ta tashi da safe har an d’auko Najee daga gidan Hajja da ke Azare. Burin Najee kawai ganin y’an biyu don haka suna zuwa ta shige motar da za’a kai abinci asibiti. Ba tare da ko shiga cikin gidan ta yi ba. Baffa yana lek’a su ta window ya saki ajiyar zuciya kawai tausayin Najeen ya kama shi ganin yarda zawarci ya hauta da k’ananun shekarunta, shekaru sha bakwai. Ya gimtse b’acin ransa jin sallamar Umma data shigo sanar da shi zuwan su Tauraruwa da neman iso wajensa.
Duk da b’oye damuwar zuciyarsa da ya yi hakan bai hana Tauraruwa gane ya ji labarin sakin ba. Don ita wata irin mutum ce mai gane d’abi’ar da halayyar d’an Adam ta yanayinka kawai zata iya fallasa maka duk wani sirrin da yake ranka. “Barka da safiya.” Ta fa’da a hankali cike da muryar kamala. Baffa ya ‘dago yana amsa gaisuwarta da ta sauran jama’ar da suka rako shi. “Idan ba zaka damu ba ina son yin magana da kai ta sirri.” Ta fa’da kanta tsaye ba tare da ta damu da idanun mutanen da suke walagigi a kanta ba. Mik’ewa kawai Baffa ya yi zuwa wani k’aramin parlournsa da bai fiya zamansa ba sai idan irin hakan ta taso.
Zama ya yi itama Tauraruwa ta zauna daga d’aya b’arin da yake. “Ina jin ki.” Ya fa’da cikin muryar da take bayyana dattijantakarsa. “Ina nemawa Murad Afuwa abisa tarin laifi kansa ba komai ya jawo hakan ba sai yarinta don Allah Baffa a yi hak’uri a mai da masa da matarsa ya yi nadama wallahi irin nadamar da take kassara tunanin mutum a yi hak’uri don Allah…” Wani irin kallo Baffa ya d’aga ya jefeta da shi, kafin ya saki murmushi a hankali ya furta “An yi na farko an yi na k’arshe ki k’addara Murad bai tab’a sanin Najwa ba balle har auratayya ta shiga tsakaninsu….” “Ban gane ba Baffa?” Murmushin ya sake sakar mata ya ce “Ba aure a tsakaninsu har abada!” “Tirk’ashi!” Tauraruwa ta furta a hankali ta cikin k’wayar idanun Baffan ta hango rashin wasa a cikin abinda ya furtan kuma da alama ba wani sassauci a cikin zancensa….
Baffa ganin bata da shirin tafiya ya mik’e a hankali don nufar k’ofa ya furta “Allah ya bashi mata ta gari amma banda Najwa…”
JIKAR NASHE🥳
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Shiru d’akin ya d’auka kamar an d’auke wutar nepa, kowa ya kasa motsi mamakin girman wautar Najee kawai Tauraruwa take. Umma kuwa ji ta yi kamar ta tashi ta mugun yi mata duka. Ta mik’e ta fice daga d’akin bayan ta wurgawa Najwa da take tsaye harara. Najwa jikinta ya yi sanyi ta tabbata abinda ta aikata ba mai ma’ana ba ne daga ganin yarda suka ta sha jinin jikinta. Da sauri ta juya zata fice Tauraruwa da take ta sakin murmushi ta saka baki ta kirata. Dawowa ta yi da baya tana kallon Nene itama ta fice daga d’akin ya rage daga ita sai Tauraruwa a d’akin. Cikin murya mara sautin wasa ta kira sunanta “Najwa!” Kiran da Najwa ta ji shi har tsakiyar kanta. Ta d’ago cikin sanyin jiki da na zuciya tana amsawa. “Zo nan.” Ta isa inda Tauraruwar ta nuna mata gefenta ta zauna. “Shekarunki nawa?” “Sha bakwai.” Tauraruwa ta nisa tana mamakin yarda y’ar shekaru sha bakwai a zamanin nan bata son komai ba a fannin sha’awa da auratayya ma gaba d’aya. Lallai ya kamata a jinjinawa Umma da dukkan tarbiyyar da ta bawa yaranta. “Kuna Fikhu a islamiyya?” Najwa ta d’aga kai. “Yauwa Malamanku sun tab’a muku k’arin haske akan Balaga da dukkan abinda ta k’unsa…” wata irin kunya ce ta kamata don sai yanzu karatun ya dawo mata daki daki tana jero shi a kwanyarta kamar yanzu ake biya mata shi da sauri ta runtse idonta tana jin kamar k’asa ta dare ta shige ciki. A zahiri ta furta Kalmar “Na shiga uku mai na aikata?” Sai kuma ta mik’e da mugun gudu ta koma d’akinta ta saka key ta murza tana sakin haki da ajiyar zuciya, tsananin nadama ta shiga zuciyarta wata irin wauta ce yau ta sameta?
Tauraruwa dariya ta yi sosai ganin abinda ta aikata d’in wato da gasken mantawa ta yi sai yanzu ta tuna. Najwa kenan! Ta furta a hankali tana jin son yarinyar har a ranta da kuma tana da dama a yau zata mayar da aurensu don ta fuskanci itama Najwan tana son Murad kamar yarda yake son ta. Mik’ewa ta yi ta fita tana dariyar Nene da Umma suma da suka dare suka barta da yi wa Najwa bayani.
Har suka gama shirin tafiya da Nene Najwa ta k’i yarda ta fito kunya take ji sosai gefe guda kuma matsananciyar sha’awar da Murad ya jawo mata ta girma ma a jikinta wani irin yanayi take ji irin wanda bata tab’a riskar kanta a ciki ba. Ba yarda ba a yi ba ta fito su yi sallama ta k’i dole Nene ta hak’ura tana sake jaddada rok’on Umman a turo mata Najwan ta k’arasa iddarta a wajenta. Umma murmushi kawai ta yi don sun Riga sun gama shirinsu da Abba can Yola zata kaita gidan k’anwarta a can zata yi iddar, Fareeda wayayyiyar macece za kuma ta d’ora Najwa akan duk abinda bata iya ba, don yau tab’argazar da Najwan ta yi ta tsorata Umman sosai ta ina zata yi saken da zata sake aurar da ita bata san komai ba.
Ta window ta dinga lek’en motocinsu tana jin idanuwanta na zubar da hawaye, ba na komai ba ne sai na rabawa da Nenenta matar da ta d’auka kamar Uwa gareta. Ta ji zuciyarta ta yi zafi abu goma da ashirin ya ha’de mata a zuciya ga waccan matsalar ga kuma wata daban. Murad ya bar mata wani assignment mai girman gaske da har yau ta kasa amsa shi daidai abin sake naso yake mata kamar wani almara. Da Umma aka tafi raka Nenen don haka ta ji gidan ya mata girma don haka ta nufi sashen Mahmeey wajen Yayarta Nasma idan zasu tafi asibiti ta bi su.