← Book details Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 43

Sashe 36

Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A fada an musu wata irin tarba ta mutunci da karramawa. Fulani Saddik’a ta shirya musu Walima duk da ba mutane da yawa amma akwai abinciccika kala kala masu yawan gaske. Nene dai jin ta take kamar a mafarki ta kasa sakewa duk da k’ok’arin Tauraruwa da Saddik’a na son ta aikata hakan. Kwarjinin Sarki da wata irin Haiba sun cika mata idanu taf har ta fara jin tsoron a kirata da matar Sarki. Tabbas lamarin Ubangiji yana da girman gaske, daga y’ar bayi yau itace kai tsaye take amsa suna MATAR SARKIN GABAS. Ta lumshe idonta tana jinjina godiyarta da yabo ga rabbil izzati.

Aka ci aka sha aka Kuma addu’a da wasa da raha kafin Tauraruwa ta kama hannunta don isa da ita sashenta. Umma na gefenta suna shiga sashen su dinga yaba kyau da tsaruwa da sashen ya yi komai Sabo ne dal mai kuma tsadar gaske tabbas Naira ta yi kuka wajen shirya b’angaren nata sai kace a fadar Sarauniya England. Tattausan k’amshi ne kawai kai caku’de da na turaren wuta da sanyin A.C ya gauraye sashen. Nan aka bu’de k’ofa bayi suka dinga kawo gaisuwa kowa kuma ya shigo sai ya yaba da amaryar da kuma sashen duka . Don Nene dawowa ta yi kamar wata y’ar shekara talatin sai walwali take tana shining jikinta ya cika ko ina b’ul b’ul Masha Allah. Umma dai bayan Tauraruwa ta bi don ta ce a wajen Tauraruwar zata kwana da yake sai kashegari za’a mayar da ita garin Kano. Nene duk da bata so ba haka tana ji tana gani ta hak’ura ta fuskanci rayuwar da take jiranta a gaba….duk da wani sashe na zuciyarta tana jin mugun tsoron fuskantar mai martaba da sunan mijinta tunda abu ne bak’o a wajenta wancan da ya faru ba abinda zata k’arar a cikinsa kusan yanzu ne zata san menene aure? Me kuma da’dinsa da rashinsa yake nufi tana fata dai koma menene zai zo mata yazo mata cikin rahamar Ubangiji. Ta saki ajiyar zuciya tana bin sashen nata da kallo ganin yarda ya yi tsit kowa ya watse sai tsirarun masu mata hidima da suke can parlour na farko.

Sai Yamma suka yi shirin tafiya asibitin. Cikin shigar wata doguwar Riga da ta masifar yi musu kyau suka yi rolling da mayafin rigar da ya sake fito fa kamalar fuskarsu. Glass Najwa ta saka mai kyawun gaske a idonta sai ta sake yin d’as da ita kamar ka sureta ka gudu. Driver ya ja suka isa asibitin.

Ba kowa a d’akin daga ita sai nurse d’aya sai Babies d’in. Najwa da sauri ta d’au Baby d’ayan tana fa’din “Ya zama dole na fara banbance ku, yara sai shegen kyau ga su kamarsu d’aya.” Najma tana dariya ta ce “Matso na banbanta miki su, wannan na hannunki Murad ne sak Mijinki…” Gaban Najee ya wani irin bugawa da sauri ta d’an yi yak’e tana furta “Mhmnn.” Daidai lokacin suka turo k’ofa suka shigo dukkansu fara’a fal fuskarsu Murad idanunsa cikin Najee da ta yi saurin d’auke kai tana jin haushin yanayin da yake jefata. Murmushi ya saki yana kallon Jaheed da ya d’an d’aga masa gira suka saka dariya a tare kafin Murad ya ‘Dan gintse ya nemi kujera ya zauna still idanunsa zube a kan Najwa da ta kasa motsin Kirki sai wasa take da yatsun Baby Hassan. Ya d’an yi gyaran muryar da yasa ta ji kamar ta saka ihu saboda abinda ta ji ya tsirga mata gaba d’aya ya ba’de d’akin da k’amshin turarensa. “Najwa kawo min yaro na…” k’iris ya rage Babyn bai sub’uce daga hannunta ba, jin yarda ya kira sunanta da wata irin siga. Ganin ta k’i motsi tsam ya mik’e ya nufi inda take cikin wani irin taku ya sunkuya daidai kanta tana jin saukar numfashinsa a wuyanta k’iris ya rage bata saki fitsari ba, ya sa hannunsa ya janye nata hannun ta ji kamar an mata shocking a hannun ta d’ago a tsiwace zata masa masifa ya kasheta da wani irin kallon da yasa bakinta ya mutu ba shiri ya zare yaron daga jikinta a kunnenta ya ra’da “Idan kin ji haushi get ready to have your’s…..” Ya zauna daf da ita bai damu da kallon da mutanen d’akin suke masa ba, burinsa isar da sak’on so, don ya lura sam yarinyar bata san ma me ye so ba. Matsawa ta yi niyyyar yi ya take k’afarta da tasa k’afar “Kina jin feeling ne idan na zauna kusa da ke?” Ya fad’a ta yarda ba mai ji sai ita. Cikin dakiya da k’arfin hali ta murgu’da masa baki tana furta “God forbid.” Ya waro ido yana kallonta kafin ya d’aga gira d’aya ya furta “So yanzu kin san me nake nufi?” Ta d’auke kai murmushi ya saki yana kallon Nasma ya ce “Nasma k’anwarki fa Villager ce.” Nasma dariya ta yi kawai sai ta ji suna burgeta yanayin tasa soyayyar irin mai tsayawa a rannan ce da alama gwani ne a fagen nuna kulawa ga mace. Har bayan Isha’i suna zaune kuma bai bata dama ko ka’dan ta matsawa daga jikinsa ba, ya bi ya takurata irin takurar da take jinta har tsakiyar kanta, ji take kamar ta saka ihu. K’amshin turarensa ya bi yi manne gam a kayanta. Sai 8:30 ya mik’e yana kallonsu “Ku taso mu tafi gida.” Najwa ta waro ido “Me ye ha’din tafiyarmu da kai.” “Saboda nima Baffa ya ce a can zan kwana bai amince na sauka a hotel ba, idan kuma gorin gida zaki min let me know sai na kama gaba na, na kuma gaywa Baffa.” Ya fa’da yana koyon irin maganarta yana kuma narkar da idanunsa cikin nata, hakan ya sata yin shirin dole kafin murya a sark’e ta ce “Ku je kawai ni anan zan kwana..”. “Ki hanata soyayya da Mijin ta kenan ko? Tana son ta ji d’imun mijinta ki zo ki zauna musu…” Najee runtse ido kawai ta yi ta mik’e ta fice da gudu. Murad ya d’au jakarta yana dariya ya kalli Nasma “Mu je ko?” “Aa Ya Murad ku je kawai zan kira Driver…” Dariya ya ce “Hakan ma ya yi Allah ya miki albarka asuba ta gari…” Ya fita da d’an hanzari. Duka d’akin dariya suka yi suna mamakin k’arfin hali irin na Murad.

A tsaye ya tarar da ita tana ta cin magani. Ya k’arasa wajenta yana dariya k’asa k’asa. “Shall we?” Ya furta a hankali yana kama hannunta ta janye hannun tana furta bana so.” “Ni kuma ina so shine ma abu mafi soyuwa a gareni a duniyar nan….” ya furta yana lek’en fiskarta ta hau dube dube tana kallon hanya. “Nasma ta k’i biyomu bata son ta takurawa love birds so feel free daga ni sai ke!” “Cab’di!” Ta furta a hankali tana gyara tsayuwarta “Nima ba inda za ni.” “Wasa kenan!” Ya furta yana dariya “ki taho Malama ko na d’aga ki cak aba kamar Baby doll.” Wani irin kallo ta wurga masa ya matsa daf da ita “Kina ganin ba zan iya ba?” Ya fa’da yana juyawa sai ji ta yi ya yi sama da ita cak. Ta fara turje masa ya saka yatsa ya d’alle bakinta “Ki min shiru gobe ma ki sake min tsiwa.” Bai direta ko ina ba sai wajen mota. Ya kuma sakata ta dole ya shiga ya danna lock.. yana d’an sakin haki ya ce “Ashe dai kina da nauyi? Ko da yake na san inda suke da nauyi a jikin naki….” Ya fa’da yana kallon inda yake nufi d’in wani irin bugu k’irjinta yake ga shi mahaukacin feeling d’in da take ji ya fara zuwa ta ja d’an bakinta ta tsuke don ta lura hanyar da kunya take Murad bai santa ba. “Na nuna miki wajen?” Ta girgiza kai da sauri tana furta “Na yafe.” Dariya ya yi sosai ya ce “Sai tsoro sai tsiwa.” Lumshe idonta kawai ta yi ba tare da ta san inda za su je ba, sai da ta ji ya yi parking ta bu’de idonta tana kallonsa “Nan fa? Me za mu yi?” “Love… And honey moon…” Ta bu’de idonta da sauri “Ban gane ba?” “Zaki gane idan mun shiga.” Ya fa’da yana saka hannunsa saman fuskarta ya janyo hab’arta “Najwa kalle ni nan…” Ta d’ago a hankali tana kallonsa ya furta “Ki amince zaki cigaba da zama da ni a matsayin Miji?” Wani irin dum ta ji kwanyarta ta buga ya hau murza hannunta a hankali yana furta “Answer me, Idan kin yarda a yau zamu bar k’asar nan…
And I promised you Nene zata yafe mana idan ta ga jikanta a hannu….

JIKAR NASHE……🥳
Chapter 36 · 0% Book details