← Book details Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 43

Sashe 16

Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

08033748387.
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Dukkanmu a razane muke duban mutumin da yake tsaye ba kowa bane sai mai tsaron bakin zauren gidan Baffa Liman. Muka sauke ajiyar zuciya duk kusan a tare ganin ba mutanen da muke tunani ba ne. Baffa Liman ya ce “Lafiya D’an Audu.” Ya girgiza kai a tsorace ya ce “Wallahi mutane ne suka dunfaro nan… shi yasa na yi saurin zuwa na sanar muku.” Da sauri na mik’e ina kallon Baffa Liman da yake nuno min Amintacce “Ku bi da shi ta k’ofar Baya Hajiya K’arama, ni kuma zan san yarda zan yi da jama’ar da Suka yi yo nan d’in, amma ki tabbata a daren nan ya ha’de kaf iyalinsa sun bar masarautar nan don zamansu anan d’in akwai hatsari mai girman gaske…” Kafin ya gama muka dinga jin suna durfafo inda mu ke, tuni muka fice ni da Amintacce ta k’ofar baya jikinmu duk rawa yake sosai don razana da firgita. Mun yi tafiya mai nisan gaske ta hanyar da ba zasu tab’a ganin mu ba, kafin mu isa gidan Amintacce ya shiga ba su tsaya b’ata lokaci ba suka fito da matarsa da yaranta maza ban bar su sun d’au komai ba banda kayan jikinsu suka nufi hanyar da zata sada su da cikin gari bayan na ba su wani mukullin gida na wanda Amintacce ne kawai ya san da shi. Sai da naga b’acewarsu sannan na koma sai dai ban isa gidan da nake d’in ba, na dai cigaba da k’udundune mukullin d’akina na inda sirrikana suke ciki. Gidan Baffa Liman na nufa kai tsaye don na san zuwa lokacin ya isa gidan sa na san kuma wa’dancan mutanen za su cigaba da bibiyar gidan tunda har hankalinsu ya kai nan, ba za su k’yale gidan ba sai zuwa wayewar gari idan sun tabbatar Amintacce ya tattare zuri’arsa sun bar masarauta.

Shiru gidan Baffa Liman d’in, tsoro ya cika min zuciyata da ba tambayi matar gidan ta amsa min da Baffan bai dawo ba, hantar cikina ta d’aka ina duban matarsa da ba abinda ya dameta tana ta harkar gabanta da alama bata shaida ni ba dalilin b’atar da kamar da na yi. Na sake tambayarta “Me zai hana shi dawowa ga shi har goshin asuba ya zo.” Ta d’an juyo tana kallona sai kuma ta ce “Ba mamaki ya nufi masallaci sallar asuba dama ya saba fita a wannan lokacin.” Zuciyata bata amince da abinda ta ce d’in ba, sai dai ya zama dole na yarda don samun sauk’in bugun da zuciyata take tsoro mai girma ya riski zuciyata bana son wani abu ya samu d’an tsohon da bai ji ba bai gani ba.

Ban sake firgita ba sai da naga har gari ya fara haske amma ba Baffa ba labarinsa, sannan ne fa na tabbatar da rashin wanzuwar lafiya, na zare jikina daga gidan cikin b’atacciyar shigata na nufi waje har na je bakin masallacin, anan na tarar mutane ana ta tambayar juna dalilin rashin fitowar Liman masallaci hankalina ya sake tashi ga shi ko yaransa ban gani ba balle na tambayesu. Haka na ja gefe na zauna zuciyata na wani irin bugu na tabbata dai tabbas Baffa ba lafiya yake ba.

Sai k’arfe 8:00 na safe rasuwar Baffa Liman da yaransa guda biyu ta kara’de masarautar gabas hankalina ya dugunzuma ya tashi na rasa wanda zan tara da lamarin ba don komai ba sai don bana son na bayyana a matsayin rayayyiya a lokacin.

Aka Sallaci gawar Baffa Liman da yaransa guda biyu da aka kashe, d’ayan ne ban san inda yake ba ban kuma ji labarinsa ba. Na dinga kuka kamar raina zai fita kafin na samu na lallashi zuciyata da niyyar ko ba yanzu ba sai na d’au fansar rayu kan bayin Allahn da ba su ji ba ba su gani ba. Da daren ranar na fice daga masarautar don zama a cikinta bai ganni ba, gidan da su Amintacce suke na nufa.

Hankalinsu a tashe suke kallona ganin yarda yanayi na ya nuna rashin nutsuwa. Amintacce da matarsa suka saka ni a gaba da tambaya kafin na sanar musu rasuwar Baffa Liman, Mutuwar da na ga ta girgiza su matuk’ar girgizawa har ma fiye da ni. Cikin muryar kuka Amintacce ya fara furta “Shikkenan itama Uwata ba zata sha ba, kasheta za su yi Tauraruwa a duk sanda suka samu cikar burinsu, Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna….” Ha’diye wani irin yawu mai d’aci na yi kafin na furta “Ba zasu kasheta ba Amintacce ni na jefaka a cikin wannan masifar ni kuma zan fitar da kai In sha Allah, yanzu abu guda da nake son sani ka san Likitar da aka saka zata mata aikin….” D’an shiru ya yi da alama nazari yake kafin ya d’ago ya ce “Na santa Dr. Hantsi ce…..” waro ido na yi na ce “Hantsi fa ka ce? Yanzu duk yardar da muka yiwa Hantsi da amince mata da muka yi da ita za’a ha’da baki a cutar da mu?” Tuni idanuna suka jirkita tsananin b’acin rai na mik’e ina kallonsa na ce “Tashi mu je har gidanta yau ba zan runtsa ba har sai na ganta, wallahi idan bata yi wasa ba a yau ba sai gobe ba zan aiakta lahira banda ina tsoron mahallici na.” Hantsi ita ce Likita d’aya da Maimartaba ya aminta da ita, shi yasa da na ji sunanta hankalina ya tashi.

Ba nutsuwa a tare da mu har sanda muka tari motar haya zuwa gidan Doctor Hantsi.

Shiru unguwar kasancewar nan ne G.R.A don haka ba yawan mutane sai tarin bishiyu da kukan tsintsaye. Kowa yana gidansa da yake juma’a ne bana mantawa an sakko daga masallaci kenan. A bakin gate muka tsaya muka kuma buk’aci Maigadi ya mana iso wajen Doctorn ka gaya mata sak’o ne daga wajen Maimartaba na Gabas ya ce a kawo mata.” Na fa’da ina kallon maigadin da da ya yi niyyar k’in zuwa ya sanar mata, amma jin abinda na ce sai ya juya da sauri har yana yi kamar ya fa’di duk da shigar mu da kamanninmu ba su yi kama da ta masu arziki ba amma kowa ya san k’arfin mulki irin na masarautar Gabas. Ba a d’au lokaci ba sai ga shi ya dawo ya gaya mana ta ce a kai mu b’angaren bak’i.

Muka bi bayansa har zuwa parlourn da ya kira na bak’i. Mintuna biyar muka d’auka muna jiranta sai gata ta fito cikin shiga mai bayyana wacece ita don kayan likitoci ne a jikinta da alama aikin yamma zata fita.

Kallonmu kawai take da son gane su wanene mu, ganin ta shiga zurfin tunani sai kawai na yaye hiramin kai na, da sauri ta zaro ido duk da babbar rigar da take jikina bai hana kamannina bayyana ba, a ru’de take matuk’a da gaske tana nuna ni tana ja da baya. Murmushi na sakar mata nace “Nutsu Doctor Hantsi ni ce dai Tauraruwa ban mutu ba, ina so kuma ki zauna ki nutsu akwai abinda ya kawo ni wajenki ki ba ni hankalinki nan.” Zama ta yi a d’an d’ofane jikinta na shaking kamar mai jin sanyi ta furta “Ina…..Ina jin Ki….” Murmushi na sakar mata sannan na mik’e na isa inda take. Na dafata dafawar da ta saka ta kusan sumewa. “Nawa suka baki a aikin da zaki musu?” Tsaf ta fahimci abinda nake nufi don haka jikinta na rawa lab’banta suna kakkarwa ta ce “Don Allah ki yi hak’uri Wallahi ban riga da na aikata ba duk da dama tilas suka min da min barazanar mutuwa idan ban aikata ba….” A idanunta na hango gaskiyar zancenta, don haka na daidaita tsayuwata na kuma sassauta fuskata na ce “Ina jin ki, ba ni labari, kada kuma ki min k’Arya a duk abinda zaki fa’da don kin sani ba na yiwa mak’aryaci da sauk’i a duk sanda na gano k’aryar sa.” Ta d’aga kai da sauri tana furta “Ba Zan miki k’arya ba wallahi gaskiya zan gaya miki, k’annen Sarki Da Fulani Raheena ne suka tilasta ni aikata hakan suka kuma tsorata ni da kisa idan ban amince ba kin san su kuma kin san muguntarsu za su iya aikata abinda suka ce shi yasa na yarda… to kuma jiya da aka zo yin dashen sai bai yiwu ba dalili an rasa hanyar da zaa bi a samu Sperm d’in Maimartaba don haka suka ce a gobe suke son na bugar da maimartaba irin buguwar da ba zai san me ya aikata ba, ita kuma yarinyar na mata allurar da zata gusar mata da kwanya na tsahon lokaci.. to a yau Zan musu hakan da daddare……….

JIKAR NASHE✍🏽🥳
Chapter 16 · 0% Book details