Sashe 15
Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A biya ni hakkina idan kin san kina karanta na bati ba kyauta ba ne, na fa’da da Babbar murya KUDIRAR ALLAH BOOK TWO NA KUDI NE EEEHE😏
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Ta sauke numfashi a hankali tana mayar da idonta a kai na, duk gumi ya gama jik’ata sharkaf idanunta sun ka’da sun yi jajur da alama tashin hankalin da take ciki ya wuce misali. Nima dubanta nake idanu cikin idanu na rasa ma me Zan ce mata tsananin mamaki ya hana ni magana, tabbas ta bani mamaki duk da a gefe guda bana ganin laifinsa ga duk wanda aka saka a wannan takunkumin abinda zai aikata kenan, laifinta guda da bata sanar da Maimartaba ba tunda ta san zai bata dukkan kariyar da take buk’ata ba zai bari a cutar da ita ba. Ajiyar zuciya na sauke a hankali wacce take tafiyar da tarin takaicin da ya yi min dabaibayi a zuciya, na lumshe idona wasu hawaye masu zafin gaske suka shiga kwaranyo min, tunda abubuwan suke faruwa sai a lokacin na samu hawaye suka zubo min hawayen da nake jin suna saka sanyi da nutsuwa a zuciyata, hawayen mutuwar Baffa liman na yi kuka amma bana saka sanyin zuciya ba ne na sake saka zuciya a k’unci ne. “Ki yi hak’uri.” Muryarta ta katse min tunani na na bu’de ido a hankali ina kallonta kafin na girgiza kai. “Bakomai Doctor ba ki min komai ba, sai dai ina neman wata alfarma a wajenki, ki aikata duk abinda suka umarceki a daren nan.” Ta ware ido tana kallona cikin zallar mamaki ta ce “Na aikata fa kika ce?” Na d’aga kai ina furta “Hakan nima nake buk’ata, sannan ban amince ko da wasa ki sanar da wani kin gan ni a raye ba, wannan ya zama sirrinmu.” Na fa’da ina kallon cikin tsakiyar idanunta. D’aga kai ta yi alamar ta amsa duk umarnina. “Idan komai ya tafi successfully ina son duk abinda zai faru ki sanar da ni, sannan ina son ki bata dukka kulawa da ta dace bana son wani abu ya sameta ko ya samu d’an cikinta idan abinda ake buk’ata ya samu akwai kyauta mai girman gaske da zan miki…. Abinci mai kyau, abin sha mai kyau shi nake son a dinga bata bana son ko k’warza ne ya samu yatsanta.” Ta d’aga kai tana tabbatar min da ta d’au dukkan alk’awarin da ta d’auka. Na mik’e ina kallon Amintacce muka tafi Doctor ta raka mu har bakin gate. Muka yi sallama ban koma gida ba, inda su Amintacce suke muka nufa, anan na ha’da musu goma ta arziki na saka aka musu shatar mota suka nufi Garin Yola, na musu alk’awarin bayan kwana biyu nima zan biyo su amma bana son ko da wasa a ga ko inuwarsu a garin Gabas, wannan shine mafarin barin su Amintacce garin nan shine kuma har yanzu ba su dawo ba amma suna nan da ransu har yanzu cikin k’oshin lafiya.
Wata irin ajiyar zuciya Nene ta sauke mai k’arfin gaske tana jin wani abu da ya tsaya mata a k’irji yana narkewa zuwa wani irin sanyi, Farin cikin ganin iyayenta shine abinda ya fi komai a zuciyarta da gaske ta yi murna da ya zama na su Babinta suna raye suna da rabon ganawa kuma. Daraja da kimar Tauraruwa suka sake ninkuwa a zuciyarta fiye da kwantance tun kafin ta ji k’arashen labarin ta tabbata Tauraruwa itace ginshik’in samar da dukka farin ciki a rayuwarta ita ta mata garkuwa ga dukkanin muguntar wa’dannan bayin Allahn.
*
“Na sake komawa gidan da su Amintacce suka zauna, na kuma saka aka ha’da min wayar landline a gidan ba don komai ba sai don na dinga samun duk wani bayani daga bakin Doctor. Koda yaushe a zaman shirin ko ta kwana nake, tunda Doctor ta tabbatar min duk wani aiki ya tafi successfully Maimartaba ya sadu da Nene ba tare da shi ko ita sun san sun aikata hakan ba. Ita kanta bata farko ba sai bayan kwana biyu da afkuwar hakan. Kafin nan Doctor ta mata allurai da drips da zai d’auke mata duk wani ciwo da zata ji a jikinta wanda zai bayyana mata abinda ya faru don haka ba zata gane ba. Su ma kuma ba su san shirinmu da Doctor ba don haka ko a ransu basu kawo Doctor zata ci amanarsu ba dalili sun sanya tsoronsu a zuciyarta ta yarda ba ta yarda za’a yi ta iya k’etare duk shara’din da suka gindaya mata.
Bayan wata guda da faruwar hakan, a karon farko da Doctor ta mata gwaji ta tabbatar da samuwar ciki a jikinta. Sun shiga murna sosai don sun san mugun shirinsu daf yake da cika. Duk da ita Fulani Raheena a zatonta taimakonta za su yi su cika mata nata burin itama, sai dai na su burin daban da nata, su burinsu b’atawa Maimartaba suna don har sun d’au hotunan da zasu watsa a duniya ni na saka aka sace cameras d’in bayan biyan mak’udan ku’dad’e. Sun yi bak’in ciki sosai lokacin da suka wayi gari babu cameras d’in da suka dogara da su. Sanda cikin ya bayyana a lokacin ne kuma Fulani Raheena ta samu cikin d’an Sarkin gabas na gaske, wannan karan kam sai Allah ya zartar da ikonsa ta hanyar samar da k’wayan halittar Maimartaba a mahaifar Raheena ba don komai ba sai don ya bayyana ishararsa da ikonsa. Ta yi murna sosai ta so kuma tona musu asiri sai dai sun garga’deta da muddin ta tona musu asiri kamar fasuwar nata b’aragurbin k’wan ne. Wannan yasa ta yi shiru ta kuma shiga bin kwakwkwafin ganin Cikin da Nene take da shi ya zube, lura da hakan da suka yi yasa suka kasa suka tsare suka hanata aikata hakan ta hanyar hanata shiga inda Nenen take.
Duk bayan kwana uku nake zuwa duban Nenen ba tare da ta san ni wacece ba saboda na kaurara muryata. Idan na je ina k’ok’arin kwantar mata da hankali da k’arfafa mata gwiwa ha’de da sata cin abincin da zai gina mata jiki ya kuma ginawa jaririn jiki. Har zuwa sanda cikin ya isa haihuwa abin al’ajabi duk da yawan scanning d’in da ake mata baa tab’a ganin y’an biyu a cikinta ba. Ni na bata idea ta sanar da su Nene ba zata iya haihuwa ba sai dai a mata theatre ba don komai ba sai don mu b’atar da tunaninsu. Suka amince da hakan don haka aka saka ranar theatre wanda a ranar ne suka yi nufin kashe Nenen bayan sun d’auke abinda ta haifa, na sanar da Doctor ta amince da abinda suka d’in. Da kai na na saka Doctor ta mata allurar janyo nak’uda sai ga shi cikin hukuncin Ubangiji ta haifo santalelen d’anta. Da kaina na yanke masa cibiya na kuma masa hu’duba da Suna Muhammad Murad sunan da Maimartaba ya da’de yana burin sanya wa d’ansa. Daga nan ne na umarci Nene ta gudu bayan na amshe d’an na kuma bata dukkan abin da zata buk’ata, Na saka wani driver ya kai ta bayan gari ba tare da sanin cewa yana sake bibiyar duk inda ta yi ba. Har haihuwar da ta yi ya sanar min ni na ce ya k’yaleta ta je ta raini abinda ta haifa kada dukan ya mata biyu. Har gidan da ta zauna na saka aka bibiyeta sai dai na k’i bayyana kai na Sabo da ina son nuna girman Allah a wajen mugayen mutanen. Ni na kai shi k’ofar masallachi a lokacin da aka d’auke ruwan sama. Daga nan kuma na koma inda na fito na fara shirin barin k’asar zuwa wani lokaci mai tsaho. Ban sake waiwayar gida ba sai dai na baza masu saka min ido akan dukkan abinda yake wakana wannan shine abinda ya faru tsawon wa’dannan shekarun ina fatan Maimartaba zai min afuwa akan k’aryar da duk na yi masa na mutuwa da kuma b’oye masa aurensa da Nene da na yi, ba don kowa na yi hakan ba sai don kai don kuma ka samu Magajin da ka da’de kana buri……
Wani irin annuri ne kawai yake fita daga fuskar Maimartaba yana cigaba da kallon Tauraruwa cikin tsananin k’aunarta da take sake rub’anya a zuciyarsa, ta sarayar da duk farin cikinta saboda nasa farin cikin ta bar yaranta guda biyu da ta san suna buk’atarta amma ta jinginar da su suka zama marayun k’arfi da yaji duk saboda cikar nata burin. Me zai ce da Tauraruwa ba shi da bakin gode mata don duk abinda zai furta sai yaga kamar ya yi ka’dan. Mik’ewa kawai aka ga ya yi hawaye na zuba a idanunsa ya isa har inda Tauraruwa take. Ya jawo hannunta kafin ya kira Murad da Jaheed ya nuna musu Tauraruwa yana furta “A yanzu da bayan raina ba ku da wata uwa da ta shige Tauraruwa ni da mahaifiyarku haifar ku kawai muka yi, amma itace silar zuwanku duniya, don haka na umarceku ku yi mata biyayya a cikin dukkan abinda ta umarceku sab’a mata kamar sab’a min ne, kuma ba zan yafewa duk wanda ya saka Tauraruwa a cikin bak’in ciki ba……” Ya juya idanunsa cikin Na Nene da ta yi saurin sunkuyar da kanta wani abu yana tsikararta tun daga yatsun k’afarta har zuwa kwanyarta, idanun Maimartaba sun mata kwarjinin da ba zata iya duban cikinsu kai tsaye ba. Murmushi ya saki kafin ya sake kallon gefen da sauran matansa suke, ya juya ya sake kallon Nene a hankali ya furta “A wani matsayi zan ajiyeki?”
JIKAR NASHE✍🏽🥳