← Book details Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 43

Sashe 28

Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kashegari ba yarda abokansa ba su yi da shi ba ya tashi su tafi d’aurin aure amma ya ce shi sam ba zai je ba, don ya Riga ya shirya abinda zai fishsheshi.. yana kallo Suka dinga tafiya yana sakin tsaki. Aka d’aura aure cikin mutane da dama da suke ziyarta don d’aurin aure ne da shelarsa ta karad’e duniya. Ana gama d’aurin aure dangin ango suka je don tafiya da amarya kamar yarda al’adar gidan sarautar gabas take da zarar an d’aura aure za a isa da amarya cikin gidan sarki inda za’a cigaba da gudanar da abubuwan bikunkuna iri iri. Da al’adu iri daban daban. Kuka Najwa kawai take kamar wacce za’a cire wa kai, aka kaita wajen Ummanta don ta mata fa’da sai dai Umman albarka kawai take saka mata don duk wani fa’da da nasiha ta yiwa Najwan ta yi da baki ta yi a aikace don a cewarta ba a fafe gora ranar tafiya. Don haka kanta kawai ta dafa ta ce “Allah ya miki albarka a gidan aurenki Najwa ya kauda dukkan abin k’i ya saka abokin zamanki ne har a Aljanna.” Daga haka ta saki kanta. Najwa kuma ta fa’da kanta tana sakin kuka da k’yar aka sake b’anb’areta daga jikinta suka fita tana wani irin gunjin kuka.

Sanda suka isa masarautar tuni an gyara sashen su an zuba kayan alfarma da alatu anan kuma zata kwana da mijinta washegari idan aka tabbatar ta kai budircinta sai a yi biki na ban mamaki a kuma karramata kwana uku za’a yi ana bikin.

Ita ka’dai ce a tsakiyar gadon d’akin nasa tana bin ko ina da kallo iya tsaruwa d’akin ya yi ya kuma tafi da imaninta ta ji an turo k’ofa da k’arfin gaske da sauri ta ja mayafi ta rufe kanta jin k’amshin turarensa kuma su Nene sun k’i barinta ta sake mayar da b’atacciyar fuskarta. Da takun Isa ya Isa wajenta cikin wata irin murya da shi kansa bai san yana da ita ba ya ce “Ba dai sun kafe sai sun aura min ke ba, suna da right su aura min ke amma ni nake da right na zama da ke ko akasin haka don haka a yanzu ma na gama yankewa zuciyata ba zan zauna da ke ba don haka karb’i nan…” Ya fad’a yana janyo hannunta ya saka mata takardar daidai sanda mayafin fuskarta ya sauka ya yi tozali da fuskar da take hana shi sukuni fuskar da take saka shi tunani da rashin barci da sauri ya wara ido yana furta “You? Dama ke ce?” Ya fa’da yana k’ok’arin fusgar takardar da ta damk’e a hannunta tana masa kallon cikin ido……. “Ba zan zauna da kai ba Murad ka saki aurenka…….”

JIKAR NASHE✍🏽🥳

(Labarin nan idan muka ce za mu yi shi gudu gudu ba zai muku da’di ba sai dai dole zan yanke wani sashen na labarin na baku shi yarda ya samu don duk kun fi son a gama kafin azimi, idan banda haka da sai nace ko zaku bari bayan sallah na k’arasa idan ba haka ba zan guntile labarin na sallameku a gobe.) ina jiran na ji ra’ayoyinku cigaba bayan sallah ko yinsa yarda ya sawwak’a a gama a gobe?)
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Ya sake kifa kansa a jikin Allon gadon yana kallon hannusa da tunano rubutun da ya yi da kansa na sakin a jikin takarda duk da saki guda ya mata amma yana ji a ransa kamar sun rabasu ne har abada don ya tabbata ko zai mutu Maimartaba ba zai dawo masa da matarsa ba don haka zuciyarsa take raya masa kamar sun rabu da muradin ransa har abada. So yake ya sake kiran Jaheed amma ya kasa don shi kansa Jaheed d’in kunyarsa yake ji.

Gumi ne mai yawa yake tsatstsafa daga jikinsa, wani irin yanayi yake ji me wuyar kwatance idanunsa shi kansa bai san suna zubar da ruwan hawaye ba. Wace irin k’addara ce wannan mai girman gaske take bibiyar rayuwarsa? Runtse idanunsa ya yi a hankali yana furta sunan Allah a zuciyarsa don ya san shi ka’dai ne zai kawo masa sauk’i a
Cikin dukkan lamarinsa.

Jaheed kansa da bashi ya yi sakin ba yana jin fiye da yanayin da Murad yake ciki, wani ganganci ne ya kai Murad d’in da aikata irin wannan abu? Da wani ido zai dubi iyayensu ya yi musu bayanin tarin laifukansa ya yi tsaki yafi a k’irga kafin ya janyo wayarsa ya shiga kiran numberr Nene. Tana zaune akan sallayar ta dinga jin k’arar kiran wayar jikinta na rawa ta d’au wayar ganin Jaheed ne tsoronta d’aya faruwar wani mummunan lamari don kiran ya yi tsakar dare da yawa dole kana jin irin wannan kiran wayar na tsakiyar dare ka tabbatar da rashin wanzuwar lafiya. Muryarsa da ya ji tana rawa ka’dai ya isa ta gasgata hasashenta don haka ta runtse ido kawai itama tata muryar na rawa ta ce “Murad! Ya mutu ko?” Don haka kawai mummunan mafarkin da ta yi da shi yake bata baya cikin lafiya don mafarkin ya bayyana mata Murad d’in a wani irin yanayi da bata k’aunar ko a tunani ta sake arba da shi. “Gaya min Jaheed na rasa Murad ko?” Ya ja ajiyar zuciya yana jinjina girman tasirin Soyayyar Uwa ga yaranta soyayyace da babu ta biyunta. “Bai mutu ba, ba kuma abinda ya sameshi.” Ta ja ajiyar zuciya ba tare da ta gasgata abinda yace d’in ba sai don ba yarda zata yi da shi. Amma a jikinta ta ji ba lafiya ba. Shiru na tsawon minti guda kafin Jaheed ya runtse idonsa ya ce “Ki masa addu’a Nene tsautsayi yasa ya saki Najeee…” wani irin dum ta ji a idanunta bata san sanda ta saki wayar ba cikin tashin hankali ta furta Ya ilahal alameen! Wani lamari nake ji wannan mara dad’in ji. Kawai sai ji ta yi hawaye na zuba a kwarmin idanunta kuka sosai yake na zahiri da na ba’dini mai bayyana irin k’una da k’uncin da zuciyarta take ciki. Me yasa Murad zai aikata haka da wani idon yake son ta kalli Baffa a karo na biyu y’ay’anta na cikinta suna sakar masa y’ay’a? Anya sun masa adalci kuwa? Irin sakayyar da ya kamata su masa kenan? Mik’ewa kawai ta yi tsaye ta fara ha’da kayanta. Ba zata iya zama wannan zancen ya riski Baffa a idanunta ba, bata da jumirin iya jure ganin tashin hankalin da zai shiga. Wayar ta ta d’auka ta kira Jaheed murya a d’ashe alamar kukan da ta yi ya yi nisan zango ta ce “Saki nawa ya mata?” “Duka” ya furta kamar yarda Murad ‘din shima ya gaya masa. D’if ta kashe wayar tana jin wutar da take cin zuciyarta tana sake zafafa. Bata san irin horo da rashin mutuncin da zata yiwa Murad ba. Hukunci d’aya ta yanke a kuma goben zata aiwatar da komai In sha Allah. Ta ji zuciyarta ta aminta da shawarar da ta bawa kanta da kanta. Tsaf ta ha’da kayanta iya wanda ta san zata buk’ata don
Asubar fari take son tafiya Masarautar Gabas.

Ai kuwa ana idar da sallahr kafin a kai ga sake gark’ame gate d’in ta yi fit ta fice daga gidan cikin sauri da azama don bata son wani ya ganta balle ya tsayar da ita. Burinta isa masarautar.

K’arfe 9:00 cif a cikin masarautar ta mata ta bar kayanta a cikin motar da ta yi shata ta fa’da cikin masarautar da sauri. Shiru ba wani hayaniya daga wajen masarautar bata yi wahalar gane sashen Murad ba don dama ta san shi. Ta isa kai tsaye ga sashen da ya sha kyau kamar ba a Nigeria ba. Ganin da fadawa suka mata kai tsaye suka shaidata don haka basu wani hanata shiga sashen ba ta shiga kanta tsaye cikin k’aramin parlourn da zai sadaka da d’akunan Barci. “Murad!” Ta shiga kiransa da k’arfin gaske.

Wata irin fa’duwar gaba ce ta sameshi ya dafe k’irjinsa jin muryar Nene na kiran sunansa. Haka ya mik’e yana jin jiri ya fita parlourn daga shi sai singlet da wando three quater gashin kansa da yanayin idanunsa kawai zaka kalla ka san baya cikin walwala saboda yarda suka banbanta da yarda suka saba kasancewa a lokutan baya. Kallo d’aya Nene ta
Masa ta hango tashin hankali a cikin idanunsa sai ta runtse nata idon ko ka’dan bata son tausayinsa ya rinjayi hukuncin da zata masa.

Durk’ushewa ya yi a gabanta ya kama k’afafunta cikin hawaye ya hau furta “Pls Nene! Wallahi a rashin sani na saketa ban san ita bace….” Kafin ya kai k’arshe Nene ta wankeshi da mari cikin b’acin rai ta dinga zuba masa
Mari bai yi ko motsiba ya dai runtse idanunsa har sai da ta gaji don kanta sannan ta
Zube a kujera tana haki “Kanka ka cuta Murad ba Najee ba, na kuma godewa Allah da ka saketa kafin ka karb’e budurcinta zan yiwa Najee auren gata auren mutumin da zai sota don Allah ba don ita mummuna ko kyakykyawa bace. Kai kuma ka je ka auri hurul aini ma idan akwaisu a duniya ba zan maka baki ba amma ka rubuta ka ajiye har abada ba zaka samu macen da ta kai Najee a komai da komai ba. Zan d’auke Najee idan ta gama idda zan aurar da ita a inda aka san darajarta!” Daga haka ta mik’e cikin b’acin rai ta fice daga parlourn Murad idanu ya runtse kawai yana son kiranta sai dai ba shi da k’arfin da zai iya hakan. Zuciyarsa ta raunana irin raunin da ya bayyana har a kan fuskarsa da gangar jikinsa. Don haka kawai ya zube a saman carpet hawayen ma ya k’i zuwa kamar yarda yake so don haka kawai ya runtse idanunsa yana jin yarda hajijiya take d’ibansa duk da a kwance yake.
Chapter 28 · 0% Book details