← Book details Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 43

Sashe 12

Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“A yau ya kamata mu isa wajen mai martaba mu bayyana Nene a matsayin wacce ta haife mu.” Jaheed ya fa’da yana kurb’ar ruwan tataccen inibin da yake hannunsa. Fulani ta girgiza kai duk da ita ta san abinda ba su sani ba game da Tauraruwa hakan bai sa ta k’i mara musu baya ba, itama burinta kenan jin yarda aka samar da cikin a jikin Nene. “Hakan shine ya dace, amma ku fara cin abinci mana musamman su da suka d’auko gajiya ka kai su can sashenka su yi wanka su huta idan Maimartaba ya fito daga sallar azahar sai mu rankaya mu tafi.” Kowa ya amince da shawarar Fulani don haka suka bi Murad ita kuma suka cigaba da tattaunawa da Nene da itama ta san wani abu game da Tauraruwa wanda su ba su sani ba. A yau kuma Nenen zata bayyana kanta a matsayin mahaifiyarsu tunda ba wanda ya san da zamanta a masarautar ta san zuk’ata da dama za su shiga mamaki da tambayar yarda aka haihu a ragaya.

____

A fusace ta mik’e tana duban amintacciyar baiwarta da ta kawo mata labarin iso war Jaheed masarautar. “Tsananin kamaninsu ya b’aci uwargijiyata duk wanda ya kalleshi ba sai ya tambaya ba zai san jinin Yarima mai jiran gado ne…..” wani kyakykyawan mari ta zuba mata a k’unci tana fesar da hucin b’acin rai ta furta “Mai jiran gadon Ubanki? A gabana kike furta wannan bak’ar maganar, ina so ki rubuta ki ajiye ko zan yi yawo tsirara Murad ba zai mulki al’ummar gabas ba, balle wani d’an uwansa da bai tashi a gidna sarautar ba ma… Fice min daga d’aki….” Sum sum ta fice daga d’akin zuciyarta cike da jin d’d’acin abinda Uwargijjiyar tata ta mata. Fulani Raheena ta bita da kallon banza kafin ta mik’e a hanzarce ta bu’de wardrobe d’inta. Hotuna ta binciko wanda aka iso mata da su a daren jiya ta bi hotunan da kallo duk da shekarun da suka d’auka suna nan kar da su ana gani ba abinda ya goge a cikinsu. Murmushi ta saki a zahiri ta furta “k’aryar Ki ta sha k’arya tauraruwa mu zuba ni da ke, yanzu aka sosa wasan.”

Ta isa gaban mudubi ta d’au wata kwalbar turare ta shafa ta gyara fuskarta sosai. Fadar Maimartaba take son zuwa tafi son a yi komai a gabanta ko ba haka ba kuma tana son tarwatsa farin cikin Tauraruwa ta Kuma bayyana gaskiyar abinda tauraruwar take son ta hak’a ta birne. Hotunan ta tura cikin aljihun alkyabbarta sannan ta zura takalmin ta. Ta k’ofar baya ta fice don isa ainahin sashen Maimartaba.

Tun a k’ofa wasu fadawa biyu suka tsayar da ita ha’de da sanar da ita Tauraruwa ta bada Umarnin kada a bar kowa ya shiga sai da izinin ta. Cikin mamaki take kallonsu murya a sark’e ta ce “Baku gane ni ba ne?” Sunkuyar da kai suka yi suna furta “Mun gane ki ranki ya da’de sai dai anan wajen umarnin tauraruwa gaba yake da naki..” Hucin numfashi ta saki zuciyarta na sake fusata kamar ta make shi sai kuma ta ce “Ka je ka gayawa Tauraruwar ni nake son ganin mai martaba.” Ta fa’da tana jin wani takaici na shak’e wuyanta. Da sauri ya nufi ciki don cika umarnin ta. Tsawon mintuna kafin Tauraruwa ta d’ago tana kallonsa ta ce “Je ka kace ta shigo.” Mai martaba yana zaune bai ce komai ba duk hankalinsa yana kan ganin Jaheed da Tauraruwa ta sanar da shi zuwansa. “Jaheed zai shigo amma ina son mu fita da ni da kai waje gaban jama’a don kowa ya gan shi ya shaida jinin mu ne, ina son kuma nunawa jama’a wani abu.” Ta fa’da idanunta cikin na Sarkin da yake kallonsa ko k’iftawa bata yi, sai dai wannan karan fuskarta a gintse take ba fara’a ko ka’dan da alama akwai wani abu da ya b’ata mata rai. Sarki ya d’aga kai kawai alamar ya yarda da abinda ta ce. Fulani ta shigo fuskar nan a ha’de ba alamar fara’a balle dariya. Wani kallon tsana take jifan Tauraruwa da shi ita kuma Tauraruwar ko kallonta bata yi ba hankalinta na kan bafaden da yake isarwa da sak’o ya je ya sanar a farfajiyar masarautar. Tana gama abinda take kuma bata ko kalli sashen Fulani ba ta mik’e ta shige cikin bed room d’inta tana ji a ranta lokacin fasa b’aragurbin k’wan Fulani Raheenan ya yi, don tana lura da kallon da yake mata.

Shiru harabar masarautar don haka sanarwar da ake a loudspeaker ta isa kunnuwan duka jama’ar masarautar. Dama haka suke so don haka kafin kace me ye wannan babban filin ya cika mak’il da jama’a har da na waje ma sun shigo don ta waya aka dinga sanar da su neman da Sarkin gabas yake wa mutane, dama abinda suke jira kenan.

Sarki ne ya fara fitowa shi da Fulani Raheena da ta fito itama daga parlourn bayan fitowarsa. Cikin takun isa ta zauna a wajenta. Sai da kowa ya zo har Jaheed Murad da Fulani Saddik’a banda Nene. Sannan Tauraruwa ta fito cikin shigar alfarma da ta d’auke tunanin hankalin jama’ar wajen. Kallonta kawai ake ana ganin kamannin y’an biyu a tare da ita. Bata zauna ba ta karb’i loud speaker ta yi sallama cikin murya mai cike da nutsuwa ta furta “Alhamdulillah Alhamdulillah yau rana ce mai matuk’ar farin ciki a tare da ni, ranar da na da’de ina jira ranar da zan nuna jinin Maimartaba da nawa, a lokutan baya mun sare mun karaya mun fitar da ran samun Magaji sai dai cikin hukuncin ubangiji sai Allah ya mana kyautar da ba mu yi tsammani ba kyautar yara biyu wanda ga su nan a zaune Murad da Jaheed, Jinin mai martaba ne haka nan jini na ne yake yawo a jikinsu ma’ana su ne Jininmu yaranmu da muke alfahari da su…….” “Mu ba yaranki ba ne, ga Mahaifiyar mu nan.” Murad ya fa’da yana nuna Nene da take gefensa gaba d’aya hankulan jama’a ya koma kan Nene da yake tsaye daf da Murad…….

JIKAR NASHE.✍🏽🥳
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Maimartaba ma da gaba d’aya hankalinsa baya wajen yana kan Jaheed da ya zubawa ido yana mamakin kasancewarsa d’ansa, ya mayar da kallonsa kan wacce aka kira mahaifiyarsu. Wata irin fa’duwar gaba ta sameshi ba don komai ba sai don bai santa ba bai tab’a ganinta ba ta yaya zata zama Uwar y’ay’ansa? Me Tauraruwa ta shirya haka ne? Ya tambayi kansa duk da ya san bai da amsar don haka ya mayar da kallonsa kan Tauraruwa da take ta kallon Murad tana sakin murmushi ta furta. “Ba zan ce maka komai ba, amma ko yanzu aka tsaga jikinka za’a tarar da Jinina baka son komai ba yaro shi yasa ka ke tunanin da kake yanzu….” Ta juyar da kallonta kan Maimartaba da gaba d’aya hankalinsa yana kan Nene da take tsaye tana rawar jiki. Itama idanunta ta sauke cikin na Nene kafin ta matsa daf da ita Nene ta sake shak’ar k’amshin turaren da ya zauna ra’dam a hancinta tun shekarun da suka wuce da alama kuma har yanzu Tauraruwar bata canja turaren ba. Kallon da Tauraruwa ta mata yana nuni da kin manta da alk’awarin da kika min na ba zaki sake dawowa masarautar gabas ba ko? Kin manta gwalawalan da na baki don ki nesanta kan ki daga masarautar gabas? Me yasa kika dawo? Kin shirya mutuwa kenan? Wad’annan sune fassarar da ta yiwa kallon Tauraruwa don haka zuciyarta ta shiga bugu da sauri kamar yarda gabban jikinta suke kakkarwa tsoro da razana suka bak’unci sassan jikinta da ma zuciyarta gaba d’aya. Da sauri ta sunkuyar da kanta duk da Tauraruwa ta b’oye kamanninta a wancan lokacin ita kuma zuciyarta ba zata tab’a kawo mata Tauraruwa ce ba saboda labarin rasuwar ta a lokacin ya da’de da karad’e masarautar gabas, ba mamaki da ace ta bayyana kanta a lokacin tsananin firgitar da zata yi zai iya sanadiyyar rasa ranta, da ba ma sai ta wahalar da kanta da gold ba balle har ta umarceta da tafiya mai nisan da ba zata sake wai wayar masarauta ba. Shiru da ta yi da rawar da jikinta suke shine dalilin da ya janyo mata idanun jama’a kanta. Murad ya ja hannunta zuwa kujerar da ke gefen Mammansa so yake zuciyarta ta samu nutsuwa baya son ta saka tsoron da zai sa ta kasa kwatar y’ancinta. Duk da iya ahalin masarautar ne a k’aramin filin fadar mutanen waje suna ainahin babban fili bai hana ihun da ake shigowa cikin fadar ba, mutane suna fa’din yau dole ne su san gaskiya.

Tauraruwa ta lumshe idonta bayan ta sake damk’e speakerr hannunta murya a nutse ta fara jawabi.

Ga duk wanda ya san ni ya san ni da soyayyar mai martaba a rayuwata, ya kuma san yarda muke sadaukar da farin cikin junanmu don wanzuwar farin cikina ko mai martaba. Rasa Magaji da mai martaba ya yi a wancan lokacin shine abinda ya dugunzuma hankalina yake kuma hana ni barci a kowane daren duniya. Mafita nake nema masa ko nace nake nema mana don duk wani abu da zai damu Maimartaba kamar ya shafi tauraruwarsa ne, kamar yarda ya sha fa’da a mabanbantan lokuta, Ni ce farin cikinsa ni yake burin sakawa a farin ciki a koda yaushe, nima Kuma haka yake a wajena burina samun farin cikin mai martaba ko da ni nawa farin cikin zai yi k’aura. A wannan lokacin ban damu da kai na ba. Kwatsam sai aka wayi gari Raheena ta samu ciki. Ni na bi diddigi na hango cikin da Raneena take d’auke da shi ba halastaccen d’an sarki ba ne, don haka a duk sanda zata haihu ni nake ha’da baki da Jakadiya mu saka mata gawar jariri mu sace d’an da ta haifa……
Chapter 12 · 0% Book details