Sashe 32
Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsaf ta shirya duk da turtsetsen cikin da yake jikinta bai hanata fesa kwalliya ba da adon mai ban k’aye murnarta da zakwad’in da zuciyarta take ciki suka kasa b’uya a fuskarta sai zuba fara’a take tana jin yau rana ce mai girma da tarihinta ba zai gobe a zuciyarta ba. Ranar da zata koma gidan Jaheed mutumin da take wa wani irin so da kai tsaye ba zata taskance shi a mizaninta ba, abu guda ta sani son da take masa ya huda duk wani bigire na zuciyarta. Najma kenan da take tsaye tana sake fesa turare a jikinta duk da gabbasar da kayan ta sha bai hanata sake saka Humra ba.
Mahmeey kallonta kawai take tana murmushi duk wannan cunkushashshiyar fuskar ta Najma yau ta washe ta zama fuska mai cike da murmushi da tarin annashuwa. “Ki nutsu dai Najma ki ja ajinki kada ki yi abinda zai rainaki ni da don Baffa ya k’i ne da bari aka yi sai kin haihu…” “A’a Mahmeey gwara na koma idan kuma na mutu fa bana gidansa gwara ko mutuwar zan yi ya kasance ina tare da shi a kusa da shi….” Mahmeey ta d’alle bakinta tana furta “Sau nawa Zan gaya miki bana son zancen mutuwar nan?” Najma ta yi murmushi kawai ta d’an rungumeta ta ce “Ki min addu’a Mahmeey Allah ya raba ni da cikin nan lafiya yasa ni zan raineshi da kai na ba wata ba… Duk da sai na dinga ji a jikina kamar mutuwa zan yi..” Mahmeey ta d’an rungumeta tana basar da zancen ta ce “Maza ki je ki ywa Umma sallama Baffa na jiranki zai kai ki da kansa har gidan yace don yana son ha’daku da abokiyar zamanki ya muku nasiha…” Ta ja ajiyar zuciya tana tunano idanun Khaireey da take mata wani wulakantaccen kallo ranar da ta ji Mijinta zai mayar da ita….. ko wane irin zama za su yi? Shin ko zata yi tsawon rayuwar da zasu zauna zaman kishin?
JIKAR NASHE🥳
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Hankalinsa tashe yake kallon yarda idanunta suke jikirtawa zuwa launin da yake nuna jigata da d’imauta da gaske ko wane irin ciwo ne yake damunta yana da zafin gaske… gumi take tsatstsafowa daga dukkan sassan jikinta don haka hankalinsa a tashe ya d’au waya ya shiga latsawa da bincikar family doctor d’in su na gidan Baffa. Sai dai kafin Doctorn ya d’ago ya hango yarda Najma ta sassank’ame alamar da gaske ta mutu ko kuma ta yi doguwar suma. Bai san sanda ya yi wulli da wayar ba ya rarumi rigarta ya zura mata yana aikin kiran sunanta sai dai ba alamun ta ji balle ta amsa. Bai san sanda ya wuntsila daga gadon ya zura tasa rigar ba duk ya ru’de ya gigice fatansa da addu’arsa Allah yasa Najma dogon suma ta yi ba mutuwa ba. Cak ya d’auketa bai yi la’akari da girman cikinta ba balle ya ji nauyinta burinsa ka’dai isa asibiti don samun ceto lafiyarta da ta abinda yake cikinta. A bayan mota ya saka ta yana cigaba da bubbuga bayan ta don kiran sunanta amma bai ga alamun motsi ba ko ta kan Khaireey bai bi ba ya ja Motar a sukwane ya fice daga harabar gidan bayan mai gadi ya bu’de masa gate……
Ko kafin su isa asibitin ya kira Umma ya gaya mata itama a ru’de ta sanar da Baffa, Baffa k’irjinsa ya nufa sosai haka kawai sai ya ji tsoro da firgita ba bin sassan jikinsa yana tsoron rasa Najma a lokacin da ta zama Saliha yarinya ta gari kamar yarda burinsa yake a koda yaushe. Ba su gayawa Mahmeey ba suka mik’e da sauri don nufar asibitin da Jaheed ya ce suke.
Kafin zuwansu asibitin tuni Family Doctornsu ya saka an shirya musu d’aki da duk abinda zasu buk’ata, don haka suna isa aka zo da wheelchair don isa da ita kafin su shiga d’akin har likitan ya fito daga office d’insa a k’agauce ya fa’da d’akin ya turo k’ofar da saurin gaske… wanda bugun k’ofar ya yi daidai da bugawar zuciyar Jaheed ya fara jin tsoron sa na sake hauhawa kawai sai ya samu kansa da runtse idonsa da mugun k’arfi yana jan hasbunallah a cikin zuciyarsa….
_____________
A bakin k’ofar gidan ta tsaya kafin ta kalli Najwa da itama take Tsayen tana jiran jin umarni na biyu da Nene zata bata. Nan dai gidan Kakarta ce Hajja wacce ta kasance k’anwa ga Mahaifiyar Umma don haka ba wani tsoro ko shakka da zata ji na zamanta anan…. Nene ta ce “Mu shiga Najee anan na fi buk’atar zamanki bana son kuma ko mutanen gidan ki gaya musu dalilin kasancewarki anan d’in ina son ya zama sirrri daga ni sai Ke zan zo na d’auke ki bayan kwana goma da zarar na tare a fada..” Najee ta jinjina kai kafin su saka kansu cikin Babban zauren gidan a share yake tas ko abinka ne ya fa’di zaka iya durk’usawa ka d’auka ka ci kayanka. Najee ta cigaba da jan k’aramin trolley d’inta zuwa cikin gidan. Suna sallama a tare da Nenen. Sai ga d’aya daga cikin Surikan Hajjan ta fito tana amsa sallamarsu. Ganin Najwa da Nene a tsaye sai ta saki baki tana kallonsu don dai idan bata manta ba shekaranjiya suka dawo daga bikin Najeen to me ya kawo su? Fahimtar hakan da Nene ta yi ya saka ta sakin murmushi ta ce “Iyami kin gan mu rana tsaka ko?” Iyami ta d’aga kai don da gaske tana neman k’arin bayanin. “Mu shiga ciki tukunna kin san abinka da gidan sarauta tafiya ce ta kama Mijin to shine ya rok’i alfarmar na kawota nan na ajiye kada a fahimci tana nan d’in Kuma don an rasa visa dinta, idan kuma aka fahimci baya nan za’a iya cutar masa da mata kin ga dalilin zuwan mu Kenan Ina Hajja?” Iyami ta saki ajiyar zuciya kuma ba wani kokwanto zuciyarta ta amince da abinda Nenen ta ce don bata ga dalilin da zai saka Nenen ta mata k’arya ba. “Lamarin gidan sarauta kam abin tsoron ne musamman ga k’aramar yarinya kamar Najee gaskiya ya yi dabara Allah ya dawo da shi lafiya Hajja na ciki ku k’arasa.” Nene ta saki ajiyar zuciya tana jin da’di da Iyami bata gano k’aryarta ba, suka shiga d’akin Hajja wanda ya kasance parlour ne Babban gaske mai d’auke da d’akunan kwana uku da kitchen da toilet a ciki. Hajja ta amsa sallamar ta su idanunta akan Najee ta ce “Wa nake gani haka kamar amaryar da aka wa aure a satin nan?” Nene ta zauna a gefenta suka gaisa sosai da Hajjan da yake akwai Sabo mai girma a tsakaninsu, nan itama ta sanar da ita abinda ta gayawa Iyamin.
Hajja ma ba wani ja in ja ta amince da abinda Nenen ta sanar mata. “Yaro kam ya yi farar dabara gidan sarauta lamarin su sai addu’a Allah ya dawo da shi lafiya Ai sai ta zo ta share d’aki tayi zamanta na samu me yi min tausa…” Nene ta yi dariya sosai dariyar da ta bayyana zallar murnar da zuciyarta take ciki na yarda da abinda ta ce wa Hajja. Nan ta yi alwala ta yi sallar da ake bin ta don dole ta zauna aka yi La’asar kafin ta musu sallama ta barwa Najee ku’di masu yawa ko Zata samu abinda take son siya. Sannan ta tafi tana sake jaddada kwanaki goma kawai Zata yi da yardar Allah zata dawo ta d’auketa. Najee bata ji komai ba ta ce “Allah ya dawo da ke lafiya My Nene..”
Sai 9:00 na dare Nene ta koma gidan Baffa a lokacin kuma ta tarar da rashin lafiyar Najma har ma mutanen gidan duk sun tafi asibiti hankalinta tashe itama ta juya don nufar asibitin da suka je don ba bak’onta bane ta san asibitin Nahdi farin sani….
Napep na sauketa ta isa cikin asibitin bata sha wahalar ganinsu ba, Jaheed yana ganinta ya mik’e da sauri ya nufi wajenta. Idanunsa Nene kawai ta kalla ta tabbatar yana cikin matsananciyar fargaba da tashin hankali, sai ta ji tausayinsa mai girma ya fisgi zuciyarta ta d’an lumshe ido tana jan addu’a a ranta kafin ta ware idon a kansa ta ce “Addu’a itace maganin dukkan wata masifa me ya sameta Jaheed?” Tattausan kalaminta yasa ya ji ya samu nutsuwa ka’dan a ransa ya lumshe nasa idanun sai ga hawayen da yake ta dako yana b’oyesu a kwarmin idonsa sun samu damar sauka suna zarya akan k’uncinsa bai san sanda ya damk’i hannunta ba ya kifa kansa a tafin hannun kafin ya fara magana cikin wani irin sauti mara amo ya ce “Ki mata addu’a Nene bana son na rasa ta ina son ta Nene…” Nene ta saki ajiyar zuciya sai ta ji itama gabanta ya wani irin bugawa da k’arfin gaske irin bugun da sam bata son ya yi don idan ta yi irin hakan ta san akwai wani abu mai girma da zai faru… Innalillahi ta furta can k’asan ranta kafin ta furta “Khairan In sha Allah Jaheed ba zamu rasa Najma ba alfarmar Manzo s.a.w….” Jaheed ya amsa da ameen yana furta Allah yasa Nene… ta d’an janye hannunta ganin Umma ta nufo su tana kallon Nenen da sam bata son su ha’da ido kamar akwai wani abu da take son b’oye mata. Umma ta janye hasashenta sannan ta furta “Nene yau ina kika shige ne? Tun safe ban gan ki ba…” Kafin Nenen ta amsa fitowar likitan da yanayin yarda ya buga k’ofar da k’arfi yasa numfashinsu ya tsaya cak na wuncin gadi zuciyarsu ta buga da k’arfin gaske a tare suka fara jan addu’oin da duk suka zo bakinsu don fuskar likitan kawai zaka kalla ka tabbatar da abinda yake son ya furta cikin zuciyarsa ba sai ya furta ba sun san sun rasa Najma!
JIKAR NASHE🥳🤗