Sashe 33
Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A cigaba da hak’uri da ni kun san nace mutuwa aka mana yanzu ma ina dawowa na hau typing Uba ne a wajena ya mutu ku saka shi a addu’oinku shi da duk musulmi da Suka riga mu gidan gaskiya
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: D’an cije leb’ensa likitan ya yi, lokaci guda kuma ya furzar da huci daga baki da hancinsa ya d’an juya gefen damansa yana kallon Baffa da ya yi zugum yana jiran bayani daga bakin likitan “Allah ya amshi ran Najma!” Shine abinda Baffa yake jiran ji kawai daga wajen likitan. “Baffa zan iya magana da kai?” Doctorn ya fa’da yana kallon Baffa da alamun rashin nutsuwa ya bayyana a cikin idanunsa.. Gaban Baffa ya fa’di kamar yarda duk na mutanen da suke wajen ya fa’di jikinsa a sanyaye ya ha’diye yawun da ya tara a bakinsa. Jaheed kuwa lunshe idanunsa kawai ya yi yana zubar da zazzafar k’wallar da yake jin zafinta da d’acinta a mak’ogoronsa. Baffa ya d’aga kai yana yak’i da jirin da yake son fara d’aukarsa. Doctor ya d’aga kai yana juyawa zuwa Babban Office d’insu. “Ku taho da Jaheed d’in Baffa…” Baffa ya kama hannun Jaheed da ya zama kamar wani mara ji mara gani kawai bin Baffa yake duk inda ya saka k’afarsa shima hulla tasa ya ke. Suka isa office d’in Doctorn da yake fitar da wani sassanyan k’amshi da sanyin ac mai k’arfin gaske. “Ku zauna” ya ce da su ganin ba su da niyyar zaman. Da k’yar suka zauna d’in Jaheed yana ji a ransa kamar ya hau likitan da duka. “Fa’da mana kawai Doctor Ba Najma ba kuma abinda yake cikinta.” Girgiza kai Doctor ya yi “Ba haka ba ne, tana da ranta amma tana cikin wani yanayi da ya kamata a yi gaggawar ceto lafiyarta don haka muke buk’atar amincewarku a mata aiki don ceto rayuwarta da ta yara biyu da suke cikinta….” Ya fa’da yana turawa Jaheed dogon file d’in da yake gabansa na Najma tunda anan take antenatal duk wani record nata suna da shi. Da sauri Jaheed ya saka hannu a aljihun da ya ciro biron ya rattaba hannu yana sakin ajiyar zuciya. Doctor ya ba shi takardar da zai je reception’s ya biya duk wani abu da ake buk’ata ya mik’e da sauri ya fita shima Doctorn fita ya yi da saurin da basu da lokacin b’ata lokaci. Suka dawo nan wajen su Umma suka sanar musu nan suka zauna zaman jigum suna jiran a fito da addu’oin samun nasara a bakunansu.
Ba b’ata lokaci aka mata theatre, aka ciro kyawawan yara maza biyu masu kama da iyayensu sak. Likitan ya saki ajiyar zuciya yana kallon Najma da take idonta a rufe don allurar barci suka mata. Ya d’an duba bugun zuciyarta ya tabbatar da lafiya sai ya saki ajiyar zuciya. Aka gyara yaran tas kafin a nad’e su a showel aka fito da su. Sanda aka iso da su Jaheed suman zaune ne kawai bai yi ba, so yake kawai ya ga Maman yaran hankalinsa bai kwanta ba sai da Doctor ya tabbatar masa tana nan lafiya amma tana buk’atar hutu sosai. Ya saki ajiyar zuciyar da duk mutanen wajen sai da suka ji. Kowa ya fara masa dariya Baffa ya mik’a masa d’aya da nurses suka tabbatar masa shine Hassan yace “Amshi takwarana Mujaheedu amshi Ibrahimul Khaleel.” Jaheed ya saki murmushi cikin jin kunyar da ta bayyana akan idanunsa ya saka hannu ya amshi yaron da yake tsananin kama da shi. Bakinsa ya d’ora a kunnensa a take ya masa kiran sallah ya kuma jaddada sunansa na Khalilullahi kamar yarda Baffa ya saka masa. Ya mayar da shi hannun Baffa yana fa’din “Baffa ga takwaran naka.” Sannan ya amshi Usaini a wajen Umma shima a take ya saka masa Muhammad Mukhatar sunan Mai martaba sannan ya mik’awa Umma shi ya na furta “Ga Magajin mai garin Gabas.” Hankalinsa ya koma kan k’ofar da ake fito da Najma barci yake amma hannunta d’auke da k’arin ruwa. Da sauri ya k’arasa
Wajen yana kiran sunanta sai dai bata san ma yana yi ba. Aka zarce da ita d’akin hutu daidai lokacin da ake kiran farko na Asuba.
A gefen gadon ya zauna don an sanar masa baa son hayaniya su Kuma su Umma suna wani d’aki da yaran tuni kuma suka fara sanar da mutane ta waya duk wanda aka gayawa sai
Ya hau murna. Jaheed da kansa ya kira Murad lokacin yana zaune a gefen sallaya ya idar da nafila hannunsa d’auke da waya yana aikata abinda ya saba na kallon hoton Najee da ya cika screen d’in wayarsa. Wayar na ringing zuciyarsa na wani irin fusga da zafin soyayyar Najee. Ya runtse idonsa kafin ya kara wayar a kunnensa yana ture haushin Jaheed d’in da yake ji na k’in taimakonsa da ya yi. “Uwargidana ta haihu ina ka shige ne an haifa maka twins…” Murad ya ware ido yana furta “Are you sure?” Jaheed cikin farin ciki ya sake tabbatar masa “Ka bu’de whatsapp d’inka I will send you their pictures.” Da sauri ya kashe wayar ya kuma hau whatsapp d’in sai ga hotunan kyawawan yaran sun cika screen d’in wayarsa. Da wani irin murna ya ce “Wow Ma sha Allah, Ya Allah kasa wata rana ni da Najee mu ga namu haka.” Ya fa’da yana lumshe idonsa sai ya samu kansa da imagining wai ga Najwa ta haifa masa twins har ya tsira mata ido tana ba su Nono tana sinne kai tana harararsa yanayinta na tsiwa yana nan. Ajiyar zuciya ya saki a fili ya furta “Ya Allah!” Wata y’ar k’walla ta gangaro masa da bai san da ita ba. Hoton ya yi uploading a status d’insa sannan ya kashe data ya sake kiran Najeen sai dai still bata shiga ba nan ya fara tunanin ko dai ba numberrta ba ce? Ya d’an ja guntun tsaki.
Kafin asuba haihuwar Najma ta
Karad’e masarautar gabas kowa murnar sa ta kasa b’oyuwa musamman Tauraruwa da mai martaba nan da nan aka fara shirin tafiya Kano don ganin jarirai da kuma rok’on iyayen Najma ta dawo cikin masarautar ta yi jego don a mata sunan da baa tab’a irinsa ba. Ba su san Najman ma har a lokacin bata farka ba. Kasa fita ya yi daga d’akin ya mik’e ya shiga toilet alwala ya yi yazo ya tada sallah a d’akin so yake da zarar ta farka ta gan shi.
Bata farka ba sai k’arfe 9:00 na safe lokacin duk an cika asibitin ba wanda bai zo ba idan ka d’auke mai martaba sai Fulani Saddik’a amma Tauraruwa ma tana cikin tawagar. Nene dai ba shiri ta zame ta koma gida don dai da kunya a ganta a asibiti wajen jikokin Fari don haka ba wanda ya san ta silale ta fice daga asibitin.
Hana kowa shiga d’akin ya yi don likitan ya gaya masa baa son ta farka ana hayaniya. Don haka ya kasa ya tsare yana zaune hannayensa cikin nata, duk wani jan numfashinta da sauke shi akan idonsa take. Cikin ikon Allah ya ji ta yi salati tana ware idonta a hankali a kansa. Wata irin ajiyar zuciya ya saki yana matsa hannunta ya ce “Alhamdulillah Najma are you okay now?” Hannunta ta kai kan cikinta sai ta d’ago ta kalleshi a hankali tana furta Babyn ya mutu ko?” Girgiza kai ya yi kafin ya kai bakinsa kan goshinta ya sumbata a hankali yana furta “Kada ki yi magana da yawa C.S aka miki.” Sai a lokacin ta ji zafin cikinta da sauri ta d’an lumshe ido ta ce “My J, ka gaya min Babyn babu ko?” “Ina zuwa” ya furta a hankali yana fita da d’an sauri daga d’akin. Mutane suna ganinsa suka mik’e aka fara tambayarsa “Yaya ta farka?” D’aga musu kai ya yi “Ku bani Babies d’in na kai mata…” HASSAN ya fara d’auka Nasma ta d’au Usaini ta bi shi suka koma cikin d’akin. Najma na ganinsu da yara a hannu ta d’an ware ido tana furta “My J, Twins ne?” Ya d’aga kai wata ajiyar zuciya ta saki da sauri. Ya saki murmushi yana lakace tsinin hancinta kafin ya kara mata Baffa k’arami a fuskarta “Gaya min da wa suke kama?” Lumshe idonta ta yi alamun kunya na bayyana akan fuskarta. “Bar su na gansu.” Dariya ya yi ya ce “Nasma ji min mata ita fa ta dameni wai sun mutu kuma an kawo zata min gwallin kunya, kada dai kice yarda aka samesu da k’iyayya har yanzu ba kya son su.” Turo bakinta ta yi irin na yarinta ta furta “Bana so My J…” murmushi ya saki bai ji kunyar Nasma ba ya kaiwa cute lips d’inta kiss. Ya furta mata cikin kunnuwanta “An samu cikin su da k’iyayya an fara nak’udarsu da wata irin soyayya mai zafin gaske Allah ya maimaita mana daren jiya My Cute Angel.” Nasma dai da sauri ta fice don ta lura Jaheed baya ji baya gani. Sai da suka gama lalle yaransu tas sannan Jaheed ya fita ya kira nurses don a d’agata a gyarata tunda ba iya tashi zata yi da kanta ba.