← Book details Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 43

Sashe 22

Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da azahar kuwa suka shigo harabar gidan cikin rakiyar fadawan Sarkin Gabas da Tauraruwa da Murad. Nene kasa juriya ta yi ta ture alkunya gefe ta k’arasa harabar gidan a guje kamar ta kifa. Wani irin sauri ta yi ta fa’da jikin Inno da take tsaye tana kallonta alamun tsufa sun fara bayyana sosai a jikinta. Babi kallonta yake yana murmushi kafin ya mik’a hannu yace matso nan y’ar Akbarka Matso Hajiyata na sake ganin ki Allah Alhakamu ashe zan sake ganin ki a rayuwa?” Wani irin kuka ne ya kufcewa Nene ta fa’da gefen kafa’dar Babi tana sakin ajiyar zuciya da hawaye masu yawa a fuskarta. Babi ya rik’eta tsam ba wanda ba su bawa tausayi ba a wajen. Kowa sai da ya share hawaye. Jaheed ne ya bu’de musu b’angaren Bak’i na gidan ya ce su shiga kafin su huta tunda tafiya ce mik’akkiya suka yi. Nene hannun Inno ta ja tana bin k’annenta da duk suka zama
Magidanta da kallo “Mu je ciki Inno ta na cigaba da ganin ki har yanzu ban gaji da ganin ki ba.” Inno ta yi murmushi kunyar Fulani ta kamata sai ta dinga tuno Nenen a lokutan yarintarta yarda ta tashi da tsananin mak’o sai ga shi lokaci guda Allah ya raba su. Murad ma bin bayansu ya yi ba tare da sanin su ba. Suna shiga d’akin ita kuma Najee ta fito daga kitchen ba tare da sanin sun shigo ba kanta ko d’ankwali babu ta ware ido tana kallon Nene ba tare da sanin Murad na bayansu ba ta ce “Nene kin ga fa yarda kika shige jikinta kamar zaki sha Nono.” Karaf idanunta ya fa’da kan Murad!

JIKAR NASHE✍🏽🥳

08033748387.
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Ita d’in ma kallonsa take yi dariyar da take dannewa tana son kub’uce mata, ganin yarda ya yi da fuskarsa kamar yaga kashi ko wani mugun abu. “Me ya kawo ki nan witch?” Ya fa’da idanunsa a lumshe don baya son ya sake katari da mummunar fuskarta. “Cewa aka yi nazo naga angon da aka Zab’a min..” bai San sanda ya sake ware idanunsa ba ya bu’de su sosai a kanta ya ce “Kada kice min ke ce Najwa?” Ta d’aga kai tana sake wage manyan hak’oranta da suka turo gaba. “Ni ce mana, ka yi mamaki ne?” Bai furta komai ba illa mik’ewa da ya yi fuskarsa a ha’de ya fice daga sitroom d’in yana jin komai za’a yi ba zai auri yarinyar nan ba, cabd’i duk zuk’a zuk’an matan da suke duniya a rasa wacce za’a ba shi sai wannan abar mai kama da….. ya sake datse leb’ensa yana ha’diye sauran maganar a cikinsa zuciyarsa na sake wani irin k’una ya fita wajen gidan so yake ya samu nutsuwa kafin ya je wajen Tauraruwa ya tubure mata ya zama dole ta kunce wannan abin da ta k’ulla, banda Uban muni da ke tattare da ita ga rashin shekaru wato sun rasa wanda za su aurawa y’ar su shine ake nema a lika masa. Zama ya yi kan wata mota a harabar gidan ya saka hannayensa ya tallafe kansa yana kallon taurarin da suke sararin samaniya kai kace hankalinsa a wajen yake, sai dai tafasar da ke cin zuciyarsa yafi gaban ya tsyaa duban Taurari. Tana ganin ya fita ta yi dariya son ranta kafin ta mik’e ta bi ta baya ta koma d’akinta. Wanka ta yi ta wanke fuskarta sosai ya fito tana tsane gashinta da ta dank’ara masa gel duk don ya kwanta ta yi kamar mara gashi. Simple Riga da wando ta d’auka ta saka masu colour pink. Sai ta yi rolling pink gele ta fita parlourn har da y’ar wak’arta zuciyarta cike da nisha’di.

Suna zaune gaba d’aya ta shige kitchen don ta ha’do black tea d’in da ya zame mata dole ta sha duk dare, sai zabga k’amshin zuma da kaninfari da citta da cinnamon yake. D’ankwalinta kanta ya zame yalwataccen gashinta da ya zuba har baya ya kwanta a saman goshinta. Bata damu da rufe kan ba kasancewar duk mata ne a parlourn kuma ta kasa jumirin yin d’abi’ar kunyar da Umma ta umarceta da yi. Zamanta ke da wuya, sassanyar muryar Murad mai cike da Haiba ta doki kunnuwanta, bata damu da ta tashi ba don ta san ba zai tab’a ganeta ba. Yana saka kai cikin parlourn idanunsa suka fa’da kanta wani irin duka k’irjinsa ya yi yanayin da bai tab’a ji ba game da mace a karo na farko ya sameshi wata irin halitta mai kyau cute baby a binta kamar ita ta yi kanta. Ya kasa cire idanunsa a kanta itama ba ta fasa kallonsa ba da golden eyes d’in ta dara dara masu baiwar kyau da fusgar hankali. Da k’yar ya saita kansa sanda ta mik’e surar jikinta da k’ugunta yake a cike taf kamar ba yarinya ba ya bayyana mayafin da ya zame ne ya ba shi damar ganin tudun k’irjinta da sauri ta sunkuya don d’aukar mayafin inda idanunsa suka sake masa wani kyakykyawan gani gaba d’aya bata san saman k’irjinta ya fito ba. Da sauri ta gyara rigarta ganin kamar yana kallonta, ta turo d’an leb’enta gaba tana k’unk’uni kafin ta d’au shayinta ta harareshi ta gyara mayafin. Murmushin da bai shirya ba ya sakar mata ganin yarda tsiwar ta mata kyau shagwab’a da tsiwa suna daga cikin abinda yake so a tare da mace, Tabbas wannan ko wacece ta ha’da duk abinda yake so a tattare da mace, ashe y’an matan d’azu da ya gani bai ga komai ba sai yanzu amma da wannan zuk’ek’iyar aka rasa wacce za’a ha’da shi da ita sai waccan mummunar wallahi tabbas yanzu yaga mata kuma ko ruwa da iska ba mai hana shi mallakar yarinyar nan da ta tafi da dukkan tunaninsa at first sight. Duka wannan tunanin a cikin mintuna ba su fi uku ba komai ma ya faru kuma ba wanda bai ga abinda ya aikata ba a cikin parlourn suka kalli juna suna murmushi.

Cigaba ta yi da sipping shayinta a hankali a kuma yangance da matuk’ar jan aji kamar ba Najee ba. Murad ya kasa hak’uri ya dubi Tauraruwa ya ce “Ammeey I want to talk with you.” Ta kalleshi ta ce “Okay go ahead.” Ya girgiza kai still idanunsa na kan na Najwa da sam baya son ya d’auke idanunsa a kanta ya ce “I need privacy Mah.” Tauraruwa ta saki murmushi tana mik’ewa ta ce “Okay mu je can parloun.” Ya mik’e har yana yin tuntub’e garin kallon Najwa da ta bi ta ha’de ranta kamar bata tab’a dariya ba.

Suna shiga parlourn ya zube a gaban Tauraruwa ya ce “Haba Ammeey me yasa? Me yasa sai mummuna zaa bani bayan ga colour ta wallahi wannan yarinyar ta parlour ita nake so ita na zab’a yau yau na fara ganinta amma duka tunanina da hankalina ya tafi kanta, don Allah save your son life wallahi ba ta yarda za’a yi na iya hak’ura da ita.” Tauraruwa wani kallo ta masa shek’ek’e ta ce “Ka san me kake fa’da kuwa? Matan auren kake so? Wannan k’anwar Umma ce kuma da aurenta kada ka ganta yarinyar matar wani ce, don haka ka yi saurin istigafari….” Runtse idanunsa ya yi yana jin a duniya bai tab’a jin mummunan magana kamar wannan da Tauraruwa ta yi ba. Tana da aure? Ashe kuwa rabuwarsu da Mijinta ta zo don wallahi yarda nake jin zuciyata na nauyaya da sonta dole ne na mallaketa zan ba shi ko nawa ne don kawai ya bar min ita.” Tauraruwa ta tab’e baki ta ce “You are out of your mind, don haka ni ba zan ce maka komai ba, amma wallahi ka bi a hankali ita wacce muka zab’a maka menene Aibunta?” Ya ware idonsa da suke runtse murya a shak’e ya ce “Menene aibunta? Ko menene aibukanta? Ta yaya zaku ba ni wannan ku ce na aura fisabilillah?” “Jihadi zaka yi, ka tuna tana da tarbiyya da addini kuma ko bakomai ta ci albarkacin kula da k’aunar da ta nunawa mahaifiyarka ta so Nene ta bata dukkan kulawarta lokacin da take a matsayin mahaukaciya… sannan wannan da ka gani a parlourn bata da aure amma k’anwar Umma ce kuma da kunya kace baka son y’arta k’anwarta kake so…””Ni wallahi ba zan aureta ba ta fa’di ko nawa ne na biya ta amma ina kai haba!” Ya fa’da zuciyarsa a raunane yana jin kamar ya zunduma ihu bai ma gama jin sauran zantukan Tauraruwa ba ya fice daga parlourn ya sake zuba idanunsa akan Najee da tayi kamar bata gan shi ba kafin ya fice da sauri. Jaheed da shigowarsa kenan suka gabza karo ya yi saurin ja da baya yana kallonsa sai dai Murad ko ta kansa bai bi ba ya fice a zafafe. Jaheed murmushi kawai ya saki ya shiga cikin parlourn yana dubansu da Tauraruwa da take ta dariya bata gaya musu abinda ya faru ba. Ya ce “Wai lafiya kuwa naga Murad ya fita a zafafe?” Tauraruwa ta shiga basu labarin abinda ya faru Najee ma ta d’ora da nata Ai kuwa aka dinga dariya a parlourn Jaheed ya ce “Don Allah mu bi da shi a haka har zuwa sanda zata tare a gidansa muga yaya zai yi?” Umma ta girgiza kai “Ba kyau gaskiya hakan, ku fa’da masa gaskiya mana.” Rok’on ta Jaheed ya dinga yi akan ta taimaka ta musu hakan da k’yar zuciyarta ta yarda a hakan, aka kuma ce Najee kada ta sake koda wasa ta nuna masa ba haka kamanninta suke ba, ta d’aga kai tana jin da’din had’in kan da suka bata.

A bedroom rasa nutsuwa ya yi ya kai gwauro ya kai mari surar Najee tana masa gizo a zuciya ya lumshe idanunsa yana jin wata irin zafaffiyar k’aunarta na huda zuciya da ruhinsa har hango kansu yake kwance a matsayin maaurata yana wasa da kayan fulaninta. Ya lumshe idanunsa yana sakin hucin numfashi a hankali wani din shauk’i yana fisgarsa yana ji a duniya zai iya rabuwa da duk abinda ya mallaka in dai zai samu yarinyar a matsayin mata.
Chapter 22 · 0% Book details