Sashe 24
Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A kitchen Umma ta samu Najee ta rutsata tana zabga mata harara “Marar kunyar banza don shashashanci wannan maganar da kika musu ke a tunaninki ta dace, Wai Najwa yaushe zaki zama mai hankali ne? Ki yi ta abu kamar goyon kaka ko don kin tashi cikin maza shikkenan sai ki zama mashiririciya har abada kin kasa nutsuwa balle ki fara gwalli da fyalli irin na y’an mata, koda yaushe ba nutsuwa a tare da ke, to ki bu’de kunnenki da kyau na gaya miki Murad shine mijin da zaki aura ya zama dole kuma ki jajirce wajen kula da kan ki, kwalliya tsafta iya magana idan ba haka ba kina ji kina gani ya miki nisa shashasha kawai. Kuma ki wuce ki je ki durk’usa har k’asa ki gaishesu, kina da kwanyar manya amma shiririta ta miki yawa. Ana sallahr magriba kuma ki yi wanka ki shirya tsaf ki je sitroom kina da bak’o.” K’asa ta yi da kanta tana fa’din “To Umma, don Allah ki yi hak’uri.” “Ni baki min komai ba halayenki nake son ki canja gwara ki san kin girma yanzu Allah ya miki albarka kin ji?” Ta d’aga kai tana gyara mayafinta ta fita parlourn a zuciyarta tana fatan Allah yasa Murad baya nan don bata shirya bayyana masa kanta yanzu ba.
Ajiyar zuciya ta saki ganin baya nan sai ta hau jan mayafi tana rufe fuskarta wai ita aladole sai ta aro wannan halin da Umma take so, ta san dai haka ake wa surikai don tana gani a film. Tauraruwa murmushi ta saki tana furta “Yau kuma Najwa mu kike jin kunya ko Inno?” Bata yi magana ba sai dai ta cikin mayafin take kallonsu tana ganin yarda Inno take ta hangen son ganin fuskarta. “Ina wuni? Kun zo lafiya ko?” Nene dariya ta yi tana mamakin Najwa wanda daga ganin acting d’in da take ta san tursasata aka yi. Suna amsawa ta mik’e da sauri ta hanyar d’aki don har ga Allah gumin da take na yafen mayafin da ta yi ya isheta. Tauraruwa ta bita da kallo tana dariya k’aunar yarinyar na sake shiga ranta, komanta mai kyau ne da tsari tun a yanzu ma ina ga nan gaba idan mak’erin y’an mata ya sake k’erata.
Tana shiga d’akinta ta yi wurgi da mayafin har da d’an kwalin ta ce “Wannan masifa har ina? Wallahi Umma ba zan iya ba in yi ta wani k’unshe kai na kamar wata munafuka, shi kuwa anjima zai ga kyakkyawa Ai ina jin duk abinda yake fa’da d’azu…. Ta tuntsire da dariya tuna abinda ta shirya masa.
Ana sallahr Magriba cikin zakwad’i Murad ya koma sashen da nan ne D’akin Jaheed da Faruk na asali yake. Wajene mai kyau da ya sha kayan alatu na more rayuwa. Wanka ya yi sosai gaba d’aya a k’afauce Yake ya damu k’warai ya je Yaga matar da aka zab’a masa, duk yarda yake k’issima kyanta sai yaga kamar ya rage mata kyau shi gani yake ma a duniya ba mai kyanta don ya san kowa ya san tsarinsa na son auren mace kyakykyawa mai kuma ajin gaske. Taje kansa ya yi sosai ya baza turare tsananin kyan da ya yi zata zaka yi a ranar zai angwance a d’akin amaryarsa. Tunda ya fito Jaheed yake kallonsa cikin mamaki ya ce “Irin wannan ado haka sai kace za’a kai ka d’aki?” Murmushi ya saki yana furta “Kusan haka tunda yau zan ga Matar da aka zab’a min, na san dai hundred percent ta cika mace tunda Ammeey da kanta ta min zab’in ka san bata zab’en abu marar kyau, don haka dole nima na matso kyau na da yarinta ta ba don komai ba sai don na sace zuciyarta at first Sight.” Jaheed murmushi ya saki a ransa yana jin Murad bai san y’ar ficikar da aka zab’a masa ba. Dariya yake son yi sai don ya matse ya ajiye dariyar zuwa anjima ka’dan. Murad ya fice har da y’ar wak’arsa yana rausayawa a hankali cikin tsananin shauk’i da farin ciki da ya bayyana muraran akan fuskarsa.
Zama ya yi a sitroom d’in yana karewa sitroom d’in kallo duk da hankalinsa ba anan yake ba yana kan ta inda Najwa zata b’ullo.
Bata bari kowa ya ganta ba ta fice da sauri ta k’ofar baya tana sakin ajiyar zuciya kafin ta isa sitroom d’in ta lullub’e fuskarta da mayafi Ta yi sallama cikin kasalalliyar muryar da Yasa Murad saurin d’agowa yana sakin ajiyar zuciya wani farin ciki na ratsashi ya amsa sallamar. Yana kallo ta isa kujerar da ke gefensa ta zauna tana furta “Ina yini?” Waro ido ya yi yana furta “Wait tsaya don’t tell me da wannan hiding face d’in zamu gaisa, please remove it I want to see your beautiful face Baby….” Ya saka hannu yana yaye veil d’in fuskarta wani irin razana ya yi ya ja da baya da k’arfi a tsawace kuma ya furta “What?”
JIKAR NASHE✍🏽🥳
08033748387.
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Har tsakiyar dare Murad ya kasa runtsawa shi dai kam da kansa zai iya cewa bai ga wani abu da ya tab’a hana shi barcin dare ba kamar yau da soyayyar Najwa ta hana shi sak’at. Da zarar ya rufe ido cute lips d’inta yake gani sanda ta turo shi gaba da niyyar yi masa tsiwa. Ya dinga juyi shi ka’dai akan gado ya rasa me ke masa da’di. Bai k’i ba ace ya sake ganinta kusa da shi tana sakar masa harara da daradaran idonta. Ashe haka soyayya take? Da yakewa maza masu soyayya kallon wa’danda ba su san ciwon kan su ba. Hotonta ya zauna daram a zuciyarsa da idaniyarsa ba abinda yake gani sai kamanninta da gaske yana jin ko cewa aka yi ya zanata tsaf zai zanata sabida yarda kamanninta suka zauna ra’dam a ruhinsa. Har Asuba ya kasa runtsawa Allah kawai yake rok’o ya mallaka masa Najwa a matsayin matarsa ta aure matarsa ta dindin. Ya daure ya yi Sallah kafin ya watsa ruwa ya zura wasu sassauk’an kayansa na shan iska sabida yarda ake zafi a gari. Wasu irin kalolin turare ya fesa a jikinsa duk da nauyin da idanunsa ya yi masa bai saka shi fasa fita harabar gidan ba ko Allah zai saka ya ganta kafin gari ya waye sosai ya shiga cikin sashen Umman. Wannan karan da kansa zai rok’i Umma ba zai ji kunyar gaya mata y’arta bata masa ba k’anwarta ce ta masa. Tattausan silifas bak’i wuluk da ya dace da tattasar k’afarsa da alamun hutu suka gama ratsa tafin k’afar kamar ta jarirai shi ya zura ya fita k’ofar gidan. Idanunsa sun d’an tasa ka’dan saboda rashin barci.
Yana fita suka yi arba da Baffa da shigowarsa kenan daga masallachi. Da sauri ya rusuna ya gaisheshi. Baffa cikin jin da’di ya amsa a ransa yana godewa Allah da ya saka Murad ya zama surikinsa tarbiyyar yaron da nutsuwarsa ta masa sosai ji dai yarda ya zube yana gaisheshi kamar ba Dan sarki ba. “An tashi lafiya Murad? Ya bak’unta da zafin garin mu?” Murad ya d’an sosai kai yana furta “Alhamdulillah.” “Ma sha Allah, Ai sai mu shiga ciki mu karya ko?” Murad ba musu ya bi shi don burinsa sake arba da yarinyar da ta tafi da dukkan tunaninsa, so Yake ya yiwa Baffa maganar sai dai ya kasa kallon k’wayar idonsa ya gaya masa sirrin zuciyarsa abin kamar da nauyi. “Mu fara shiga mu gaisa da matan gidan, haka ake so ga duk magidanci bayan sallahr asuba ya zaga ya tabbatar da iyalinsa sun kwana lafiya koyi ne k’warai da sunnar manzo s.a.w babu Alfanu kace kana jiran matarka tazo ta gaisheka ba mu ji haka a Hadisi ba ba Kim’s ruwayar da ta rawaito shi duk da idan hakan ta faru ba laifi ba ne, amma dai a bi koyarwar annabin shine mafi a’ala.” Murad ya saki murmushi kawai, halayen Baffan da nagartar d’abioinsa suna sake masa naso a zuciya yana jin Baffan yana sake burgeshi abu guda da yayi ya ba shi haushi rasa yarinyar da zai ba shi a cikin y’ay’ansa sai waccan mummunar da ko tunata baya son yi.
Sashen Mahmeey suka fara shiga. Shiru sashen da alama sun koma Barci. Baffa ya d’an bi parlourn da kallo kafin ya ce “Sarkin barci har ta koma zauna ina zuwa Murad.” Ya fa’da yana shiga corridor da zai kai shi inda bedrooms d’in d’akin suke.