Sashe 30
Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Suna isa Jaheed ya fito cikin girmamawa da ganin girma da dattijantakar Baffannasu mutum ne da ya amsa duk wani suna da nagartaccen mutum da duniya ta yarda da nagartarsa yake amsawa. Baffa ya amsa gaisuwar da Jaheed yake masa cikin fara’a ya kama Jaheed d’in suka mik’e tsaye “Ba irin wannan gaisuwar a musulunci Mujaheedu, musabaha shi manzon Allah ya umarcemu da yi da yiwa juna sallama duk da al’adance bahaushe yana ganin wannan itace gaisuwa mafi dacewa sai dai ba hakan take a musulunci ba duk wata gaisuwa ta bi bayan Assalamu Alaikum da kuma kama hannun juna. Don haka ka kiyaye ka ji ko?” Jaheed ya d’aga kai yana kallon Najma k’asa k’asa da yake zabga wani irin k’amshin turare mai masifar fusgar hankali. “Mu je ciki ka ha’da min kan matan naka akwai nasihar da zan musu wanda in dai sun bi to sun rabauta daga afka wa turbar shai’dan idan kuwa ba su bi za su yi kaico da nadama tun a duniya.” Jaheed ya shige gaba suka isa Babban parlourn inda Khaireey take tana zaune tana cika tana batsewa gaba d’aya ranta a dagule yake da dawowar Najma cikin gidan.. da k’yar ta amsa sallamar su Baffan ta kuma gaisheshi da k’yar bayan ganin tabbas ya cancanta ta yi gaisuwar banda haka jan bakinta zata yi ta tsuke. Baffa yana kallo Jaheed ya wurga mata harara murmushi kawai ya saki a ransa ya fara tunanin lallai akwai aiki a gaban Jaheed matuk’ar yace wannan abinda Khaireey ta yi har zai zama abin damuwa. “UMMUL KHAIREEY!” Baffa ya kira sunanta cikin kambama murya. Ta d’ago a hankali tana kallonsa ha’de da amsawa da na’am can k’asan mak’oshinta. “Na zo nan ne a matsayin Uba a waje dukkan ku ki k’addara naki mahaifin ne a zaune kin tabbatar dai mahaifi ba zai cutar da y’arsa ta cikinsa ba ko?” Khaireey ta d’aga kai. “To ki bani wannan position d’in nasa, Ita kishiya ba komai ba ce idan mutum ya mayar da ita bakomai d’in ba ya sanyata a mahallin da ya dace. Idan kuwa ka saka ta a matsayin komai d’in sai ta zame maka komai d’in har ta zame maka wata masifa a rayuwa. A duk yarda kika d’au kishiya a haka Allah yake baki iko da nasara a kanta ko ita ya bata nasara a kan ki. Bance babu asiri ba amma nan yarda yana yin tasirin da k’addarar Ubangiji take yi ba. Duk abinda ya samu bawa daga Allah yake matuk’ar mutum ya yi imani da haka to imaninsa ya cika hundred percent. A duk sanda kuwa mutum ya raunata haka a ransa to tabbas imaninsa ya ragu. Ki d’auki kishiya matsayin y’ar uwa wacce zata tayaki da buk’atun mijinki idan ta kama har da ta y’ay’anki sai ki ga ta zamar miki a matsayin y’ar uwa matuk’ar baki k’ullaceta da sharri ba ba ta yarda za’a yi cutar da zata miki ta yi tasiri a kan ki idan ba a yi hankali ba ma sai cutar ta ta ta dawo kan ta ke Allah ya kareki ba don komai ba sai don taki zuciyar mai kyau ce ba kya nufarta da sharri. Ga duk macen da ta saka wannan a ranta zata samu sauk’in kishi, ki rik’e cewa Allah ne ya halatta masa ya auri mace sama da d’aya ba son ransa ba, idan kika hana kin haramta abinda Allah ya halatta kenan menene makomarki? Ku rik’a tunanin yawan matan da suke zaune a duniya waye zai aure su? Shin zaki so k’anwarki ta rasa Mijin aure ko y’ar ki? Idan kuma aka tashi bikin k’anwar ki zata auri mai mata sai kuma ki zamo sahun gaba wajen ingiza mai kantu ruwa, abinda ka sowa kanka ka sowa d’an uwanka shine cikar imanin mutum! Don Allah ku zamo masu kwantarwa da mijinku hankali ba masu tayar masa ba dukkanku y’ay’ana ne kuma idan kika bijirewa umarni na sai na saka d’ana ya sake ku, Allah ya baku zaman lafiya ya kawar da dukkan fitina da munafukai a tsakaninku.” Suka amsa gaba d’aya. Khaireey ta saki ajiyar zuciya sai ta ji zuciyar ta wasai duk wani abu da ya dunk’ule mata a k’irji yana narkewa a hankali ta shaida da nagartar Baffa a yau ta sake tabbatarwa da Baffa da Umma dattijan ne na gaske. “Allah ya muku albarka!” Baffa ya fa’da yana mik’ewa suka amsa cikin fara’a da jin da’din addu’ar sannan suma suka mik’e suka raka shi har mota. Najma na share k’walla sai ta ji kamar yau ne aka kaita gidan Miji take turjiya bata so sai ga shi a yanzu ba abinda take muradi sama da gidan Mijinta ba kuma wanda take so sama da Jaheed data tsana a baya. K’ok’arin shiga sashenta take kawai ta ji hannun Jaheed a cikin tafin hannunta ya janyota da sauri ta baya. Har suna ha’da jiki tana juyowa cikin wata irin murya da bata tabbatar tasa ba ce ya ce “Mu je can parlourn tukun.” Ya fa’da yana kokawa da numfashin da yake k’ok’arin sar’ke masa sabida tasirin turarenta da da’din da ya masa a rai. Lumshe idonta ta yi ka’dan tana ha’diye yawun da ya taru a harshenta ta yi k’ok’arin zame hannunta sai dai bai bata damar hakan ba ya kuma d’auke kai kamar ba shi ya rik’e hannun ba, cikin murya mara amo sosai ya ce “Don’t try it again….” Shiru ta yi ta bar masa hannun suka nufi sashensa. Don bai bata damar komawa nata sashen ba ji yake kamar wani magana’disu na jansa zuwa jikinta. Khaireey kuwa tuni ta koma nata sashen tana k’ok’arin yak’i da kishin da yake son turnik’e zuciyatta ta hanyar tasbihi a zuciyarta da jan Hasbunallah lahaula wala k’uwwata.
Suna shiga sashen nasa ya kai mata wata kyakykyawar runguma ta baya, Allah ne ka’dai ya san yarda ya iya daure zuciyarsa zuwa wannan lokacin bai fasa sirrin da yake ransa na tsananin son matar sa da tausayinta ba. Bai bata sukuni ko dama ba ko ka’dan balle ya marabceta da abubuwan mak’ulashen da ya siyo mata ba, burinsa ya isa can birnin da yake mafarki. Bata hana shi ba, don itama ta yi kewarsa matuk’a da gaske don haka komai ma da ya faru ya faru ne cikin shauk’i da son juna da kuma tsananin buk’atuwa da zumu’di ga juna. Jaheed kam ya nuna mata wata irin soyayya mai tsayawa a rai da ya kasa barinta har sai da ya furta a saman lab’b’ansa “I love you with all my heart Baby kada ki sake nisa da ni pls!” Murmushi ta saki tana furta In sha Allah! Ta fa’da tana cije bakinta saboda wani irin murd’a wa da mararrta ta yi tun tana daurewa har sai da Jaheed ya gane ya d’ago ta da sauri yana kallon k’wayar idonta ya ce “Gaya min menene?” Cikin wata irin murya da ta nuna galabaita ta ce “Ciwo My J… mutuwa zan yi na sani ba zan yi doguwar rayuwa da kai ba duk da tsananin son da nake maka……! Sak Jaheed ya yi wata tarin k’walla na shirin zuba daga k’wayar idonsa cikin muryar tsorata ya ce “Ya Allah kada ka nuna min wannan ranar!” K’arar da ta yi ya ankarar da shi ya kamata ya kaita asibiti sai dai ko kafin ya yi wani yunk’uri sai gani ya yi ta cije bakinta ta furta “Jaheed da gaske mutuwa zan yi, pls ka kira min Baffa Umma da Mahmeey!