← Book details Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 43

Sashe 43

Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Ranar da suka isa Nigeria kai tsaye masarautar Gabas suka wuce inda dandazon mutane suka cika don taransu. Baffa ma ya je Jaheed da matansa da yaransa su Umma da Mahmeey duk sun halarta don a ranar za’a yi sunan su. Najee suna shiga masarautar ta dinga mamakin yarda aka cika kamar me? Murad kuwa fuskarsa ta koma irin fuskar da ta sani a wancan lokacin ya kuma rik’e hannunta gam bayan ya dank’awa Tauraruwa yaran yana sakin murmushi. Nene kuwa duk kunya ta bi ta isheta ganin yarda Najwa take kallon cikinta da ya fito sosai haihuwa ko yanzu ko anjima. Niyyar ta ta rungume Nenen sai dai yanayin yarda taga Nenen yasa ta ja baya a kunyace.

An ci an sha an kuma yi hidima sosai dafatan Allah ya yiwa yara albarka. Abin al’ajabi a cikin daren dai Nene ta fara nak’uda. Ranar girkinta ne a gigice mai martaba ya kira Tauraruwa da Jakadiya aka kira likitar masarautar su suka karb’i haihuwar Nenen inda ta haifo sankaceciyar yarinyarta mai kama da Tauraruwa. Sarki bayan an kai masa ita yana d’aga ta ya saki murmushi ya furta “Tauraruwa y’ar Tauraruwa Ma sha Allah Allah yasa ki gaji mai sunanki wajen son zumunci da sadaukar da farin cikin ki ga y’an uwanki Allah ya miki albarka…” Duk wanda yake parlourn sai da ya amsa y’ay’a da surikan Sarkin da y’ay’an Tauraruwa su Baffa da su Umma. Tauraruwa ta rungume y’ar a k’irjin ta tana furta “Wannan tawa ce Nene ki gama shayar da ita na karb’i abata kuma Tauraruwa nake son a dinga kiranta….” Murad ya yi murmushi ya ce “Allah yasa kada ta gado fa’danki…

Aka saki dariya gaba d’aya.

Ma sha Allah Alhamdulillah nagode da jumurin karatu dafatan kuma zaku yafe min idan da wanda na b’atawa a cikin ku. JIKAR NASHE TA KU CE!

Don samun litattafaina kai tsaye ku nemeni a wannan numberr

08033748387…

https://chat.whatsapp.com/CSyG2rUpE7d9mgJLU8VCzJ

In sha Allah littafin KHUL'I zai fara zuwa muku 8/5/2024.
Ban sani ba ko zai ƙayatar da ku amma ina ji a raina za ku so shi fiye ma da NAGARTA. Zai ilimantar ya kuma faɗakar kai har ma ya nishaɗantar In sha Allah.
Nabeehar Amaan ta na miƙo gaisuwa tare da fatan za ku yi jumurin bibiyar labarinta.
Update ba kullum ba ne daga Monday ne zuwa Thursday. Madallah da nagartattun mutane.

So domin Allah💞

UMMU AMMARAH✍️
Chapter 43 · 0% Book details