← Book details Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 43

Sashe 41

Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babban hotel d’in Hilton suka sauka. Tun daga yanayin yarda aka zubawa gadon d’akin wasu irin flowers gaban Najwa yake fa’duwa ta zauna ta rab’e a lungun gadon. Tana kallon yarda Murad yake cikin Nisha’di sai wak’ar India yake rerawa kamar Baindiyen. Ganin zai cire kaya ya sakata runtse dariya kawai ya yi yana furta “Mhmn…” Ya shige toilet. Najwa ta shiga duban d’akin tana tunanin yarda zata kwana ita ka’dai daga ita sai Murad a wannan d’an k’aramin gadon don ko ka’dan bai da girma. Ya dai sha ado na alfarma kamar me? Sai kuma zabga wani ni’imtaccen k’amshi yake. Daga shi sai Bathrub ya fito da hand towel a hannunsa yana goge sumar kansa ya tsaya a kanta yana furta “Oya taso a yi wanka…” Najwa ta yi saurin zaro ido… “Ki taso kafin na d’aga ki cak!” Kafin ta ce me kuwa ya sureta tana ihu amma bai k’yaleta ba sai da suka shiga toilet Najwa ta dinga rok’onsa ya ajiyeta. Ya ajiyeta a cikin bathtub yana dariya ya furta “Me Zan gani k’waila kuwa… Ki tsaya na cu’daki da kyau don na san da k’yar hannunki zai kai baya…” “Yaya Murad…” Yes Naj” ya furta yana kai hannunsa kan zip d’in Rigarta da niyyar zuge wa ta yi saurin rik’e hannun tana furta “Please ka bari ba kyau, y’an iska ne suke haka..” Ya lumshe idonsa a hankali yana furta “Nima shine… Naj called me Dan iska as from today…” Daga nan fa duk wani labari ya fara canjawa idonsa ya rufe baya ji ba ya gani dole na juya da sauri don wannan rahoton yafi k’arfina abu guda da na sani a ranar Murad ya sha Allah ya isa…

—————-

Shiru sashen Nenen Jakadiya ta yi sallama ta shiga. Nene da take zaune zugum abin duniya ya isheta kusan zata iya cewa jinta take kamar wata amarya ko da yake amaryarce bata tab’a aure ba a rayuwarta a zahirance kuma bata tab’a soyayya da wani namiji ba balle har ta kai ga ta fara hasashen aure a rayuwarta. Duka rayuwarta ta sadaukar ne wajen son ganin rayuwar d’anta Jaheed ta inganta. Ta lumshe idonta tana sake shak’ar k’amshin humrar da Umma ta bulbula mata. Wani irin k’amshi ne mai fisgar hankali. Sallamar Jakadiyar ta amsa tana sake sunkuyar da kanta yanayinta ne na kunya ne sosai jinin Fulani ke aiki a jikinta. “Ma sha Allah, Allah ya yiwa aurenku albarka.” Jakadiya ta furta a hankali kafin ta bu’de wani akwati da tazo da shi.
Wata irin alkyabba ce a cikinsa mai masifar kyau ta cireta tana zabga k’amshin turare ta mik’awa Nene. “Ranki ya da’de sarki mai dafan iko yana jiranki a wannan dare mai albarka cikin turakarsa!” K’irjin Nene ya yi wata irin tsawa, tsawar da ta ji ta masa a dukka sassan jikinta. “A fito lafiya ina parlour ina jiranki ya da’de…” Daga haka ta fita Ta bar Nene da wata irin rawar hannu da kakkarwar jiki. Ta mik’e cikin sanyin jiki ta sake d’aukar zumar Kayan matan zuru ta sha sannan ta shiga toilet ta wanke bakinta ta fito ta zura Alkyabbar ita kanta ta yaba sa kyan da alkyabbar ta mata a jikinta, sam idan ka ganta ba zaka ce ita ta haifi Jaheed da Murad ba. K’wank’wasa k’ofar da aka yi ne ya sake hargitsa y’ay’an cikinta ta amsa cikin k’asan mak’oshi. Jakadiya ta sake shiga tana furta “Idan Gimbiyar Gabas ta shirya ta fito…” Tattausan silifas black da ya dace da y’ar duma
Dumar k’afarta fara tas ta saka a k’afar suka nufi b’angaren Mai martaba da yake ta wata sirrintacciyar hanya a d’akinta.

Ba kowa a hanyar sai Fadawa masu tsaron fadar da daddare. Suka nufi k’ofar mai Martaban. Yana zaune a saman kujerarsa mai masifar kyau ta cikin falonsa na sirri wanda ba mai shiga daga matansa sai y’ay’ansa sai kuma Jakadiya. Ya d’ago yana amsa sallamar yana shak’ar k’amshin turaren da ya kusa saukar da shi a saiti. Murmushi ne sosai ya sub’uce masa irin murmushin da Jakadiya zata ce ta da’de bata ga ya yi shi ba. “Kin gama aikin ki” ya furta a hankali yana kallon Jakadiyar. Gaisuwa ta kai masa kafin ta mik’e ta fita. Shiru parlour ya d’auka idanun Maimartaba akan Nene ya saki ajiyar zuciya a hankali ya furta “Fulani!” Sunan ta ji ya mata girma sai dai sanin cewa daga ita sai shi ya sata ta d’ago dara daran idonta ta zuba masa. “Taso ki dawo nan kusa da ni…” Zuciyarta ta buga a hankali. “Taso Fulani taso na ji jikin da na da’de ina mafarki kusa da ni…” Ta mik’e a hankali don isa wajensa, tana shirin zubewa a k’asa ta ji ya ja hannunta ta zauna kusa da shi sosai a hankali ya fara magana. “Dukkan burina ya cika yau ga ni ga Uwar mafi soyuwa a cikin yara na. Ban san me Zan ce miki ba, kalmar Ina son ki ta yi ka’dan sai dai na ce ina miki wani gigitaccen so dafatan a wannan daren zaki samar min cikin k’annen su Murad wannan karan mata zalla nake so…” Hasbunallah shi kawai Nene ta iya furta saboda yarda tasirin kalamansa suka gigita zuciyarta a ranta ta furta “Ashe haka soyayyar take?” To Fulani Nene asuba ta gari.. Allah ya amsa bakin sarki a samo k’annen Murad…

________

Umma na shiga gidan ta ji shiru da sauri ta fito tana kallon mai aikinta “Ni Ina Najwa ta shiga ne? Tun d’azu nake bulayin nemanta a gidan nan ban ganta ba?” Mai aikin ta ce “To Ai ni Umma na zata tare kuka tafi don ko yau da nazo ban ga Najee a gidan nan ba….” A tsorace Umma take kallonta cikin fa’duwar gaba ta ce “Ban gane baki gan ta ba ina Najwan zata tafi je ki ki tambayo Mahmeey ko tana wajen Najma…”

JIKAR NASHE…

08033748387.
[5/12, 8:57 PM] Bahaushiya👍: Komai ya yi farko zai yi k’arshe banda ikon Allah……..

*********Murfi********🤗🤗🤗

Jinjina ga yabo ga y’an group d’in K’udirar Allah special group da normal group bani da bakin da zan gode muku. Tukuicin Aljannah garesu ya Allah.

Ina mik’a sak’on godiya ta Ga Bright Pens y’an uwana a fannin rubutu:

Naima sulaiman Sarauta

Ayshercool

Zee kumurya.

Godiya ga Mikiya Writers Association Nagode da karamci da jumirin sharing Rabbi ya sake ha’da kan mu……

*******Kun shirya karanta littafi mai da’di? To kada ki sake a yi tafiyar KHUL’I babu ke don zaki zo kina cizon yatsa maza garzaya group d’in Maktabu UMMU AMMARA don karanta littafin Khul’i daga jin sunansa kun san ba littafin Banza bane..

KUDIRAR ALLAH KARSHEN SHAFI…..

Mai aikin bata yi musu ba ta bi umarninta na zuwa b’angaren Mahmeeyn abinda ta gaya mata ya ‘dan tayar da hankalinta. “Rabo na da Najwa tun da asuba da ta tafi b’angarensu lafiya dai ko?” Cikin tsoro mai aikin ta furta “Ba a ganta bane…” Mahmeey da sauri ta mik’e ita da Nasma suna zare ido ta furta “Baa ganta ba kamar ya ya?” Ta fito ta bi bayan mai aikin d’an kwalinta a hannu.. Nan ta sake tabbatar da rashin Najwan. Nasma ce cikin murmushi ta ce “Anya basa tare da Murad, don jiya ma ya je asibiti ya d’auketa.” Umma ta waro ido tana furta “Da kuwa na ci Ubanta, ba igiyar aurensa a kanta yake bin sa….” “Ke kika hana igiyar auren nasa a kanta?” Suka tsinci Muryar Baffa cikin tsananin fushi da fusata. Da sauri Umma ta ‘dago tana kallonsa. “Ni na bata umarni ta bi mijinta bayan na mayar da auren da kuka zamo sanadin mutuwarsa saboda shashanci da k’wak’walwar yara… “ Shiru Umma ta yi don a idanun Baffa ta hango ya samu dukkan labarin abinda suka b’oye masa, don haka ta yi saurin saukar da idanunta a k’asa tana furta “Ka yi hak’uri sai da na hana Tauraruwa ce ta ce ta aikata hakan..•” “Da kuwa kun cucesu yau da ace saki Uku ya mata ya zaku yi da su? Ya zaku yi da Son da suke wa Juna da ya kasa b’uya har a cikin k’wayar idanunsu kun san abinda kuka aikata? Wannan shi ake kira da Ganganci don haka na mayar da aurensu kuma na umarceshi ya tafi da matarsa duk inda yake so.. Itama Nenen ki gaya mata ni na bashi umarni idan yaso sai ta shirya yin azimin kaffara guda Uku currrr!” Daga haka ya juya ya bar wajen ya bar Umma da sakin ajiyar zuciya ita kam don ta ita lamarin ya mata da’di hakan dama take so sam bata son ace Najwa ta na zawarci da k’ananun shekarunta… Mahmeey da bata san kan zancen ba ta tambayi Umma yarda aka yi Umman ta gaya mata Mahmeey ta ware ido tace “Gaskiyar Baffa ne kun aikata aikin yarinta wallahi, Allah ma ya kiyaye.” Umma dariya ta yi ta ce “Ai shikkenan Allah ya shige gaba ya ba su zaman lafiya…” suka amsa da ameen suna watse wa da barin wajen.

_______

Da wata irin kunya Nene ta farka daga barcin da ya sureta a gadon Mai martaba. Yanayin ya mata wani iri abinda Hausawa suke cewa banbarakwai. Ta kai dubanta gefen Mai martaba don ganin ko yana nan sai ta ga gadon wayam, ta duba agogon da yake kusa da ita kan bed side ta waro ido ganin yarda lokaci ya ja sosai sha d’ayan safe. Shi yasa tunda suka yi sallahr asuba ta so guduwa amma mai martaba ya hanata ya sake janta suka koma barci. Ta saki ajiyar zuciya tana lumshe ido ashe haka lamarin Aure yake tabbas da ta san haka matan aure suke cikin ni’imar Ubangiji da ba abinda zai kaita dakon wannan shekarun ba tare da aure ba.
Chapter 41 · 0% Book details