← Book details Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 43

Sashe 2

Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fulani Saddik’a kuwa jikinta a salub’e yake sosai, duk wani karsashinta ya gudu sai tsoro da jin kamar shikkanan za’a rabata da Murad da take jin sa kamar gudan jininta. Ta shiga sashenta hannunta cikin na Murad da sam ya kasa sukuni da walwala shima zuciyarsa a cikin ru’danin take, neman wanda zai sanar da shi wacece waccan matar yake? Yana jin nauyi da kunyar tambayar Mamma duk da itace Tambayar da son amsarta ya fi kowace tambaya a wajensa. Maganar matar da take ikirarin aura masa ba matsalar sa ba ce muddin matar bata masa ba sakin ta zai yi, ba ruwansa da wai itace mahaifiyarsa me yasa tana son sa ta wullar da shi kuma wanene Jaheed da har take kiransa d’an uwansa?

Fulani Saddik’a cikin d’akinta ta shigar da shi. Kafin ta koma kitchen ta ha’da masa tea mai lipton zalla don dai ta san cikinsa yau kam bai ga abinci ba, kamar yarda nata itama bai gani ba. Kanta a d’aure yake da tarin tambayoyi sai dai bata bari hakan ya bayyana akan fuskarta ba. Ta d’ebo tea d’in bayan ta soya masa scramble egg ta fito da su zuwa d’akin nata. A zube yake a k’asan carpet ya yi pillowa da hannayensa yana kallon ceiling. Ta saki ajiyar zuciya tana furta “Murad me ye haka? Sarki guda mai jiran gado a zube a k’asa, tashi maza ka sha tea idan ba so kake ka sake d’aga min hankali ba.” Ya mik’e kamar yarda take so ya kuma karb’i cup d’in a hannunta bai yi la’akari da zafin sa ba ya kafa
A bakinsa. Da sauri ta kalleshi sai dai kafin ta yi magana ya zuk’eshi tas yana mayar da numfashi. A tsorace ta kalleshi “Me ye haka Murad?
Kana cikin hankalinka kuwa?” Da k’arfin gaske ya runtse idonsa ya furta “Bana ciki Mamma, ina son sanin wacece waccan matar?” Da sauri Fulani Saddik’a ta kafa masa ido, tana son karantar yanayin da yake ciki. Tsoro ne ya kamata ganin kamar Murad cikin zakwa’din son sanin mahaifiyarsa yake, idan kuwa hakane ya zama na ita zata tashi a tutar babu. Da sauri ta dakatar da zuciyar ta ta kuma ha’de rai tana kallonsa ta ce “Me kake son sani game da ita? Kana son ka san ko itace mahaifiyarka a zahiri? Me hakan yake nufi akwai inda na tauyeka ne?” Ta fa’da cikin yanayi mai nuna zallar b’acin ranta. Wannan karan abin da ta yi bai da Murad ya ji zuciyarsa ta canja daga zakwa’din son sanin ainahin mahaifiyarsa ba da ma d’an uwansa guda da zai kira tilo, sai dai gudun b’acin ranta sai ya danne damuwarsa ya koma ya kwanta kamar yarda yake a da, sai dai yanzu ya lumshe ido ne yana cigaba da saurarar sak’a da warwara da zuciyarsa take masa. Fulani Saddik’a ta saki ajiyar zuciya tana mik’ewa ganin kamar barci ya d’aukeshi ta fice daga d’akin da sauri don isa wajen su Nene da take tunanin acan duk amsoshin tambayoyinta su ke.

Yanayin da ta bu’de k’ofar zai tabbatar maka da ta na cikin rashin nutsuwa. Nene da suma suke cikin rashin nutsuwar suka d’ago da sauri suna kallonta. Fuska ba walwala ta isa wajen su, ba tare da ta rufe k’ofar ba. Ta zauna idanunta cikin na Nene ta ce “Ki sanar da ni wacece ke? Sannan kuma ina son sanin shin abinda kika fa’da min da gaske ne ke kika haifi Murad ko kuwa?” Nene ta saukar da idanunta k’asa kafin ta jijjiga kai ta ce “K’warai har a yanzu bana manta rad’ad’i da zafin naku’dar haihuwar Murad da na yi nice mahaifiyarsa abinda yake bani tsoro waccen matar da ta bayyana kanta a matsayin mahaifiyarsu tabbas shine irin turaren da nake ji a jikin matar da ta taimakeni a wancan lokacin….” Da sauri Fulani Saddik’a ta bu’de manyan idanunta ta ce “Da gaske?” Nene ta ce k’warai kuwa ban mance ba, sanda ta ke taimakona ina nak’udar Murad ita kuma ta bani mak’udan ku’dad’e da gwalagwalai ta ce na nesanta kai na daga masarautar gabas kada na sake dawowa don akwai mutanen da suke jiran rayuwata abinda yasa kenan na yi nisa da garin nan, amma tabbas ni na yi nak’udar haihuwar Murad na kuma d’aukeshi a cikin tsawon watanni tar……. Yawun bakinta ne ya k’afe ganin Murad yana tsaye idanunsa cikin na Nene da ta ha’diye sauran maganar a cikinta. Yana nuna ta da yatsa ya ce “Ke ce magaifiyata? Me yasa kika b’oye min?” Ya fa’da yana zubewa a gabanta….

JIKAR NASHE✍🏽🥳
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: (*** Da dai ba zan yi magana ba, amma fisabilillah an min abinda ban ji da’di ba, sai da na rok’eku akan kada a Fidda min littafi sai gashi har ya fara galantoyi a gari saboda son zuciya akan 500 ki ja min asara da yawa. Ina littafin kyauta amma wannan tunda kuka ji na ce na ku’dine me yasa ba zaku bar ni na ci gajiyarsa ba nima, ko ban ce komai ba na tabbata Rabbi yana ji kuma yana gani. 😟😭 littafi nawa na yi kyauta?***)

Tauraruwa itace mace mafi soyuwa a gareni fiye da kowa da komai a duniya, ciki kuwa har da ku dama duka mata na gaba d’aya. Ina son Tauraruwa irin son da ba zan iya kwatantashi da komai ba, sanda labarin rasuwar ta ya iskeni sai da na yi jinyar zuciyata sosai kafin na koma yarda nake da, duk da dai duk wanda ya san ni da yasa ba Mukhtar bane na canja zuwa wani mutum mai yawan shiru da tunani ba don komai ba sai don ji nake kamar na rasa wani b’angare na zuciyata. Dukkan wani farin ciki na yana tattare da rayuwa da Tauraruwa ne, don haka yanzu nake jin zuciyata ta dawo sabuwa dal irin zuciyar da tauraruwa ta tafi ta barta da kewarta da tunaninta. Na yi kewar hirar Tauraruwa murmushinta rigimarta da saurin fushinta, don haka Murad ina umartarka ka so Tauraruwa ka bi kuma dukkan abinda tace in dai kana son farin ciki na, watarana da kanta zata zaunar da kai ta baka labarin yarda aka yi kazo duniya, na tabbata banda taimakon tauraruwa da har yanzu banda Magaji… tauraruwa ce silar samuwarku a duniyar nan…” Sarki Mukhtar ya fa’da yana d’auke k’wallar idanunsa abinda bai tab’a yi a gaban Murad ba. Shi kansa Murad nasa jikin ne ya yi sanyi ya tabbata soyayyar Sarki ga tauraruwa girmanta ya zarce kwatance… Yana share k’wallar ya cigaba da fa’din “Bana fatan Allah ya sake maimaita min ranar da labarin mutuwar Tauraruwa ya riskeni, ba zaka santa ba ko a hoto dalili ni na yi umarni a kawar da duk wani abu da zai dinga tuna min da ita ciki kuwa har da hotunanta na kuma yi umarnin idan ba ni na amince ba ban yarda wani ko wata a cikin masarautar nan ya sake tuna min da ita ba, don na tabbata a duk sanda aka sake ambata min ita ko hotonta zan sake shiga tashin hankali duk da hoton nata sam bai b’ace min a zuciya da ruhina ba, ina sanar maka zan iya rasa komai da kowa idan har Zan samu tauraruwa a raye kuma tana tare da ni muna cikin walwala da nisha’di kamar lokutan baya, Murad ka so Tauraruwa in dai kana buk’atar soyayya ta……” Shiru Murad ya yi yana mayar da numfashi a hankali ga tambayoyi fal a cikinsa amma mamakin furucin sarki yasa ya kasa magana sai lumshe idanunsa kawai da ya yi,zuciyarsa na bashi shawarar ya tsaya ya yi bincike da nutsuwa har ya gano komai a hankali. Don haka ya mik’e a hankali zai fice daidai lokacin da tauraruwa ta fito daga d’aki tana zabga k’amshin turare murmushi ta sakarwa Murad d’in tana neman wajen zama. Fuskarsa a ha’de ya d’an dubeta kafin ya d’auke kai yana mamakin kamanceceniyar da suka yi mai taken kwabo da kwabo. Bata masa magana ba har ya fice daga d’akin. Baya buk’atar magana don haka kai tsaye d’akinsa ya wuce. Mai martaba kuwa kallon Tauraruwa yake fara’a fal fuskarsa kafin ya ce “Ta yaya kika samu cika min buri na bayan fitar da raina akan haihuwa ina son sani?” Dariya ta yi mai ha’de da shashshek’a kafin ta ce “Ka k’addara faruwar hakan a matsayin KUDIRAR ALLAH ni kai na ba wayo na ko dabarata ba ce Suka ba ni haka, duk abinda na aikata d’in na aikata ne Saboda kai da kuma ni, Alhamdulillah a yanzu dukka burikana sun cika, zan bayyana maka komai ba amma ba yau ba sai rana ita yau ranar da Amaryar Murad zata tare a cikin taron mutanen zan sanar da kowa yarda duk abubuwan da suka faru, na yi alk’awarin bayyana gaskiyar lamari a ranar, ba zan b’oye komai ba samuwar cikinsu haihuwarsu da kuma ko su waye suke da hannu a cikin kisa na, da hanaka samun zuri’a.” Sarki ya jijjiga kai ya tabbata Tunda ta ce zata fa’di gaskiya ta kafe kuma sai ranar ya san zata fa’da d’in ba zai takurata ba zai jira lokaci ya san ko zai mutu yana rok’arta ba zata janye k’udirinta ba, Tauraruwa na da kafiya da naci ha’de da tsayawa akan abinda take so daidai ko akasin sa. “Allah ya kai mu” ya furta murya a tausashe yana sakin murmushi. Itama murmushin ta saki ta cikin idonsa ta hango yarda ya k’agu da son sanin labarin sai dai ya danne ne gudun b’acin ranta, haka yake dama tuntuni yana sadaukar da nasa farin cikin da wanzuwar nata farin cikin koda baya so.
Chapter 2 · 0% Book details