Sashe 8
Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kashegari kuwa jirginsu ya sauka a Nigeria, ba wanda ya gayawa za su zo shi yasa ba wanda yazo tarar su sai taxi ya tarar musu don zuwa gida. Gidan Baffa ya nufa direct duk da d’okinsa na son zuwa Garin Gabas sai ya ji ba zai iya wucewa kai tsaye ba ba tare da yaje ya ga Baffa ba. Khaireey sam bata so haka ba don zuciyarta bata son alak’arsa da gidan Baffa ba don komai ba sai don Najee yarinyar da ta tsaya mata a rai, amma ta san ko giyar wake ta sha bata isa ta tari Jaheed da zancen bata son zuwa gidan Baffa idan bai kai tsaye tana son ya ce ta tafi gidan nata Uban bane, don haka taja d’an bakinta ta tsuke har suka isa gidan Baffan.
Ba kowa kasancewar rana ce ko nace Hantsi kowa yana d’aki ana barcin hantsi. Jaheed ya bi filin gidan da kallo yana sakin ajiyar zuciya ganin motar Baffa na nan da alama bai fita ba.
A sashen Umma ya yada zango yana kwa’da sallama. Najee da take kitchen tana dafa abincin rana da sauri ta fito jin murya kamar ta Jaheed, mutumin da take kwana da shi ta tashi da shi a rai. Hular ta har tana zamewa ba tare da ta sani ba. Baki ta bu’de tana pointing d’insa da yatsa fuskarta fal fara’a, sai kuma ta yi saurin gintse fuskar tuna garga’din Umma da ta yi na ta dinga b’oye zumu’di ta akan Jaheed, ba ta lura ma da matarsa da take tsaye tana wurga mata harara ba. Jaheed ma murmushin ya sakar mata yana kallon Buzu buzun gashinta da yake tsaye kamar gargasa saboda cika da kauri da tsawo. “Tsifa a kitchen don k’azanta Najee? Wato ke dai ba kya girma ko?” Turo d’an bakinta ta yi tana furta ba tsifa fa nake ba, kan ne a kunce ni kuma bana son a kitsa min shi.” “Saboda raki ko? Ke komai zafi kitson ma zafi yake miki?” Ta d’aga kai idanunta na sauka a kan Khaireey da ta b’ata fuska tana mata kallo mai kamar harara. “Lah! Ya Jaheed Ai sai kace da Anty Babba kake? Ki shigo mana kika tsaya kamar bak’uwa.” Hararar ta sake wurga mata sai dai Jaheed na juyowa ta yi saurin sakin murmushin yak’e ita kuwa Najee itama hararar ta b’alla mata har da guntun tsaki ta fice daga parlourn tana ji Jaheed yana furta “Ina Umman?” Bata amsa masa ba sai dai ta je d’aki ta taso Umman Daga haka ta shige d’aki sai ta ji gaba d’aya har shi ma haushinsa take ji ba matar tasa ka’dai ba.
Mamaki ne ya kama Umma da ta gansu a parlourn “Ku kuma fa saukar yaushe?” “Now now Umma.” Jaheed ya fa’da yana dariya. “Ai ba sai ka fa’da ba, kamaninku ma sun nuna yanzu kuka shigo k’asar, amma zuwa ba sanarwa Jaheed.” “Zuwan dole ne Umma, Nene ce ta kira ni wai an ga Baba na har ma da Murad!” Umma da sauri ta kalli k’ofar tana masa alamar ya yi shiru. Shirin ya yi yana mata kallo cike da neman k’arin bayani. “Baffanku bai san inda ta tafi ba, kuma bana son ya sani ta ja min fa’da, da gaske dai tana can garin gabas d’in sai dai har yanzu bata tabbatar da yarda aka samar da cikin ku ba, yanzu ba sai anjima ba kafin Baffa ya san da zuwanku ka yi sauri ka je sashensa ka gaya masa ana tsammanin an ga mahaifin ku zaka je ka ‘dau Nene ku je, idan shine zaka yi waya ka fa’da sai mu rankaya mu tafi.” Jaheed ya d’aga kai yana mik’ewa, sai yaga Khaireey itama ta mik’e da mamaki Nene take kallonta ta ce “Ki jira ya dawo mana, ai ko can garin zai je ba dake zai tafi ba zama zaki yi anan har sai mun san yarda ake ciki sai mu bi shi.” Khaireey ta zauna tana jin ranta bai mata da’di da hukuncin Umman ba, har tana furta “Mai shegen shishshigin tsiya in zauna in miki Uwar me? Kina neman cusa masa y’arki ya aura ko kunya ya saki ya ku aura masa k’anwa gidana zan tafi ba zan zauna anan d’in ba, ina ganin buzuwar y’ar ki mai kama da mutanen ethiopia. Umma dai bata kulata ba ganin tana cika tana batsewa ta kawo mata ruwa da abinci ta shige d’akinta don ba da ita za’a yi wannan iya shegen ba.
Shiru sashen Baffan sai k’arar t.v Mahmeey ce kawai a parlourn tana d’an gyara inda Baffan ya gama cin abincin safe. Ta tsinci sallamarsa a bakin k’ofa da sauri ta d’ago tana kallon k’ofar tana ganinsa ta gintse fuskarta sosai don ta tsaneshi musamman da aka wayi gari Najma na da cikinsa a jikinta. “Ina yin Mahmeey.” Ya furta shima tasa fuskar a ha’de. Bata amsa ba illa juyawa da ta yi ta cigaba da aikinta. Bai hak’ura ba ya ce “Wajen Baffa na zo.” “Saboda Baffan Ubanka ne?……..” gyaran muryar Baffan da ta ji ne ya sata yin shirun da bata shirya ba. “Wa nake ji kamar Mujaheed?” Bata amsa ba ta bi ta gefensa ta shige d’aki. Jaheed kuwa yana murmushi ya mik’e yana furta “Ni ne Baffa, ashe kana ciki?” “Ina Jaheed, daga ina haka ba sanarwa.” Jaheed ya d’on sosa kai yana gyara zaman hular sanyin da take kansa ya ce “Wallahi tafiyar gaggawa ce Baffa, wani ne ya sanar da ni ta waya ya san iyayena shine na zo neman izinin ka na d’au Nene na wuce da ita idan mun tabbatar da sahihancin labarin sai na muku waya kuma ku biyo mu, to sai na tarar ma Nenen na wajen Hajja Kaka…” Kallonsa Baffan kawai yake kafin ya d’an jijjiga kai ya ce “A wani gari aka ce mahaifinnaka ya ke?” “Garin Gabas.” Baffan ya maimaita Sunan garin sai kuma ya ce “Shikkenan ka je, Allah yasa a dace sai ku tafi da Faruk ko?” Jaheed ya d’aga kai ya ce “Tom shikkenan Baffa mun gode Allah ya k’ara girma.” Baffa ya d’aga kai yana furta “Allah ya kai ku lafiya Allah ya muku albarka, ina iyalin naka? Ka kuma san Najma na da ciki ko?” Da sauri Jaheed ya d’ago kai ya kasa cewa Baffan komai sai dai mamaki da ganin girman Ubangiji ya cika zuciyarsa, wato tabbas KUDIRAR ALLAH da girma take girmanta ya wuce duk wani tunanin bawa. “Tana da ciki, saboda haka har yanzu da aurenka a kanta, har sai ta haihu tukun na, don haka tana da hakkin kulawa a wajenka, bana son Allah ya kama ka da laifin watsi da hakkinta. Shi yasa na gaya maka.” Jaheed ya saki ajiyar zuciya yana d’aga kansa a hankali “Ka je, Allah ya dawo da ku lafiya.” Jikinsa a sanyaye ya mik’e ya fice daga d’akin duk ya kasa ha’da ido da Baffan, kunyarsa ta masa dabaibayi.
Umma ma kunyarta yake ji, don haka yana fita ya kasa kallonta illa fita ya yi yana furta “Umma zan je na d’au Faruk mu wuce.” Umma ta bi shi da kallo tana furta “A haka zaka wuce ko abinci fa baka ci ba.” Murna da d’oki ma yasa shi ya manta da batun abinci burinsa ya je garin gabas yaga waye mahaifinsa. Ya girgiza kai “Na k’oshi Umma, wanka kuma idna na je zan yi.” Umma ta girgiza kai “Duk don zumu’di Jaheed? To ita kuma matar taka fa?” Ta zauna anan Umma idan na dawo zuwa jibi sai mu tafi, idan kuma ta tabbata mahaifin nawa ne sai ku taho da ita idan zaku zo.” Khaireey wani kallo ta zuba masa kamar ta zunduma ihu. Umma tab’e baki ta yi tana nazarin yanayinta tun d’azu. Har zai fita ta ce “Ka biya sashen Mahmeey kaga Najma ka san tana da juna biyunka a jikinta ko?” Wata irin fa’duwar gaba ta samu Khaireey ta ‘dago tana kallonsa sai taga ya d’aga kai yana furta “Na sani Umma, idan na dawo zan ganta….” Ya fa’da a gaggauce yana ficewa daga sashen.
Najma kuwa tun bayan shigowarsu ta gan shi don haka ta fito tana dakon fitowarsa. Ta tsaya jikin motarsa hannayenta rungume a k’irji. Ta hangoshi yana tahowa cikin takun dake nuni da cikar mazantakarsa da alama yana cikin nisha’di don fuskarsa ta nuna haka. Ta sake gyara tsayuwarta tana jin cikinta na motsi a hankali. Yana isowa wajen ya lura da ita. Da sauri ya gintse fuskarsa.. idanun ta da suka tara k’walla ta zuba masa tana furta “Ya Jaheed ina yini?” Bai amsa mata ba ya shiga motar sa ya mayar da murfin ya rufe sai da ya tayar da Motar sannan ya sauke glass d’in yana kallonta ya furta “Koma ciki Malama akwai sanyi bana son komai ya samu Jikan mahaukaciya da ke cikin ki.” Ya ja motar da sauri Najma kuwa runtse idanunta ta yi tana sakin hawayen da take ta b’oyonsu tun d’azu.
Ya biya ya d’au Faruk suka nausa Garin Gabas Faruk da yake ya san hanyar garin shi ya yi driving har zuwa cikin masarauta.
A harabar masarautar suka yi Parking Jaheed yana sako k’afarsa waje idanunsa suka fa’da cikin na Tauraruwa da take tsaye tana ta sakar masa murmushi murya cikin nisha’di ta ce “Barka da sauka Mujaheed yarona d’an albarka!
Madalla da Uwar da ta min rainonka ta haifa min kai ta kuma shayar da kai da nononta mai albarka, nan gaba ka’dan zamu sakanta mata da sakamakon alheri na ladan d’awainiyarka da ta d’auka, Tabbas Nenenka ta cancanci a yaba mata!” Cak ya tsaya yana zuba mata wani irin mugun kallo!
JIKAR NASHE✍🏽🥳